← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma va ta maganin bacci ta sa mata a ruwa dan mu samu mu yi aikin mu. Bayan ta ba ta ruwan bacci ya sace ta,ta dauki kudi ta ce da mai gadin gidan ka wai inji matar ka ta ce ya siyo magani hawan jini da ke rubuce a yar takarda ya kai wa Hajiya,da har ya mata musu wai idan ya tafi wa zai yi gadi? Shi fa ba a taba aiken shi ba,ta ce da shi umarnin ka ne,sai ya hakura ya tafi. Bayan fitar shi ne na sami damar shiga gidan,inan cikin farfajiyar gidan na ji hon,daga baya aka sauke ka,kafin ka shigo na je na kwanta tare da matar ka ta na bacci ba ta san abunda ke faruwa ba… In banda hawaye babu abunda ke sauka daga idanun Aliyu. Shikan sa C. Suleman jikin shi ya yi sanyi. Ya dafa kafadar Abokin sa,ka yi hakuri Aliyu,kaddara ta riga fata,ka godewa Allah ba ka yiwa Jauda lahani ba,amma sai dai ka rasa cikin da take dauke da shi. Aliyu ya fashe da kuka kamar karamin yaro ya na fadin ka ce na rasa su duka biyun,Suleman na saki Jauda,na sake ta saki uku! C. Suleman ya dafe kai ya na fadin damn!damn!damn it Aliyu! Aliyu ya ci gaba ya zan yi da rayuwata? Ya zan yi da Hajiya? Ya zan yi da wannan gardin dan Allah? Ka fitar min da shi,ka shanya shi a rana sai jini ya fito daga idon shi,ka dake shi Suleman ka tabbata ka balla min shi,amma ina san shi da rai. Babba ya sa ihu ya na fadin dan Allah,ku yafe min,dan Allah! C. Suleman ya na fadin saboda motar banza motar wofi ka wargaza iyali,motar da ba za ta amfane ka ba dan wallahi sai na kona ta,idan na ga dama na hada da kai na kona!ya tisa kyeyar shi su su ka fita domin aikata abunda Aliyu ya umarta,shi ko Aliyu ya na nan ya hade kai da gwaiwa sai kuka ya ke. Can asibiti kuwa ko da na tashi daga bacci na kalli Anty Sa’a da ke tsaye kai na,na ce Anty Sa’a na gaji,dan Allah ki tada ni daga mafarkin nan. Cikin tausayawa ta ce ki yi hakuri Jauda,ba mafarki ki ke ba. Na lumshe idona in ba mafarki na ke ba da gaske ne kenan,Anty Sa’a dama Aliyu zai iya daga hannu ya dake ni? Dama Aliyu zai iya saki na? Saki kuma? Anty Sa’a ta fada a kidime! Hawaye na zuba daga ido na na ce mata saki uku Anty Sa’a…ta na salati ta na sallallami,me ki ka masa ke kuwa Jauda,na fashe da kuka ina fadin ban sani ba,wallahi bi ban masa komai ba,lfy mu ka rabu kafin ya tafi Abuja.Anty Sa’a ta rungume ni ta na fadin mazan kenan Jauda,mazan kenan,ita ma kukan ta ke…. [12:23pm, 11/24/2014] Khadija Sidi: [1:01am, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 36;37;38:Hajiya zaune a farfajiyar gidan ta tare da Indija. Sun yi dai- dai su na cin kaji na murnar sakin da Aliyu ya min. Baki cike da nama Indija ta ce ai Karima cewa ta yi ya ma ta dukan kawo wuka Hajiya,wata kila ma ta mutu,shi ya sa fa ta gudu garin su. Hajiya ta kada baki ta ce ai dama ya kashe shegiya mun huta,kai wannan mutumin Babba ya burge ni kin ga….tini maganar ta kare a iska ganin Aliyu ya banko gate ya shigo,daga ganin sa ba cikin hayyacin sa ya ke ba,biye da shi C. Suleman ne ya taso Babba a gaba. Ganin yanda suka canzawa Babba halitta ya sa hankalin Hajiya ya dada tashi,gaba daya ya fita daga hayyacin sa,idanun sa sun yi jajur kamar jini,sun hada masa jini da majina tafiya ma da kyar ya ke. Jiki na rawa Indija ta koma kusa da Hajiya. Aliyu ya durkusa gaban Hajiya yayinda C.Suleman shi ma ya durkusar da babban gaban ta,ya juya ya fita dan basu waje. Aliyu ya dubi Hajiya ya ce shin Hajiya ko kin gane wannan? Babba kasa kasa ya ke duban Hajiya,gaba daya ya kasa magana.Hajiya ta yi mirsisi ta ce ina ita ko mai kama da babba ba ta sani ba,ya ma za a yi Aliyu ya ma ta wannan tambayar? Aliyu ya dubi Babba ya ce ka ce Hajiya ce ta turo ka ka kashe ni…..Hajiya ta ce lahailahaillallah kun ga tsinanne,cewa na yi ka kashe shi?yaushe mu ka yi haka da kai Babba? Aliyu ya ce Hajiya kin san shi din kenan? Ta fara kame kame,eh toh ya dai taba min aiki haka,eh wanki da guga ba…cikin ladabi Aliyu ya ce Hajiya shi dai tuwo tuwo ne,ba a sake masa suna,har abada ke mahaifiya ta ce,amma Hajiya ba ki kyauta min ba..hawaye su ka fara zubowa daga idanun shi..Hajiya da hannun ki kin kashe min rayuwata Hajiya,Hajiya ba raba ni da Jauda ki ka yi ba Hajiya kin lahanta min rayuwa,kin dasa min ciwo cikin kirji na,kin sa na kashe dana tin kafin ya zo duniya,shin kin kiyaye kiwon da Allah ya baki?ina