← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke yar nan Jauda fa! Indija ta ce wlh Hajiya har da ciki fa. Hajiya ta sa salati ta na sallallami,ta ce maciya amana,dama tintin cin amanar Aliyun su ke,kin ga gwara ma da mu ka yi silar rabuwar ta su dan ko bajima ko ba dade asirin su sai ya tonu! Indija ta ce Hajiya,ni gaskiya na gaji da irin wannan rayuwa,Jauda kullum dada ci gaba ta ke,hassada ga mai rabo taki,mu kuwa da mu ka shuka sharri gashi sai girba mu ke,wlh ni gida wajan baba ta zan koma. Hajiya ta bude baki kuji yar butan uwa,ni kikewa rashin kunya? Toh kama hanya ki tafi gidan na ku! Indija ta ce yanzu ma kuwa,ta shige ta na fadin rayuwa ba cigaba haka! Hajiya ta doka tagumi duniya ta ma ta zafi,ta rasa inda za ta sa kanta dan bakin ciki,tini hawaye ya cika fuskar ta. [9:33pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 53;54;55:Ciki na ya kai wata takwas,rayuwa ta dawowa S.Man sabuwa,babu hakkin shi da na toye masa,hakan ya sa ya shiryu sosai ya dai na bin mata da shaye- shaye,in banda sigari babu abunda ya ke sha,shi ma din sai lokaci lokaci. Har yau ban fara jin san Suleman cikin rai na ba,sai da akwai wata alaka ta sabo da aminci da ya kullu tsakanin mu,gaba daya zuciya ta ta yarda da shi. Zancen MBS di na kuwa ya min alkawarin bayan na haihu zan sake nema amma a nan jami’ar Bayero. Sam ko da wasa be taba min zancen Aliyu ba,ni kuma ban dai na zargin shi da cin amanar Aliyu ba,amma ban taba furta ma sa ba,na ciki na ciki. Duk dare mu kan fita strolling tare,yau ma tafe mu ke hannu na cikin na shi,hira mu ke sosai,bini bini sai ya tambaye ni kin gaji? Sai na ce masa ah ah,har na gaji da jin tambayar na ce wai menene damuwar ka da gajiya ta ne?yayi kissing hannuna ya ce saboda ba na so ki gaji sosai,na fi so da kin gaji ki fada min na dauke ki dan kar mu je gida na ce mu yi strolling din daki ki ce min kin gaji. Na kwace hannu ina dariya na ce dama nan kafi kauri ai. Yayi saurin mayar da hannu na cikin na sa shi ma dariyar ya ke yace bashakka a wajan ki na fi kauri,you are the best thing that ever happnd to me,ya sankalo da hannun shi kafada ta,na kwantar da kai na jikin shi. Ya ce ranar da ki ka haihu Jauda sai na zabu ruwa a kasa na sha. Na ce Allah dai ya nuna mana,ko ka mance sai na tuna maka,ya ce amen. Haka mu ka ci gaba da tafiya har sai da na gaji din mu ka koma gida,da shigar mu ya dauke cak wai tinda na ki yarda ya dauke ni awaje bari ya min ladan gida yanzu,na ce ai kai za ka sha nauyi,ya tura kofa da kafar shi mu ka shi ga falo ya ce haba Madam Soja na ke fa. Mu ka sa dariya. Gidan Hajiyar Aliyu kuwa gaba daya duniya ta ma ta zafi,ta na zaune ta doka tagumi sai ga mahaifiyar Indija Hajiya Binta tare da Indija sai surfa ma ta zagi ta ke tare da duka,ko da Hajiya ta ga shigowar su da sauri ta je ta ceto Indija ta na fadin baki da hankali ne Binta?Indija ta buya bayan Hajiya ta na kuka. Hajiya Binta ta watsa ma ta harara tare da fadin ya Mairo kin cuce ni,Allah ya isa tsakanina da ke! Hajiya ta ce ni? Ni binta ki ke yiwa Allah ya isa? Ladan rike mi ki ‘yar ki da na yi ko? Hajiya Binta ta ce yo da ki ka ruke min yar mai ya amfana ta da shi? Ga ta nan ta fada mi ki bakin ta abun kunyar da ta janyo ma na. Hajiya ta fito da Indija sarari ta ce Indija wani abun kunya ki ka janyo ke kuwa? Ta kasa magana sai kuka. Hajiya Binta ta daka tsawa za ki yi magana ko kuwa? Murya na rawa ta ce Hajiya amai na ke. Hajiya ta rungumo ta tare da fadin Allah sarki abun ku da annoba,kin san kan ta tafi makota na ta fama da amai da gudawa. Hajiya Binta ta harere ta,amma ban taba tunanin haka ki ke da karamar kwakwalwa ba wlh,toh ciki ta dauko a titi! Hajiya ta kurma ihu CIKI! Innalillahi..wainnailaihirajiun Hajiya Binta ta karasa ma ta,sai da ki ka gama bari ta lalace za ki turo min ita gida,toh ubanta ya ce ba dai a gidan shi ba,ni ko dan ita ba zan bari aure na ya mutu ba,kin ga tafiya. Ta yi tafiyar ta ta bar Indija gaban Hajiya. Hajiya ta fara jibgar Indija ta na fadin shegiya munafuka,me ki ka nema ki ka rasa,waye ya mi ki ciki? Waye uban sa? Indija ta na ihu ta ce Bello ne Hajiya,Bello ne! Hajiya ta ce tashi a daren nan za ki kai ni gidan su! Ta ce Hajiya wlh ban san komai akan shi ba,kawai zuwa