← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma dainawa zan yi,na ce sai mu ci me kuma kai da ba ka iya cin abuncin mai aiki ba? Ya ce sai mu na yin take away,na ce ba wannan maganar girki na zan na yi,ya ja na ja,sai ya hakura wai kar a batawa dan babyn shi rai shi ya sa kawai ya hakura. Haka mu ka isa gida,a gaban mai gadi da yaran gida na Oga ya fito ya bude min kofa,ya sure ni kamar baby ya yi ciki da ni.Nan mu ka ci karo da Indija ta yi sororo ta na kallan mu,da kyar ta ce sannu da zuwa Ya Aliyu,cikin Fara’a da ni kai na ban taba gani ya yiwa Indija ba ya amsa,yauwa Indija,ya wuce daki da ni ya dariya.Indija ta biyo mu ta labe a corridor nan ta ji Oga na kafa min dokoki,har da alalle yanzu kwanciya zan yi babyn shi ya huta.Indija ta dafe kirji baby? Ciki gare ta?cikin bacin rai ta juya da sauri ta nufi dakin kwanan ta ta dau mayafi da jaka,ta fice kamar mahaukaciya. Ba ta zame ko ina ba sai gidan Hajiya,ta na shiga ta fara rusa ihu,wayyo Hajiya,na mutu na lalace! A gigice Hajiya ta fito ta na fadin ke lfy? Rashi aka yi? Indija ta ce Hajiya ba gwara rashi da wannan abun da ya faru ba! Hajiya ta ja ta ciki,zauna ki fada min,duk kin sa hankali na ya tashi.cikin kuka Indija ta zauna dirshen a kasa,ta ce Hajiya matar Aliyu ta na dauke da juna biyu! Hajiya ta dafe kirji ta na salati ta na sallallami,wannan masifa da me ya yi kama? Ke wa ya fada miki? Indija ta ce labewa na yi na ji suna maganar,ba ki ga yanda ya ke lallaba ta ba kamar kwai..ta dada fashewa da kuka. Hajiya ta shiga rarrashin ta,yi hakuri bar kukan,wallahi idan har ni na cika uwar Aliyu cikin nan ba za ta haife ba,toh ta haihu na dau danta na ce na dauki me?jika ko dai jaki? Ishiru yar nan,ai da sake! Indija ta share hawayen ta,dan Allah Hajiya ki yi maganin abun da sauri,Hajiya ta ce sosai kuwa. Indija ta tashi Hajiya bara na koma toh,kila ta na can ta na kulla wani munafunci. Hajiya ta ce aifa,maza ki koma,amma ki kwantar da hankalin ki kin ji ko? Indija ta ce toh.ta tafi ta bar Hajiya ta na ta mita. [2:27pm, 11/12/2014] Khadija Sidi: Matar mu 16;17;18;19: Ina cikin kitchen ina kokarin hada abunda zan ci,dan ni yanzu komai na ci sai na amayar. Kamar da ga sama na ji ana Sallama,da sauri na amsa na fito wa zan gani? Kanwata ce jidda tsaye a falo da sauri na karasa mu ka yi hugn juna ina fadin mutan yola,yaushe a gari? Na ja ta mu ka zauna. Ta ce jiya jiyan nan,na ce da Anty Sa’a kar ta fada mi ki na mi ki suprise.iyye wato ke ba za ki na sauka gida na ba ko? Jiddah ta ce wannan karan rabawa zan yi,gidan kowa zan kwana biyu. Na ce yauwa ko ke fa. Ya hanya ya su Inna ( mahaifiyar mu)Jiddah ta ce lfy lau,ga tsarabar ki can ta ce na kawo miki. Na ce Allah sarki Inna ta,na tashi na dau kayan na kai kitchen na duba su daddawa ne da kuka,da cikwai da fura dadai sauran su. na dawo wajan Jiddah a falo sai na ga fuskar ta daure,ta ce da ni sis yanzu me wannan agwalumar ta ke mi ki a gida? Cikin nuna rashin fahimta na ce wafa? Cousn din Aliyu ta fada cikin tsiwa. Na dara na ce aw wai Indijan ce agwaluma? Auta ban san neman fitana dan Allah,ta ce me ta ke mi ki a gida? Na ce wai hutu ta zo,ni mantawa ma na ke ta na nan..caf amma sis shi ne ki ke korafin ban sauka gidan ki ba? Ai in har ta na nan ba zan iya kwanan gidan nan ba. Na dara auta rigima,toh ya zan yi ita da gidan yayan ta? jiddah ta girgiza kai ba dai ki ga daman yin komai ba,abubuwan yi ko akwai su,yarinyar da ki ka san ba kaunar ki ta ke ba za ki yarda ku zauna gu daya? Na mike tsaye tashi mu shiga ciki auta,zancena ya ishe ni. Na dau yar jakar ta ta na biye da ni ta na fadin ai aishikenan na yi shiru. Kafin Oga ya dawo Jiddah ta koma gidan General. Bayan dawowar sa na ke fada ma sa ina so ziyartar Anty Sa’a. Da fari ma hana ni yayi gaba daya,wai ni da ba ishasshen lfy gare ni ba,da kyar ya yarda amma da sharadin ba zai bari na yi driving ba sai dai na shirya in zai fita barracks ya sauke ni. Haka ko aka yi da sassafe na tashi,na damawa General kunun madara. Mu ka fito da Oga,mun dau hanya kenan C. Sulaiman ya kira Oga wai ya biya ya dauke shi motar shi ta sami matsala. Mu ka biya kafin ya fito na koma baya,da ya fito ya shiga gaba mu ka dau hanya. Bayan mun gaisa Oga ya