hakki na Hajiya? Ya za ki yi da hakkin Jauda….? Kuka ya subuce masa kawai ya tashi ya fice,jikin Hajiya da Indija sai bari ya ke,C. Suleman ya shigo,ganin shigowar shi ya kara mu su kwarjini,a tunanin su ya zo tafiya da Indija ne amma sai su ka ya tunkuda kafadar Babba dan su tafi,nan Babba ya fadi sumamme,ba tare da bata lokaci ba ya suri Babba ya sa a kafada ya yi waje da shi. Indija ta ce Hajiya kashe shi fa za su yi..Hajiya ta ce nasan halin Aliyu ba zai kashe shi ba,kar ki damu zai dawo hankalin sa ya zo ya bani hakuri,ta tashi da sauri ina zuwa bari na shiga bandaki,da sauri ta nufi ban daki sai zawo…. Kwana biyu aka sallame ni daga asibiti,na koma gidan Anty Sa’a. C. Suleman ya zo ma Anty Sa’a da zencen Aliyu ta ce sam ita ba za ta saurare shi ba in dai zancen Aliyu ne,ya jira General ya dawo ya masa bayani. Ni kuwa ban da aiki sai kuka,abinci ma ba na cin na kirki,na rabu da wanda na ke so har abada ga shi kuma dan cikin na sa ma na rasa,kwakwalwata ta kasa daukan abunda ke faruwa,gani na ke tamkar mafarki na ke. Washa gari General ya dawo,ransa in yayi dubu ya baci,ya dubi Anty Sa’a cikin fada ya ce dan me yasa?ga duka ga saki?irin sakin da Allah ba ya so?ni dai ina zaune gaban su kai na a kasa,ko kukan ma ba na iya yi. Anty Sa’a ta ce ni har yanzu ban san dalili ba Oga,dan Suleman ya zo min da zancen na yi watsi da shi,tin da yanzu ka dawo ka neme shi ka ji…A fusace ya ce dan ya rai na ni,ya daki yarinya ya sake ta kuma na neme shi?sakin da za a iya yiwa biko shi ake neman biko,bazan neme shi na ji takaici ba,zan iya masa abunda za a zo ana da sani. Ba dai ya sake ta? Toh idan Allah ya kai mu gobe za a je a kwaso kayan ta,Jauda! Ya kira sunana,na ce naam,ya ce kar ki damu,Allah zai mi ki sakayya kin ji? Na ce toh,amma dan Allah ina neman alfar ma,kar abun nan da ya faru ya taba aikin Aliyu. General ya ce zai yi kokari ya ga hakan ya faru.duka babu wanda be tausaya min ba,ana zancen cin mutunci na da aka yimin amma ni takan aikin shi ma na ke. [8:34am, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 39;40;41: Washagari C. Suleman ya je gidan C. Aliyu,falo ya tadda shi gaba daya ya rame ya lalace ko aiki be zuwa. Sanye da singilet da gajeran wando,ga kwalbar giya ta wisky wanda aka bude amma da alama ba a sha ba tukun aje gaban shi. C. Suleman ya dube shi tare da nuna giyan da dan yatsa aboki na ka dawo ruwa ne? Aliyu ya girgiza kai na so na koma,amma na gagara sha. C. Suleman ya dauke giyar ya sa ta gefe gwara kar ka koma,mu ma da mu ke ciki so mu ke Allah ya yaye mana. Duka su ka yi shiru na tsawon minti goma. Daga bisani Aliyu ya ce ya jikin Jauda? C. Suleman ya ce da sauki,su ka dada wani shirun wanda ya fi na fari,C. Suleman ya rasa ta yanda zai fadawa Aliyu sakon da aka turo shi. Aliyu? Ya kira sunan shi,Aliyu ya kalle shi ba tare da ya amsa ba, C. Suleman ya kau da kai tare da fadin Anty Sa’a da General sun ki su saurare ni. Aliyu ya girgiza kai,banga lefin su ba Suleman. Ya ce ka yi hakuri da abunda zan fada ma,Anty Sa’a ta ce a sheda ma ka yau za a zo a kwashe kayan Jauda…A firgice ya kalle C. Suleman,ya tashi ya ja hannun sa shi ko C. Suleman ya bishi ya na tunanin Aliyu ya sami tabin hankali. Daki na ya shigar da shi,kayan sakawa ta fal kan gadon. Ya nuna gadon kaga gadon nan?ka ga kayan nan?akai na ke kwana na ke wuni,a kudundune da kayan Jauda na ke kwana na ke wuni,ko bazan ganta ba na ji kamshin ta na ga kayan ta,ya na dan sassauta min radadi da ke rai na,Suleman sai kuma a kwashe kayan? C. Suleman ya tausaya masa ka yi hakuri Aliyu,ka yi hakuri. Aliyu ya hau gado ya tattaro kayana wanda hannun shi zai iya runguma,ya rungume ya na fadin na yi hakuri Suleman,na yi hakuri. C. Suleman ya ga ba zai iya cigabawa da ganin Aliyu a halin da ya shiga ba,ya fice da sauri.shi ko Aliyu yayi lamo cikin kaya na,idanu lumshe. A ranar aka kwaso kaya na,ranar sai da Aliyu ya yi karamar hauka. Bayan sati daya na sami sauki sosai,na hada nawa i nawa ni da jiddah sai yola gidan Inna ta. Inna ta yi matukar bakin cikin halin da na shiga,ga shi duk na lalace saboda rashin cin abunci. Ta min nasiha tare da adduar Allah ya zaba min wani mijin mafi alkhairi,ni kuwa a rai na cewa na yi ina ai ni da aure har abada,na gama aure a duniya. Sati na biyu da komawa yalo,wata
Chapter 7 · 0% Book details