gidan nan yake,Hajiya ta ce ba ki san komai a kan shi ba amma ki ka bari har ya mi ki ciki?Ina ki ka san shi?Indija ta ce facebook….Hajiya ta yanki jiki ta fadi baki karkace,Indija ta kurma ihu ta fita a guje ta na neman taimako. [9:44pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 56;57;58:Indija ta samu makota suka taimaka ma ta aka kai Hajiya asibitin barack,nan aka kwantar da ita. Washagari da safe har mota na raka C. Suleman za shi aiki. Ya kalli kafa ta ya ce farce ya taru pls ki tuna min in na dawo na yanke mi ki. Na ce yes Sir. Ya sunkuya yayi hugn ciki na tare da fadin i wil miss you my baby,ina dariya na ce he wil miss his dad too. Ya dago ya yi hugn dina tare da fadin i wil miss his momma more. Ya dago fuska ta yayi kissing goshi na tare da fadin take kia of yourself owk? Na ce owk. Na bude masa kofa ya shiga mota na mayar na rufe. Ema ya bude gate har ya fita ina daga ma sa hannu. Da shigar shi barrack ya yi kacibus da Doctor Usman,ya ke fada ma sa an kwantar da Hajiyar Aliyu rabin jikin ta ya zama paralysed. Be ko shiga office din shi ba wajan Hajiyar ya wuce ya tadda ita kwance wata dattijuwa ce ke jinyar ta. Ganin yanda barin jikin Hajiya ya daina aiki,hatta bakin ta ya karkace ya sa jikin C. Suleman sanyi. Bayan sun gaisa da dattijuwar mai jinyar ta ya je gaban Hajiya ya ja kujera ya zauna. Hajiya na magana da kyar dan sai an kasa kunne ake iya jin ta tace Suleman ina abokin ka Aliyu? Dana Aliyu na cutar da shi,S.man ya ce Hajiya Aliyu be dawo ba,amma sun kusa dawowa,shi ya ke fada,amma gaban sa sai da ya fadi. Ya ce Hajiya ya jiki? Ta ce uhum,jiki gashi dai ka gani,na ce ko ka na da wata numbar da Aliyun ke amfani da shi? Ya ce Hajiya ba sa amfani da waya in ana course din,amma akwai wata numbar da ya ke kira na da shi kafin su fara course din,yanzu ko na kira ba ta shiga. Hajiya ta nisa ta ce toh Matar shi fa Jauda? Nan fa Oga ya tsuke fuska ya ce Hajiya Jauda ki na nufin mata ta kenan? Hajiya ta ce eh haka fa,matar ka,dan Allah ka taimaka ka kawo ta,ina san ganin ta. Ya dan saki ran shi tare da fadin InshaAllahu Hajiya gobe zan kawo ta,Allah ya tashi kafadar ki. Bara na shiga office. Hajiya ta yi godiya,ya tafi gaba daya tunanin shi ya karkata ga waje na,gaban sa sai faduwa ya ke.Gashi ranar wuni yayi yana aiki,ana so a dauki sababbin sojoji amma short service,shi ne mai kula da activities din.ba shi ya gama da office ba sai bayan Isha’i. Tafiya ya ke yana driving,amma gaba daya ni ce a ran sa,cikin kankanin lokaci gaba daya na sauya ma sa rayuwa. He is a better person now. Be taba tsammanin zai so wata ya mace haka ba,shin dama haka aure ya ke? Da ya sani da tin kafin ya kai haka yayi,toh kuma ai da ba zai samu ya aure ni ba,wannan tunanin ya kawo ma sa Aliyu cikin ran shi,a fili ya ce ya zan yi da ke Jauda yar soja matar Soja,yahayyu ya quyyum Aliyu ya kunto min kura…. ya danna hon Ema ya bude gate ya ja gefe ya sara ma sa. Bayan ya faka mota ya shigo sai ya ganni kwance kan doguwar kujera ina bacci. Kai tsaye ya dauke ni ya haura da ni sama dakin shi ya aje ni kan gado ya na nazari na,daga baya shi ma ya hau gadon ya jawo ni jikin shi na dan bude ido mu ka hada ido sai na sakar masa murmushi cikin bacci na sake rufe ido. Jauda ya kira sunana cikin rada,cikin magagin bacci na amsa masa da ummmm. Ya ce kinsan ma’anar sunan ki? Cikin bacci na saki ajiyar zuciya gami da gyara kaina da ke kwance kan kirjin S.Man har sai da ya lumshe ido sannan ya ce yana nufin KYAUTA,indeed ke kyauta ce daga ubangiji gare ni,kin cancanci sunan ki Jauda,ke kyautar Allah ce,bazan taba barin ki ba ko dakuwa zan rasa rai na,ya shafi cikina tare da fadin Allah ne ya bani ke…… Washa gari da safe S.Man ya ce da ni na shirya za mu dubiya. Na tambaya wace ba lfy ya ce wata mahaifiyar shi ce. Na ce toh. Na dau lokaci ina shiri har ya gaji ya shigo daki na ya ganni zaune gaban madubi ya ce da ni dubiya fa na ce za mu ba gidan biki ba,dama dai kin hakura yanda baby na ya kumura ki haka babu abunda za ki sa ki yi kyau. Na zun buro baki tare da fadin ayya mana S.man,ya yi dariya ya ce wasa na ke mi ki,kin san you are always beautiful,amma ki taimaka ki fito mu tafi haka. Na ce toh bani minti
Chapter 15 · 0% Book details