← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 18

Sashe 14

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

za ki koma ba Saboda..ya ma isa! Kafin ta karasa maganar na katseta,na sake fadin ya ma isa ya hana ni!ban jira ta gama magana ba na aje wayar kan gado ina ji ta na hello hello ido na rufe na nufi bangaran Suleman. A dakin shi na tarar da shi zaune yana rubuce rubuce,ganina ya sa ya aje biron ya tashi tsaye cike da mamaki,amma ko da ya ga yanayin fuska ta ya san bomb ne zai tashi. Na tsaya daga bakin kofa,ya ce shigo mana Jauda,na karaso inda ya ke hannuna bisa kugu na sam na ma manta shigar da ke jiki na masifa ta na ci na ko dan kwali ban daura ba bare mayafi. Ya bini da kallo kamar zai hadiye ni,tin da yake be taba ganin macen da ta bashi sha’awa kamar yanda na bashi a halin da na ke ciki yanzu ba. Sam ban kula da irin kallon da ya ke min ba sai da na je dab dashi na ce dan me ya sa za ka hanani karatu? Yaushe ka fara magana da yawu na? Ya ina neman abu na samu dan rashin adalci ka yanke min hukunci mai tsauri ba tare da ka tambaye ni ba? Sai hawaye su ka shiga gangarowa daga ido na. Maimakon ya min magana sai kawai na ji yayi hugn dina,na shiga kokarin kwacewa amma ya rike ni gam har na gaji ni ma na yi lamo a jikin shi,da ya ji na nutsu ya dago da fuska ta mu ka hada ido,na saukar da nawa idon,ya yi kissin idon nawa sai na buye fuskata a kirjin shi. Ya ja ni muka zauna a bakin gado amma har yanzu be sake ni ba. Ya ce ki yi hakuri Jauda na je yola ban fada mi ki ba,ni ma ban san da tafiyar ba ne. Na ma sa banza. Jauda? Na ji muryar shi ta canza,kuma ni ba yarinya ba ce tuni na gane yanayin da mai irin muryar ke ciki,na yi sauri zan tashi ya dada kamkame ni ya ce ba hanaki karatu na yi ba,amma ba zan iya bari ki tafi har yola ba,za ki min nisa da yawa,ki duba halin da ki ke ciki,hankali na ba zai kwanta ba idan na yi sa da ke. Cikin rai na na ce saban salo kiran sallah husur. Ya dago fuskata na kalle shi na ga idanun sa sun canza,murya na rawa na ce bari na koma daki na toh,ya dada kamkame ni yace Jauda ai yau kin shigo kenan,I can’t let you go. Na fashe da kuka. Ya cikin rarrashi ya na shinshinar gashin kai na ya ce dan Allah kar ki manta akwai igiyar aure na a akan ki,ki taimaka kar ki haramta abunda Allah ya hallata,a matsayi na na mijin ki ina bukatar mata ta a daren yau….be jira na bashi amsa ba ya fara kissing dina kamar babu gobe,ya haye gado dani,ni ko sai kuka kawai na ke. Da ga nan ba sai na tona asirin miji na ba,kuma kun san sauran [01/11 22:47] Salma Ateeku: [8:04pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 47;48;49: Da sassafe na farka,ko sallar asuba ban yi ban. Na duba gefe na ban ga C. Suleman ba sai wata yar takarda na gani nade a gefe. Na dauka na ga rubutun S.Man kamar haka ” You are the best thing that ever happend to me. Na so ace ina nan ki ka tashi,amma aiki ya kamani da safe dole na tafi. Tak kia of yourself for me..” Na aje takardar gefe gami da runtse ido,gani na ke tamkar na ci amanar tsohon miji na duk da kuwa auren aminin na shi na ke,duk da kuma yanayin rabuwar ta mu,amma abun da kunya. Na godewa Allah da yasa S.man ba ya nan dan ban san da wani ido zan kalleshi ba,ban yi shirin fuskantar shi ba. A Hankali na tashi na ga kaya na ninke a gefen gado. Na ja su na sanya. A hankali zuciyata cike da alhini na sauka bangare na. Can bangaren Hajiyar Aliyu kuwa tin da Aliyu ya kai babba gidan ta,har ya tafi sudan be sake waiwayan ta ba. Indija ta sami wani saurayi dan duniya mai suna Bello,ba karamin kashe ma ta kudi ya ke ba,ya nuna ma ta duk duniya babu wacce ya ke so kamar ita,har ta saki jiki da shi. Ana haka ranan ya takura lalle abokin sa ya yi aure ya kamata su je su ga gida. Ta ce toh za ta tambayi hajiya ya ce ah ah,irin wannan ba sai ta tambaya ba,dan kila ta tambaya a hana ta,da safe ma za su tafi ta yi karya ta ce za ta makaranta sai kawai su wuce. Haka ko aka yi,da safe ta ce da Hajiya za ta makaranta,Hajiya ta bata kudin mota da na kashewa. Bayan fitowar ta,ta yiwa bello waya ya zo ya dauke ta sai gidan abokin shi. A waje suka tadda abokin ya shigar da su falo. Ya kawo musu lemo sai tsokanar Bello yake. Shiru Indija ta ga amarya ba