Sashe 16
Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
biyar, ya ce minti biyar ko? Idan ki ka kara ni da ke ne. Na ce yes Sir. Bakin mota ya je yana jira,ya na nan tsaye ya ga Ema ya shigo da sauri ya bude gate ya ja gefe ya sara yayinda wata mota ke shigowa,C. Suleman ya bi motar da kallo ya na fadin yanda na ga Ema ya na rawan jiki komai aka yi General ne,Toh me zai kawo general da safe haka…..ganin wanda ya fito daga motar gaban C. Suleman ya fadi,hankalin sa ya tashi,ji ya ke kamar ya ruga a guje ya boye Jauda. Cikin farin ciki ya taho da sauri ya rungume C. Suleman ya na fadin amini na long time,ina sauka na ce wlh wajan ka zan fara zuwa,ashe ka dawo gidan nan,cikin zolaya ya ce wlh idan aka dauke Jauda babu wanda na yi missing kamar kai…..kamar daga sama suka ji murya ta ina fadin S.man ko ka yi fushin ne? Zuciya ta daya na fito. Ya na duban fuskar C. Suleman cikin neman amsa ya ce mai Jauda ta ke yi a gidan ka kuma? Ko har an yi auren kisan wutan ne? Gabana yayi mummunar faduwa,duk da ya bani baya amma ko a mafarki na san mai wannan bayan na san muryar nan,ban yi zato ba,ban yi tunanin zan sake dora idona akan shi..bare kuma a yau….. C. Suleman ya kame gaba daya ya kasa magana,ya rasa me zai fada,yawun bakin shi ya kafe. A hankali C.Aliyu ya juyo,fuska ta ya fara kalla,sannan ya mayar da kallan sa ga ciki na,Jauda.. ya kira sunana a hankali,ya waiga ya ce da S.mana dan Allah yi min bayani,shin dama cikin na ta be bare ba? [9:59pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar Mu 2 60;61;62:Da kyar S.man ya ce da ni Jauda shiga ciki,a hankali na juya ina takawa kamar mai koyan tafiya na koma ciki. C. Aliyu ya bini da kallo baki bude,sannan ya gane me ke faruwa, a fusace ya kifawa S.man a mari a kumatun shi har sau hudu,yanda ka san an yiwa dutse ko motsawa be yi. C. Aliyu ya ce Suleman waccar fa mata ta ce,shin dama za ka iya min haka?kasan fa komai Suleman,a gaban ka aka yi komai,ban da aminin da ya wuce kai,dama za ka iya cin amana ta? Auren kisan wuta ashe kai taka wutar ka ke kashewa?SULEMAN ya jijjiga shi,shi ko ya tsaya cak kamar gunki a fusace Aliyu ya na nuna shi da dan yatsa ya na fadin banda makiyi da ya wuce kai wlh sai inda karfi na ya kare! Ya shiga mota,da sauri Ema ya bude masa gate,ya figi motar ya fice. Ya na tafiya da sauri S.man ya shigo ya na kirana,ya taddani kwance na hada kai da gwaiwa ina kuka kamar rai na zai fita. Ya durkusa gaba na tare da fadin ba laifi na bane,ba na ki bane,ba kuma na shi bane,kaddara ce Jauda! Nan take ya bani lbrn da ya dada rudani,gaba daya na ji duniyar ta isheni. Cikin kuka na ce duk wannan lokacin Suleman ba ka fada min ba sai yanzu? Ya taso zai riko hannu na,na daga masa hannu tare da fadin stay away from me,kar ka zo kusa da ni…ya zube gwiwowin sa biyu a kasa ya na fadin Jauda ki taimaka min,ki ceto rayuwata kar da ki juya min baya,da fari a matsayin auren kisan wuta na yarda na aure ki,amma yanzu ke ce rayuwata,ke da dan da ke cikin ki kune rayuwata,billahilazim ba zan iya sakin ki ba ko da kuwa zan rasa rai na,ya kama kafata yana fadin gani durkushe gaban ki Jauda,Allah ba zai ba ni kyau ta ba ace za a kwace min. Wayyo Allah ni Jauda na shiga uku,abunda na fada kenan yayin da na yi sauri na tashi na nufi daki na,S.man ya biyo ni,na yi saurin shiga na ja kofa na rufe,na hau tsakiyar gado ina kuka. Ina ji yana buga kofa na ki budewa har ya gaji ya dai na.ban sake jin motsin shi ba ma,kuma shi ne karo na farko da na kwana a daki na tin da mu ka fara shiri da shi. Washagari da safe na shiryar da wuri na zauna a falo ina jiran Jummai ta zo na sallame ta dan ta ce da ni ta na son tafiya gida. A hankali na ji ana saukowa daga sama,na daga ido sai na ga S.man ne gaba daya ya fita daga hayyacin sa,na ma yi tsammanin ya tafi aiki. A hankali ya karasa saukowa ya zo gabana ya sa hannu ya tayar da ni tsaye,ya yi hugn dina na tsahon wasu yan mitina,har sai da ya ji ciki na ya fara motsi ya sake ni ya dan sukuya gami da dora hannun shi kan cikin nawa ya na murmushi,sai ga hawaye na zuba da ga idanun shi. Na tausaya ma sa,na tausayawa kai na na kuma tausayawa Aliyu. Sai da cikin nawa ya daina motsi ya dago ya kalle ni,yayi kissing dina sosai sannan ya ja ni mu ka zauna