Sashe 17
Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta ya ce na yafe miki Hajiya,ni ma ki yafe min na guje ki tsahon shekara daya. Ta murmusa ta ce ba ka yi komai ba Aliyu,da ma na samu ka dawo kafin na bar duniyar,yanda na cutar da kai Aliyu babu uwar da za ta iya yiwa dan ta..ta numfashi ya fara daukewa Hajiya,da gudu ya fita kiran doctor,kafin ya dawo ina rai yayi halin sa. Indija ihu har da birgima. Aliyu ko hawaye ne kawai ke zuba daga idanun sa. Ba mu jima sosai da shiga gida ba Doctor Usman ya yiwa S.Man waya ya fada ma sa rasuwar. A rude ya sauko ko hula be sa ba ya yi hanyar fita,na biyo shi ina fadin lfy? Ba tare da ya tsaya ba ya ce da ni rashi aka yi,bara na je na samu jana’iza. Nan take na gane Hajiya ce ta rasu na sa kuka,a dole ya tsaya ya rarrashe har sai da na nutsu sannan ya tafi. [01/11 22:47] Salma Ateeku: [10:33pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 66:67:68:Bayan an kai Hajiya an dawo,aka zauna rumfar zaman makoki domin karbar gaisuwa. Aliyu zaune cikin yan uwa da abokan arziki sai ga S.man,ya bawa ko hannu suka gaisa ko da ya bawa Aliyu sai ya ki karba,S.man ya aje hannun sa tare da fadin ya hakuri? Fuska a dake yace Alhamdulillah. S.man ya ce Allah ya ji kan Hajiya,jama’a su ka amsa da amen. Ya sami waje zai zauna Aliyu ya dakatar da shi tare da fadin pls bana bukatar ka a wajennan,ka bar ni da zafin rashin mahaifiya ta kadai ya ishe ni ba sai ka kara min ba. S.man ya ce Aliyu…Aliyu ya daga masa hannu ka bar wajannan malam. S.man ya tashi ya ce Allah ya bada hakuri. Jama’a suka ce amin. Ya juya ya tafi. Kowa mamakin al’amarin ya ke musammam abokan aikin su da suka san amintar da ke tsakanin su. Ya same ni zauna kan dadduma,na idar da sallah. Ya zauna gami da jawo ni jikin sa,yayi kissing kumatu na. Cikin mamaki na ce baka zauna wajan makoki ba? Ya na wasa da ‘yan yatsu na yace abokina ya ce baya bukatar gani na awajan. Na yi shiru dai hawaye na fita daga ido na,ya dago fuskata ya ce kukan ya isa haka,pls be kamata ki na daga hankalin ki ba.Ya share min hawayen tare da fadin gobe fa za mu shiga watan haihuwan ki,kin san idan ki ka haifi mace me zan sa ma ta? Na girgiza kai alamar ah ah,ya dada kamkameni sannan ya ce Jauda,Jauda zan kira ta,na murmusa na ce dan san kai? Ya ce san kai laifi ni? Duk mu ka yi shiru muna sakar zuci. Daga bisani na kira sunansa Suleman? Ya amsa da ummm,na ce kar ka damu,komai zai dawo daidai tsakanin ka da Aliyu da yardar ubangiji. Ya murmusa ya ce Allah ya amsa Jauda ta,i miss bn his frnd. Ya tashi ya taimaka min nima na tashi mu ka shiga dakina dan bene yanzu wuyar hawa ya ke min. Gado na ya hau ya jawo ni na kwanta a jikin sa,cikin rada ya ce da ni Jauda kin san me? Na girgiza kai alamar ah ah,ya ce when it comes to you I jst want to hold you,na ji ki a jika kadai ya samin kwanciyar hankali. Na dago na yi kissng din sa sannan na koma na kwanta,a haka bacci mai dadi ya sace ni. Bayan Sati biyu da rasuwar Hajiya General yayi kiran mu gidan sa,mu na falo a zaune sai ga Aliyu shi ma ya zo,tini hankali na ya tashi. Allah ya taimaka zuwan shi yayi daidai da fitowar General da Anty Sa’a. Ba tare da bata lokaci ba ya fara gabatar da abunda ya sa ya tara mu. Kai tsaye ya ce na ji wani mummunar labari dangane da dangantar ku,shin me ke faruwa? Kowa ya yi shiru,ya ce da ku na ke ina neman bayanin abunda ke faruwa. Anty Sa’a tace Sule kai ai sai ka yi bayani. Nan S.man ya kwashe komai da ya faru ya labartawa General,ran General ya yi masifar baci da ya ji batun auren ki san wuta,ya dubi Anty Sa’a ya ce kin san da wannan zancen amma ki ka kasa fada min Sa’adatu? Jiki sanyaye ta ce na yi kuskure,ayi hakuri. Ya ce wannan ai yasheshshen zance ne,auren ki san wuta? Da ki ka sani da kin fada min tin wuri ai da abun be kai haka ba,ai shi ice tin yana danye ake tankwasa shi. Ya dubi Aliyu da Suleman kawai kun tadawa yar mutane da hankali ku dubi halinda ta ke ciki,ba ku tsoran ku ja ma ta matsala?ni dai kai na sun kuye kuka kawai na ke,suma Su ka sunkuyar da kai,yan zu ya kuke so a yi? Kai Ali me ka ke so a maka? Fadi ina jin ka. Aliyu ya ce so na ke ya sakar min mata ta..General ya ce da Suleman kai za ka sakar ma sa matar ta ka? Suleman ya ce Sir wallahi ni ina san mata ta,ba zan iya sakin ta