Sashe 5
Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya sarawa General,ya juya zai fita,har ya kai kofa General ya tsaida shi da fadin nd you can go with your wife if you like. Cikin Fara’a Oga ya juyo ya sarawa General yes Sir! Har sai da shi kan sa General ya murmusa,ya gyada masa kai.Oga ya fice cikin zafin nama. Bayan sun tashi da ga aiki Oga ya zo ya dauka na,ya cika alkawari ya shiga ya gaishe da Anty Sa’a shi da C. Sulaiman,nan na fara jin zancen tafiyar shi sudan ya na fadawa Anty Sa’a,ta yi masa murna sosai da ta ji zai tafi da ni.shi ko C. Sulaiman cewa ya yi wato Nigeria ba gaskiya,da ke jauda kanwar General ce sai ya ce za a iya ta tafiya da ita,dan masu gata ne kadai ake bari su tafi da fmly din su. Anty Sa’a ta ce ko kamar ya yi a gaban General sai ta fada masa,C Suleman ya ce dama so ta ke ta hada su ai,ya gama gane lamarin ta. Jiddah ma ta samu su ka gaisa da Oga,kamar kar na bar gidan haka na hakura na koma gida na. Washagari da yamma,na ci adona cikin atamfa orange dinkin styler mai dan karamin hannu,riga da zani,da ke babu abunda ya kai zani fitar da structure,dam ya zauna a kuna. Na kafa dauri na a goshi irin wanda ake kira ture ka ga tsiya na na faka gashi na a kyeya. Na nufi kitchen domin kwaso abincin Oga,ya kusa dawowa. Na zo kofar kitchen kenan Indija ta fito daga kitchen din ta sane ta bangaje ni sai da na kusa faduwa,ciki na ya murda.cikin sauri na tsaida kai na ina fadin Yahayyu ya kayyum! Da ke Indija ba ta da kunya sai ta hau min masifa ta na fadin ke wata irin mahaukaciya ce?ba kya gani ne? Na kalle ta cike da mamaki. Indija ni ce mahaukaciyar? Ki bangaje ni din ki kara min da zagi? Me na tsare mi ki ne dan Allah? Cikin tsiwa ta ce eh ke ce mahaukaciyar! abunda ki ka tsare min ki ki ke tambaya? toh miji na ki ka aure! Na murmusa na ce mijin ki kuma? Ai ni ban san ki na da miji ba,ni dai ni kadai ce gun miji na,daya tamkar da dubu dan kuwa gadan ari sai fanna,wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa har abada,wawiyar banza wawiyar wofi,da za ki gane da iska ta dai na wahalar da mai kayan kara..ta daga hannu za ta mare ni,na ruke hannun na zuba mata mari kwarara guda biyu,ta yi wani ihu za ta riko ni kamar daga sama Oga ya daka mata tsawa kul! Don’t you dare hit my wife! Duk mu ka jiyo mu na kallan shi,tsaye ya ke a bakin kofa,ya cigaba duk abunda ki ka mata a kan ido na,dama rashin kunyar da ki ke ma ta kenan idan ba na nan?toh ki hade kayan ki,ko ki koma gidan ku ko kuma gidan Hajiya amma dai ki bar min gida na!Indija ta sa kuka,ko a jikin Oga sai ma karasowa da ya yi,ya yi hugn dina ya na tambayar ba ta ji mi ki ciwo ba ko?na yi lamo a jikin sa kamar wata yar yaye na ce ma sa ah ah Am fyn.ya kalli Indija me ki ke jira? Da gudu ta shige daki ta na kuka.Oga ya ja ni mu ka shige ciki abun mu. [4:42pm, 11/14/2014] Khadija Sidi: Matar mu 23;24;24: kafin magrib Indija ta hada na ta ya na ta sai gidan Hajiya,ta na shiga ta fara kurma ihu,a falo ta tadda Hajiya ta na sallah,ta zube kasa ta na kuka. Da sauri Hajiya ta sallame ta na fadin lafiya?me kuma ya faru?Indija ta kada baki ta ce Hajiya yau na ga wulaknci iya ganin ido na, Hajiya ta ce wulakanci fa ki ka ce? Wa ya wulakanta ki?cikin kuka ta ce Hajiya ya Aliyu,bayan matar shi ta mammare ni,ta zage ni tas ta uwa ta uba a gaban shi,be hana ta ba sai ma kara min da korar kare ya yi..Hajiya ta fusata! Korar kara? Indija ta ce wallahi Hajiya a gaban ta kuma ya kore ni!Hajiya ta ja waya ta na kokarin kiran Oga,dan be da mutunci ya kore ki daga gidan sa?sakaran banza sakaran wofi mace tafiye ma sa dangi? Bari na kira shi,yau sai ya sake ta..Indija ta yi saurin dakatar da Hajiya tare da fadin Hajiya kar ki kira shi,wlh ko kin sa ya sake ta kin san sai ya ci gaba da bibiyanta yanda ta gama asirce,ai kamata ya yi mu ma ta bi ta da kulle dukan kabarin kishiya. Hajiya ta katse wayar dama ba shiga ta yi ba,ta ce eh nan fa daya,fada min abinda ke ran ki.Indija ta gyara zama,tina ta daina kukan da ke dama na munafunci ne. Ta ce Hajiya sharri ya kamata mu kulla ma ta,sharrin da ba Ya Aliyu kadai ba duniya ma sai ta juya mata baya. Hajiya ta ce wannan ma zai yi,dai na kame kame ki min bayani