← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direba ya tada mota mai gadi ya bude mu su gate su ka fice,Indija na daga ma Hajiya hannu har su ka kure,ta kama hanya sai ciki Nan ta taddani kancinyar Aliyu ya na bani abunci ni ma ina bashi,ba ko sallama ta wuce fooo ta shige dakin baki,mu ko ko ajikin mu wai an mintsili kakkausa [11:02pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 5:Da yammacin ranar juma’a,na ci ado cikin English wears,riga body hug da wando,ni gwanar sa wando ce dan ganin yanda ya ke karba ta abun ku da mai hipsna taje gashi na na faka shi a tsakiyar kai na irin yanda ake ma yara dan na lura Aliyu ya na so ya ga na yi irin haka dan maganar shi a kullum shi ne Jauda shin za ki tsufa kuwa? Na dubi kai na a madubi na ga na yi yar camas da ni,na janyo humrah na goga a hannu na sa’annan na shiga murzawa a jiki na kamar su bayan kunne,wuya dadai sauran su,haka dai na janyo sauran turaruka na kamar kala biyar na fesa sa su kadan kadan,tuni kamshi mai san yi ya mamaye ni,na sake kallan kai na a madubi,ni kai na nasan na hadu ba tare da na daura dankwali ba na nufi falo taran oga Da shiga ta falon Indija na gani zaune ta na kallo,ta ko bini da kallon da ita kanta ba ta san ta yi ba,na murmusa na ce yan mata kallo ake ne? Ta yi saurin mai da hankalin ta ga TV ta na fadin caf wankan baka asarar ruwa,ko ta yi ma kamar ba ta yi ba..kawai sai ma ta bani dariya.mai aiki na karimatu ta shigo ta durkusa gabana,madam na gama gugan,na ce yauwa Karimatu za ki iya hutawa ba wani aiki,ta ce thank you madam,ta wuce bangaran ta tana dan soshe soshe. Jim kadan na ji ana hoon,ina ji na gane oga ya dawo,ba jimawa sai gashi ya shigo falo,da gudu na je na yi huggn din shi,bisa da al’adar shi ya daga ni ya dire ya yi kissn kumatu na duka biyu,sai goshi sai kuma baki…ya na sunsani kamar mage ta cinci lada mai maiko,ya ce huuuuuum Ni’imatullah sunan kamshin mata ta,ita kuma jannatul na’im ce.. Duk wannan buduri akan idon Indija,ba kin ciki kamar ya kashe ta, Oga ya dada dagani ya dire,ya na juya ni madam anya kuwa wannan nauyi da na ji kin kara,ga wani kyau da sheki da ki ke,anya kuwa? Na dara anya kuwa me? anya kuwa ba baby na ba ne cikin dan cikin nan na kina rangwabar da kai cikin shagwaba shin akwai wani baby da ka ke da shi da ya wuce ni?yayi dariya mai fitar da sauti babu,amma dai ina nufin ko kin sama min karamin soja ne…. Indija ta yi gyaran murya ta ga abun ba na karau ba ne,Y Aliyu sannu da zuwa..gaba daya sai ya tsuke fuska ya sake ni,ni kuwa na sami damar sunkuyawa na cire ma sa takalmi,yauwa kin wuni lfy?baki washe ta ce lfy lau,daganan be sake walwala ba har sai da na gama cire ma sa takalmi yaron gida ya shigo da jakar oga na karba yayi side hugn di na mu ka wuce ciki cikin jin dadi da annashuwa,oga na fada min su Sulaiman sunce su na so su ci abuncin madam,wen za mu gayyace su ne? Na ce duk sanda su ke so.. Indija ta bi mu da kallo ta buga kafa aikin banza kunshi a duwawo,dallah jita baka kirin ta wani lafe cikin miji na,wa ya ga madara da milo!ni ina mamakin test din ya Aliyu da ya ke san wannan bakar matar haka,sai wani riri ta ta ya ke kamar gwal! mtsw ta ja tsaki…. [9:35pm, 11/11/2014] Khadija Sidi: Matar mu 6:kai tsaye C. Sulaiman ya shiga falon gidan Anty sa’a tare da doka sallama,ganin General kwance kan kujera Anty Sa’a na ma kafafuwan sa danna ya sa C. Salaiman dan dakatawa,cikin ransa ya na fadin Babbar yaya miji ya tsufa amma har yanzu lallaba shi ake. Anty Sa’a ta amsa wa’alaikumul salam,Sulaiman yau kuma daga nan za ka tsaya?ta dakata da dannan ta zauna gaban General,C.Sulaiman ya murmusa,ya karasa ciki ya durkusa cikin ladabi,barka da yamma Sir..General ya tashi zaune,barkan ka dai Sule,ka ji sako na ko?C.Sulaiman eh abunda ya kawo ni kenan ma Sir. General ya ce gud.C.Sulaiman ya dubi Anty Sa’a Babbar yaya mun wuni lfy?fuska ba walwala ta ce lfy lau. General ya ce Sule Madan di ta,yayar ka ta kamin korafi akan ka,ta ce ta ga ji da yanda kake gudanar da rayuwar ka,it is time you changed,time for you to settle down nd get yourself a wife..da sauri C.Sulaiman ya kalli Anty Sa’a,ita ko ta sakar ma sa murmushin mugunta domin kuwa ta san yau za a yi ta ta kare.. C.Sulaiman ya fara kame kame,Sir wallahi ai matar ce ban dace da samu ba tukun.General ya tsuke fuska dama ina za ka yi dace da samu tin da ba ka neman na gari?ai sai an nema ake samu,ya kallai