ba. General ya kalli Anty Sa’a kin ga irin ta ko Sa’a?ya nuna Aliyu you are wrong,ya sake nuna Suleman ya ce and you are wrong tooo,nd idan ku ka ci gaba da yanda kuke you wil continue to be wrong,two wrongs can not make a ryt,ina amfanin abun?toh daya dole ya hakura,kai Suleman dau matar ka ka tafi,kai kuma Aliyu ka dau dangana,kaddara ta riga fata,Allah ya baka wacce ta fi Jauda. Rai a bace ba yanda ya iya yace yes Sir,haka kowa ya tafi gida rai babu dadi. [11:20pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 69;70;71;72:Inna ta turo min Jiddah saboda rashin Jummai gashi na kusa haihuwa.yau tin da na tashi da safe na ke fama da ciwo sama sama,amma ban fadawa kowa ba.Mu na zaune a falo mu na hira da Jiddah ta ke fada min sun je sun yiwa Aliyu gaisuwa ita da Anty Sa’a,na ce sun kyauta. Ta ce yanda ta ga ya lalace wlh sai duk ya bata tausayi,na ce rayuwa kenan. Ta ce sis da ki na da zabi wa zaki zaba tsakanin Aliyu da Suleman? Wannan tambayar tata ya yi daidai da shigowar Suleman da ke juma@ ce sanye ya ke cikin manyan kaya,jin tambayar da Jiddah ta min ya tsaya be karasa shigowa ba,mu kuma ba mu lura da shi ba. Na ce Jiddah ya ina da aure na ki na tambaya ta zabi? Zabi ya wuce wanda Allah ya rigaya ya gama rubuta min?zan zauna tare da miji har karshen rayuwa ta. Jin amsar da na bata ya sa shi sakin numfashin da shi kansa be san ya ruke ba,cikin farin ciki ya yi sallama gaba daya mu ka amsa,ya shigo ya na fadin Jiddah ki na dai kular min da Madam ko? Kujerar da ke kallan tawa ya zauna,zaman sa yayi daidai da jin kamar an mintsile ne,wani irin ciwo ya taso min yayinda mara ta ta ruke na fara jin wani abu mai dumi ya na gangaromin kafa ta. Jiddah ta ce masa sosai ma kuwa S.man. kallo daya ya min ya gane halin da na ke ciki,ya dawo kusa da ni da sauri ya ce Madam yaya? Ina cije lebe na ce masa ciwo,sannan na masa nuni da kafata. Da sauri ya dan yaye zanin jiki ba sai ya ga wani brown din ruwa mai din jini jini ya na bin kafa ta,tini ya sure ni ya na fadin Jiddah dauko mayafin ta mu tafi asibiti,yayi waje jiddah ta shiga a guje ta dauko mayafi na,a baya ta zauna tare da ni mu ka dauki hanyar barrack. Abun haushi mu ka tadda wani wawa go slow na ba gyara ba dalili,motoci ko motsawa ba sa yi. S.man ya ja ya tsaya,ya daki sitayari ya juyo ya kalle ni gaba daya na fita daga hayyaci na zufa ke keto min kamar an watsa min ruwa. Cikin zafin nama ya ja dorinar sa mai baki uku ya fita a guje,ya dinga kutsawa cikin motoci har ya kai ga abunda ya haddasa go slow,ashe check point ne,kurtu ne ke abunda su ka ga dama,daya wanda shi ya haddasa go slow din ya sunkuya gaban wata motar kaya,a lalle sai direban ya ba shi kudi,sauran biyun kuma sun tare mai gyada su na ciniki. Cikin zafin nama ya zabgawa wanda ya tsaida motar kayan dorina a gadan bayan sa,a fusace ya juyo ko da yayi ido biyu da C. Suleman sai ya tsorata ya ce identify your self Sir. A fusace ya ce Captain Suleman Matazu dan Uban ka! Tini ya dakawa yan uwan sa tsawa ya ce Behold we are in the presence of a Captain! SALUTE! Gaba daya suka kame gami da sarawa,da saurin kurtun ya janye tayoyi ya saki hanya ya na fadin go,go,go give way! Cikin zafin nama ya dawo mota a guje ya na fadin sannu Jauda,ya ja mota mu ka dauki hanya. Kafin mu karasa asibiti ya yi kiran Doctor Usman,mu na shiga barrack da isar mu asibitin mu ka tadda har sun fito da dan gado,Captain Suleman ya dauko ni ya dora kan gado,Doctor Usman tare da nurses duk sanye da kaki suka shiga tura gadon da gudu,Jiddah da S.man biye da su. Muna isa labour room da kyar Doctor Usman ya dakatar da S.man,ya ma sa alkawari za su yi iya kan kokarin su. Su ka ja kofa su ka rufe. Sai kai kawo suke shi da Jiddah,Doctor ya fito ya ce da shi Captain matar ka haihuwa za ta yi,ai har faya ta fashe,ka taho musu da kaya ne? Captain ya ce ina ana ta kai babu abunda na dauko,Doctor ya ce toh ya kamata,any moment from now za ta iya haihuwa. Ya ce toh bara na je na dauko,ya kalli Jiddah ya ce kira Anty Sa’a ki fada ma ta,bara na je na dauko kayan. Jiddah ta ce toh. Da sauri ya fice jiki na rawa. Tafiyar shi ba dadewa ba na sillibo dana namiji sak kamar Captain Suleman ya yi kaki,ina ji Doctor Usman ya na dariya ya na ce wa Alhamdulillah mun sami twin son din captain,wannan captain ne