kan kujera,ni dai kamar babyn roba,ba um ba um um. Jauda? Ya kira sunana na amsa a hankali,ya dau hannuna ya dara bisa kirjin sa,ya ce kin ji yanda zuciya ta ke bugawa? Na daga masa kai alamar eh,ya ce haka na ke jin motsin dana a cikin ki,Jauda zuciya ta ce ke bugawa a cikin ki,cikin ki shi ya fara haddasa sa min soyayyar ki cikin zuciya ta. Na zame hannu na daga kan kirjin shi. Na ce Suleman ni matar ka ce kuma bazan taba bukatar saki daga gare ka ba,har sai in kai da kan ka ka gaji ka sallame ni. Murna a fuskar S.man har sai da hakoran sa suka fito ya sauko kasa ya durkusa na gode mi ki Kyautar Allah,Allah ya mi ki abunda ki ke min. Na murmusa na ce amma ka daina durkusa min. Ya yi sauri ya tashi tare da fadin na dai na. Na ce wacce za mu duba a asibitin Hajiyar Aliyu ce? Ya ce eh ita ce,na ce toh ka shirya mu je,kaga kafin ka gama na sallami Jummai. Cikin sauri ya rasa min ya ce yes Ma,ya haye sama da sauri. Na saki ajiyar zuciya,ba wai san Suleman na ke ba,amma ina tausayin sa fiye da Aliyu,hakan ya sa na yanke hukuncin kyautata masa ko da kuwa tawa zuciyar za ta na kwana ta wuni cikin kuncin tunanin Aliyu ba zan taba bari maigida ya sani ba,kuma ina ta addua Allah ya cire min Aliyu cikin rai na. [10:24pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 63;64;65:Bayan S.man ya gaisa da Hajiyar Aliyu sai ya fita ya bamu wuri. Tin da na ga halin da Hajiya ta ke ciki na sa kuka,har yanzu kukan na ke. Baki na rawa ta ce Jauda na zalunce ki,ki yafe min,dan Allah. Cikin kuka na ce Hajiya na yafe mi ki duniya da lahira. Hajiya ta nisa tare da fadin Jauda ke mutum ce,da na sani da ban raba da na da mace ta gari ba,jiya Aliyun ya zo waje na,ya zo nan ya na kuka kamar ran shi zai fita,na san daga gidan ki yake gashi kuma ya zo ya tadda ni a halin da na ke ciki,gaba daya sai na kara tsanar kai na. Na ce Hajiya ki dai na fadin haka,kaddara ta riga fata. Hajiya ta murmusa gami da kama hannu na,na gode miki Jauda,dan Allah ki na taya ni addua Allah ya yafe min,bazan tashi ba. Na ce Allah ya yafe mana gaba daya Hajiya. Na fito daga dakin Hajiya ina share hawaye na yi kacibus da Aliyu ya na shirin shiga dakin,ya tsaya cak ya na kallo na,na kalle shi na kau da kai gefe,ya karaso gaba na ya tsaya,na kauce da niyar wuce shi amma sai ya sake shan gaba na,kawai sai na sake sa kuka da ke dama a kusa na ke,ganin haka sai ya kauce ya bani hanya da sauri na yi hanyar fita Aliyu yayi tsaye ya na kallo na,ashe S.man ya ga shigar Aliyu saboda haka ya biyo baya na,ko da ya ganni na fito ina kuka besan sanda yayi hugn dina ya na rarrashi na ba tare da ya lura da Aliyu a wajen ba. Aliyu ya dunkule hannun shi,ji ya ke kamar ya kwalla ihu,da kyar ya ruke kan shi. Captain Suleman ga jani mu ka tafi mota,sai da ya tabbar na yi shiru sannan ya tada mota mu ka dau hanyar gida,ba mu yi nisa da tafiya. Ba wata mota ta zo da gudu ta wuce mu sannan ta sha gaban mu saura kiris mu yi gware S.man ya taka burki. Da Sauri S. Man ya rike hannuna ya ce ina zuwa,fitar shi ta yi daidai da fitowar Aliyu,a fusace ya sharawa Suleman mari gami da fadin ka sakar min mata ta, S.man be yi kokarin rama marin ba,ya ce ba matar ka ba ce Aliyu,mata ta ce,wallahi na rantse da wanda rai na ke hannun sa ba zan sake taba,ni da ita mutu ka raba takalmin ka za…Aliyu ya sake wanke shi da mari,ji ka ke tas! Ko motsi Suleman be yi ba. Aliyu ya nuna shi da dan yatsa wato kenan ka zabi mutuwar ka akan rayuwar ka!ganin S.man ya sa hannu a aljihu ya dauko bindiga hankali na ya dada tashi. Ya dau hannun Aliyu ya damka masa bindigar tare da kama hannun shi ya saita bindigar a goshin sa ya ce Aliyu in dai akan Jauda ne na zabi mutuwa akan rayuwa ta,go head kashe ni ka aure ta dan wallahi ba zan sake ta ba. Aliyu ya fizge hannun shi bindigar ta fadi kasa. Ya na nuna S.man da dan yatsa har ya shige mota,ya juya kan mota ya tafi a guje. S.man ya sunkuya ya dau bindigarsa ya mayar aljihu ya dawo mota,ido na tsumtsumu ya kalle ni gami da shafa gefan fuskata ba tare da ya tanka ba ya tada mota mu ka tafi gida. Ko da Aliyu ya koma asibiti ya tadda jikin Hajiya yayi tsanani,Indija zaune gaban ta sai kuka ta ke. Hajiya ta kalli Aliyu ta ce Aliyu dan Allah ka yafe min ka yafe ni dana,Aliyu ya ruke hannun