Anty Sa’a Madam wani wata mu ke ciki yanzu? ta ce febuary,toh Sule na baka da ga yanzu zuwa karshen shekara wato watan december ka fito da mata a daura ma aure.. Zufa ta fara keto masa dan idan akwai abunda ba ya gaban C.Sulaiman ya bi bayan aure,ya rusunar da kai cikin neman sulhu,dan Allah Sir a dan kara min lokaci saboda..ba wani lokaci da za a kara ma Sule,General ya dakatar da shi,it is an order!C.Sulaiman ya dankame jin sautin muryar da General yayi amfani da,ya ce yes Sir. General ya tashi tsaye good,ina tsimayin ka.Madam bari na yi haramar masallaci ko? Anty Sa’a cikin farin ciki ta ce toh oga,General ya shige ciki,Anty Sa’a ta yi saurin bin bayan shi gudun korafin da C.Sulaiman zai ma ta. C.Sulaiman ya bi ta da kallo,yau dai burin ta ya ciki ta hada shi da General sanin duk duniya ba wanda ya ke jin maganar shi kamar General,bawai dan na matsayin sa na General ba ko na mijin yayar sa kadai ba,har da matsayin marikin shi tin ya na dan karami a sanadiyyar rasuwar mahaifan su a hatsarin mota.C.Sulaiman ya nisa gama da fadin burin ki ai ya cika babbar yaya,kai mata ma dai matsalar su da ban take wlh,ya tashi ya na gunguni ko sallama be damu ya mu su ba ya yi tafiyar shi. [9:06am, 11/12/2014] Khadija Sidi: Matar mu 7;8;9:Yau na wayi gari cikin aiki dan ganin na fitar da oga kunya.tin fitar Oga office na tada Karima da ke ba ta fara min aiki sai ya fita,ba dan girma gida na ba ma da sam ba na bukatar house help dan kusan rabin aiki na ni na ke abuna sai dai dan su wanke wanke da kuma yanke yanke wajan girki da dai abunda ba za a rasa ba. Ita ko Indija yar hutu na ko tsinke ba ta dauke min a gidan,hatta plate idan ta ci abunci in da ta ci nan ta ke bari. Azahar na yi na gama komai,cocoanut rice na dafa tare da cabbage nd chiken soup,sai kuma lemon kankana da madara,da kuma kunun madara da na dama musammam saboda C.Sulaiman,dan ya na balain son kunun.gida ya gauraye da kamshi abin ku da indoor,ina kallan Indija sai kai da komowa ta take sam ta kasa nutsuwa. Bayan na gama tsara komai cikin ma zu bin su na ce da karima ta kwashe ta kai min dining table,na yi maza na shiga wanka. Bayan fitowa ta daga wanka,ina zaune gaban madubi cikin atamfa dinkin bubu,atamfar fa ta karbe ni sosai,na dau jambaki ja ina gogawa a baki na sai ga oga ya shego da sallaman shi,cikin farin cikin na amsa ba tare da na juyo ba ina kallan shi ta madubi,sanye ya ke cikin kaki,hannun shi rike da kugu ya na kallo na ba tare da ya dada motsawa da ga inda ya tsaya ba. Na juyo ina murmushi oga oyoyo..ya girgiza kai ina da sake Jauda wannan jambaki haka?na mike tsaye ina murmushi be min kyau ne oga? Na karasa na yi hugn din shi,ya dago fuskata ya na kallo na,ya mi ki kyau sosai ma shi ya sa dole na yi maganin shi..kafin na yi magana ya fara kissn dina sai da ya tabbatar jambaki ya fita sa’annan ya sake ni ya na fadin haka na ke so. Cikin shagwaba na kalli kai na a madubi na ce ayya mana oga,wallahi ka ga duk ka goge min har da yar kwallata ta kissa.ya juyo da fuska ta mu na duban juna,yace madam kin san yanda na ke kishin ki kuwa? ur beauty is for me,not for the world to behold,idan na bari abokai na su ka ganki da jambakin nan toh na yi asara babba,owk? Na murmusa gami da sarawa yes Sir! Ya ja hanci na good girl,yanzu maza dauko mayafin ki mu je na bar bayin Allah sun kwaso yunwa musammam Suleman.cikin hanzari na ce toh,ina sane na ja wani dan karimin mayafi dan neman tsokana,ya na gani ya ce shi wannan na menene ne? Na yafawa oga,wani kallo da ya min ya sa na aje da sauri na dau mai dan girma ina dariya,shima dariyar ya ke hannun shi cikin nawa mu ka nufi falo. Nan mu ka tadda C.Sulaiman da C.Eze zaune.cikin sakin fuska na ce S.man sannu da zuwa,sunan da mu ke kiran sa da shi kenan ni da jiddah tin kafin na san Aliyu.ya murmusa Matar mu ki na lfy? Kafin na amsa oga ya ce wallahi ka sake kiran ta Matar mu ba za ka ci abuncin gida na ba! mata ta ce,ni kadai in ka yi zuciya ka auro ta ka kai ma Kin gani? Kin ga irin gurin da ya ke min ko kanwata?kawai murmushi na ke musu. Oga ya ce gwara dai ka kira ta kanwar ta ka.C.Eze ya ce go marry your own wife na,haba kin damu aboki ta!C.Sulaiman ya ce shege Eze,duk mu ka yi dariya. Bayan mun gama gaisawa na musu iso zuwa dining table,sai da na tabbatar sun zauna,ko wani mutsi na yi oga na bi na da kallo,na kalle shi cikin girmamawa oga ina daki
Chapter 2 · 0% Book details