ta fito ba,ta kasa shiru ta ce ina amaryar ne,abokin Bello ya sosa kyaya ya ce ta na wanka ne,ki dan sha lemon kafin ta fito. Ta ji sanyi cikin ran ta,Bello ya zuba mata lemon ya bata ta fara sha shi kuma sai hira ya ke da abokin shi. Jim kadan ta ji jiri na kwasan ta,ta ce da Bello dan Allah mu je gida,ba na jin dadi,abokin Bello ya ce ah ah ba ki ga amaryar tawa ba za ki tafi? Indija ta tashi ta ce ma dawo…ba ta karasa magana ba jiri ya debe ta,ta fada kan kujera ta na baccin dole. Bello ya daka tsalle ya bawa abokin shi hannu su ka tafa,abokin ya ce toh sai ka dauke ta ku wuce daki ka ci kudin ka. Bello ya ce tini ma kuwa. Ya yi daki da Indija. Ba ita ta farka ba sai yamma,kanta ya sara ga wani ciwan da ya sassake dukkan gabobin jikin ta,a hankali ta bi dakin da kallo,ta duba jikin ta ta ganta tik,sai a sannan ta gane aika aikan da Bello ya ma ta,ta fashe da kuka mai karfi. Bello ya fito daga toilet yace Indija Indija,Indija babbar budurwa! Ta dada fashewa da kuka ta na fadin ka cuce ni ka gama da ni Bello,dama ba so na kake ba,dama san cuta ka ke min?ya daura kafa daya kan gado ya na kallan ta,ya ce aw ke ki na tunanin zan miki san da ya fi wannan? Hahahahaha toh na soki na ce na so me? Ai dama investing na ke,yau kuma na kwashi kudi na har da riba. Ki godewa Allah da na hana abokina kwasar bati,tin da dai bai sa hannun jari ciki ba! Ta fara zagin shi,tsinan ne,azzalumi Allah sai ya saka min,ko a jikin shi ya ce oho,ki maza ki shirya dallah,masu gidan sun kusa dawowa. Ya fita ya na dariyar mugunta. Bakin ciki kamar Indija za ta hadiyi zuciya,gaba daya ta tsani kanta. A haka ta lallaba ta shirya,Bello ya ce zai sauke ta gida,ta ma sa banza,ta na jiyo dariyar shi ya na fadin in an sami karuwa a gayyace mu suna. [8:13pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 50;51;52:Indija ta kasa fadawa Hajiya abunda ya faru,gaba daya ta canza ko makaranta ba ta iya zuwa,gani ta ke kowa ya san abunda ya faru da ita. Bayan sati biyu ta na zaune,abun duniya ya ishe ta,ta ji Hajiya na kiranta. Ta tashi ta je ta same ta ita ma ta doka tagumi. Ta zauna gaban ta ta ce Hajiya gani. Hajiya ta ce Indija kin ga Aliyu gaba daya ya yada mu,tin da ya sa kafa ya tsallake mu be sake ko da waiwaye ba,ya zan yi dole na yi bikon sa,ina wannan aminin na shi Suleman? Indija ta ce kwana ki ma na ji ance ya yi aure. Hajiya ta murmusa Allah sarki,da lfy kalau ne kin san da na ji ai. Kin san gidan na shi? Indija ta ce eh,Hajiya ta ce toh ki shirya ki je ki ce dashi ni na turoki ki karbar min numbar da Aliyu ya ke amfani da shi a sudan,kya ma ji ma na lbrn yanda Aliyun ya ke dan na san shi dai suna waya. Indija ta ce toh Hajiya. Indija ta shigo gida na ta na sallama,Jummai ce a kitchen ta fito tare da amsa ma ta. Ta sami waje ta zauna tare da gaisawa da Jummai,ta ce da Allah Captain Suleman ko ya na nan? Jummai ta ce ah ah ya fita. Indija ta dan yi jugum,can ta ce amaryar shi fa? Jummai ta ce bacci take,kuma Oga ya hana tashin ta idan ta na bacci. Ta ce toh bara na tafi,pls ki ce da ita kanwar abokin shi Aliyu ce ta zo,ta fada ma sa zan dawo,hakan yayi daidai da fitowa ta,na ce da Jummai bakuwa mu ka yi ne? Mu ka yi ido biyu da Indija a firgice ta tashi ta na nuna ni da dan yatsa. Jummai ta ce dan Allah ki yi hakuri madam kar dai ni na tada ki,sai da na ce ma ta Oga ya hana,na murmusa ina kallan Indija wacce bakin ta ya ke a bude,na ce da Jummai kar ki damu,ban ma ji ku ba,na dai tashi ne. Indija yau kuma ke ce a gida na? Na tambayeta cikin sakin fuska,baki na rawa ta ce wai dama ke ce matar da Suleman ya aura? Na ce eh,zauna mana,ina zama be kamata ba da sauri ta fice ta na simbatu,Jummai ta ce Madam halan wannan ba ta da hankali,na murmusa yayinda na zauna kan kujera na ce ko kusa,lfyn ta lau Jummai. Jummai ta ce toh,Allah ya kyauta,kamar wacce ta ga fatalwa wannan firgici haka,murmushi kawai na ke yi. Da gudu ta shiga gidan Hajiya saura kadan ta afka ma ta akai. Hajiya ta ce ke menene haka!biyo ki aka yi ko me? Indija ta ce Jauda,Hajiya Jauda! Hajiya ta ce Jaudar ce ta haukace ta ke bin mutane? Indija ta ce Hajiya ai sai dai ni na yi hauka amma ba Jauda ba,Hajiya Jauda ce matar da Suleman ya aura!
Chapter 14 · 0% Book details