ce da ni Madam Sulaiman fa ango ne? Na ce kai haba?C. Sulaiman ya daka masa harara,ya ce rabuda shi matar mu,karya ya ke,ina kallo Oga ya zungure shi,ya ce toh sorry matar ka. Oga ya ce wallahi Madam da gaske na ke General ya sa mishi ranar aure da ga wannan wantan zuwa karshen shekara,ya na murmushin mugunta ya ke maganar. Na dara kai Allah ya nuna mana. C. Suleman ya ce ai babu matar ne,ko za ki ba ni Jiddah? Oga ya ce wata Jiddar? Kanwar tawa? Allah ya sauwake! Na ce oga me zai hana? C. Sulaiman ya ja tsaki mstw isar da ba a isa ba,toh dan ka na mijin yayar ta ka isa ka hanani auran ta,har da wani kanwar ta wa,toh ka hana mu gani..Oga ya murmusa haka ka ce? Zan ko yi maganin ka kuwa. C. Suleman ya ce kai ma General na neman ka,Oga ya ce eh an fada min,amma a office din shi ya ce mu hadu. C. Suleman ya ce waya sani ma ko kai cewa zai yi ka karo mata..na zaro ido,Oga har da kwarewa,amma ba ka da mutunci a gaban Jaudar ka ke fadin haka,dan Allah kar ka sa ta yi bari cikin motar nan,hakan yayi daidai da isowar mu gidan General,na ce S.man bakin ka ya sari danyen kashi,duka su ka sa dariya. Na fito hannu na dauke da flask na zagayo ta wajan Oga,ba za ka shigo ka gaida Anty Sa’a ba? Ya ce Madam yanzu ya yi safiya ,amma idan na zo daukan ki zan shiga na ce toh,ya ce tak kia of urslf nd ma little one,na murmusa na ce adowo lfy na wuce ciki, C. Sulaiman ya ce ban fa gane ba,ka na nufin matar mu is carrying our baby? Oga ya dara ya yinda ya ke ko karin juya kan mota,yes mata ta is carrying my Baby. C. Suleman ya ce wow no wonder na ga ka karo takama da wulakanci,Oga ya ce kai ko iyali wasa ne? C. Suleman ya ja tsaki ya kau da kai gefe. Bayan shiga na gidan Anty Sa’a,Anty Sa’a ta min tarba mai kyau kamar yar da ta saba,bayan mun gaisa ta ce ya mai gidan na ki,na ce lfy lau,shi ma ya sauke ni ya ce sai ya dawo dauka na zai shigo yanzu ya yi safiya.Anty Sa’a ta ce haba wani safiya kuma ai ke kin san daga asuba bacci na ke karewa duk da ba yara gare ni ba. na janyo flask na ce ga kunun Oga,Anty Sa’a ta karba,yauwa kunun madarar ne? Kamar kin san ya na kewa kuwa. ni ko Jauda gani na yi kamar kin dab canza min,kin yi wani fresh kamar mai juna biyu,na sa hunnu na rufe fuska. Anty Sa’a ta dara haba ni fa ince,mashaAllahu,amma dai Jiddah ba ta sani ba ne da tuni ta guntsa min ni kuma na guntsawa Inna..kamar da ga sama mu ka ji muryar General,me ake guntsawa haka ni ma a guntsa min mana? Duk mu ka yi dariya,ya ce Jauda ce? Na durkusa Barka da safiya Sir,ya ce ku na lfy? Na ce lfy lau. Ya ce mashaAllahu. Anty Sa’a ta ce ga kunun Madara ma ta kawo ma ka.ya ce toh madallah Jauda,ba ki gajiya,Allah saka da alkhairi. Na ce amin.ya ce jiddah ba tashi ba ko? Anty Sa’a ta ce ina ai sai rana ta fito,a rai na ce zata dai na ne,komai lokaci ne. General ya ce Jauda ni zan wuce office,ba dai matsala ko? Na ce eh ba komai,adawo lfy.ya ce Allah ya sa,Madam sai ki biyo ni da kunun na wa ko? Anty Sa’a ta ce toh,General ya fita Anty Sa’a ta bi bayan shi. na cire mayafi na dan kishin gida ina jira Anty Sa’a ta zo ta min maganar Indija dan na san tini Jiddah ta labarta ma ta. Ile ko ta na dawowa ta fara min maganar. Ni dai sai hakuri kawai na ke cewa… [11:54am, 11/24/2014] Khadija Sidi: [4:41pm, 11/14/2014] Khadija Sidi: Matar mu 20;21;22:General be dade da shiga office ba Oga ya buga masa kofa,General ya ce ya shigo. Bayan shogowar oga ya sarawa General tare da fadin Morning Sir General ya amsa cikin murya mai nuna doka,Morning Captain,ka ji kiran da na ke ma ko? Oga a kame ya ce yes Sir!General ya ce have a seat,cikin girmamawa Oga ya zauna gaban General,ya mi kawa Oga wata farar envelop,Oga ya sa hannu biyu ya karba. General ya ci gaba,Request ne da ga ministry of defance,kamar yanda aka saba bayan every two years ko wani barrack ya na ba da soja daya wanda zai wakilce shi a exclusive course din da ake yi a Sudan na tsahon shekara daya,am very sure u knw abt it. Oga ya ce yes sir. General ya ce wannan karan kai aka zaba a wannan barracks din,za ku tafi nan da wata hudu,so ka shirya ranar Monday za ka je Abuja ka yi reportn a ministry.Oga ya ce yes Sir.General ya ce za ka iya tafiya. Oga ya tashi da sauri
Chapter 4 · 0% Book details