dalla dalla yarinya. Indija ta yi murmushin mugunta ta ce Hajiya a sannu za ki gane kudiri na,amma idan ya Aliyu ya zo ki ce masa ya turo mi ki mai aikin Jauda. Hajiya ta ce ki na tunanin ba za su zargi wani abu ba? Indija ta ce ko kusa tinda dama ai ke ki ka sama mu su yar aikin ko? Toh ki ce ma sa mahaifiyar ta ce ta zo daga kauye.Hajiya ta ce toh hakan za a yi,bari na idda sallar da ki ka katsemin.ta tashi ta tayar da sallah,Indija ta shige ciki ta na fadin in ta san wata ba ta san wata ba,wallahi sai na sa Aliyu ya wulakanta ta. Ranar lahadi da yamma Oga ya je gidan Hajiya,ba ta masa Tarbar arziki ba,sai ma tatas da ta masa akan korar Indija da yayi bayan na gama zage ta na hada da mari. Cikin ladabi ya ce Hajiya ta ba haka aka yi ba,ta na sane ta buge ta,kin san haka hatsari ne ga mace mai dauke da juna biyu..yi mim shiru mara kunya!ta daka ma sa tsawa,ka manta juna hudu ba biyu ba,ni za ka fadawa maganar banza! Ya sunkuyar da kai,Allah ya huci zuciyar ki Hajiya ta,ayi hakuri.ta ce amin. Oga ya ce Hajiya ta dama ma zo na sanar da ke barikin mu za su tura mu sudan nan da wata hudu. Sudan kuma?in ce dai ba yaki ake ba?oga ya murmusa ba yaki ake ba Hajiya,course aka tura mu,yanzu gobe idan Allah ya kai mu zan je Abuja na yi reportn. Hajiya ta ce toh Allah ya nuna mana ya kai ka lfy ya kuma dawo da kai lfy. Ya ce amen ya Allah,ya fitar da bandir din kudi ya aje gaban Hajiya ya ce Hajiya ga wannan ba yawa. Hajiya ta dauka ba ka dai gajiya da hidima,Allah ya saka da alkhairi. Na ce ina mai aikin gidan ka Karima? Ka turo min ita. Oga ya ce toh,akwai wani abu ne? Hajiya ta ce mahaifiyar ta ce ta zo daga kauyen su take son ganawa da ita. Oga ya ce Allah sarki ina mahaifiyar ta ta ai ya kamata ni ma mu gaisa,Jauda na jin dadin zama da Karima ai,kin ga sai ma na kai ta gida na sa ma gaisa da Jau….rufa min baki da Allah,da anyi magana sai ka ce jauda jauda jauda! Toh ba za ta je gidan na ka ba din,kuma kar ka sake ka kamin matar ka gidan nan,sakarai! Oga ya yi shiru,daga bisani ya ce Hajiya bara na tafi toh.Hajiya ta tsuke fuska a sauka lfy. Oga ya ce Allah ya sa Hajiya,ya tafi ya na tunanin yanda zai yi maganin matsalar da ke tsakani na da Hajiya, Bayan komowar shi gida ya Fadawa Karima sakon Hajiya tare da bata kudin mota,ni ma na hada mata da atamfa tirmi guda da sabulai ta bawa mahaifiyar ta ta. Cikin murna bayan ta gaisa da Hajiya ta ce Oga ta ce mama na ya zo Hajiya ta ce Karima saurare ni da kyau,mahaifiyar ki ba ta zo ba,wani aiki zan saka ki shi ya sa na kira ki. Farin cikin Karima ya koma ciki dan tasa aikin Hajiya ba aikin arziki ba ne,da ke ta saba ba ta kulle kulle da kayan asiri ta na birne wa a gidan Oga. Ta ce Hajiya wani irin aika zan maka? Hajiya ta ce aiki ne babba ba irin wanda ki ka saba yi ba,amma ki sani idan har ki ka min zan baki naira dubu dari..dubu deri Hajiya Karima ta fito da ido cikin mamaki. Hajiya ta ce kwarai da gaske,na kuma hada da zannuwa wanda za ki kaiwa mahaifiyar ki. Cikin zumudi Karima ta ce Hajiya fada min abunda ka ke so,wlh zen yi ma. Hajiya ta murmusa toh ba lefi,ki yi jiran Indija,za ta fada miki ta kuma ta hada ki da abokin aikin na ki. Karima ta ce toh Hajiya,wlh zen yi…. [10/20, 11:01 PM] aunty jidda: OLD BUT GOLD MATAR MU 25,26;27;28:Washagari da safe,na yiwa Oga rakiya har mota,driver ne aka turo da ga barrack zai kai shi Airport. Na dube shi cikin mota zaune na ce Oga ka ki bari na raka ka ko? Ya riko hannu na worry not my baby ni da yau dinnan fa zan dawo. Na ce toh Allah ya kiyaye,ya ce ameen ameen,take kia of your self for Oga. Na sara ma sa na ce yes sir!kar a manta da addua dan Allah,ayatul kursiyu kafin ka shiga jirgi da kuma sanda za ku tashi. Shi ma ya Sara tare da fadin yes ma! Na yi murmushi na rufe motar,ina daga masa hannu yayinda direba ya tada mota. Har sun kai gate sai na ga sun tsaya,Oga ya fito da sauri ya karaso waje na ya yi hugn dina,a cikin rada na ce Oga gate fa a bude ya ke,ga direba da maigadi su na kallo fa… ya ce ba mata ta ba ce?ya dada makale ni,ni kuwa sai raba ido na ke kamar munafuka,na ce matar ka ce amma da kunya ai….da kyar na samu ya sake ni,ya ce i will miss you,na ce i will miss you more.ya juya