← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 18

Sashe 10

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta hana ka,ban da haufi akan haka. Kar ka manta ta dalilin ka aka ba ni Jauda,bare kuma kai da kanka ka ke nema. C. Suleman ya ce sai kuma hanzari ba gudu ba,shin me zan ce game da sakin da zan ma ta bayan na aure ta? Aliyu ya ce lokacin za mu fada musu gaskiya,har makasudin mutuwar aure na da Jauda tin da yanzu sun ki su saurare mu. Ka ga ba lefi idan ka ce za ka maido min da mata ta ta hanyar sakin ta na aura. C. Suleman ya saki ajiyar zuciya ya ce Allah ya sa mu dace,Aliyu ya ce amen. Aka fara kiran su Aliyu domin jirgin su ya fara himmar tafiya. Nan su ka yi sallama,da yiwa juna fatan alkhairi,Aliyu ya masa alkawarin kiran sa da ya sauka. Sati biyu da gama idda,sai ga C.Suleman a yola. Ya tadda ina Islamiya,Inna da jiddah kawai ya samu a gida. Bayan sun masa tarba na ban girma ya huta,ya tasowa Inna da maganar neman aure na. Inna ta ji dadin zencen tare da fadin ai zuri’ar Abubakar da ta Sa’a ba abun yarwa ba ne,ba komai sai fatan alkhairi. C. Suleman ya yi godiya sosai,a ran shi fadi ya ke Aliyu ne dai ya turo ni.kafin a tashe mu da ga islamiya har C. Suleman ya koma,so ban dawo na same shi ba. Bayan na ci abunci na huta,sai na haukan wanke wanke,ina cikin yi Inna ta zo ta same ni ta ce Jauda ko sanda ki na islamiya Suleman ya zo ya tafi. Na ce eh haka Jiddah ta fada min,na ce Allah sarki Allah ya yi ba za mu hadu ba. Inna ta ce,gashi kuma musammam dan ke din ya zo ba. Na ce dan ni kuma Inna,ta ce eh,ya zo neman iznin neman aure ne. Na murmusa gami da cewa wato S. man dai da gaske yar jiddar ta mu ya ke so ya dauke. Inna ta ce Jidda kuma?ai ni Jauda ya ce min. A hankali na zame hannu na daga cikin kwanukan wanke wanke na ce Inna ba dai ki fahimce shi ba,Jidda fa ya ke nufi. Ta ce ya azancin ban fahimce shi ba,da bakin shi ya ce da ni Jauda.. na girgiza kai na ce lalle ma mutumin nan ya yi shaye shayen na shi da ya saba ya fada ma sa karya kenan,wallahi Inna be da cikakken hankali….kul!Inna ta kwabe ni,kar in sake ji,dan ya zo neman auren ki sai ya zama kin sami damar cin mutunci Jauda? Na saka kuka,haba Inna,abokin miji na ne fa,abokin Aliyu ne..Inna ta ce abokin tsohon mijin ki dai ba mijin ki ba,wanda ya mi ki dukan kawo wuka ya mi ki sakin keta ba! Na ce wallahi ba na so,ba na san shi bazan aure shi ba Inna Inna ta dafa kafadata tare da fadin na riga na amsa masa Jauda..kuka na ya karu,na ce Inna sai ka ce ba kya so na Inna,inna sati uku fa kacal da gama idda ki ce na auri abokin sa? Inna ta ce ki kasance mai biyayya Jauda,Allah zai kasance tare da ke. Ta fita jiki a sanyaye. Na daura hannu na biyu bisa kai na ina fadin Innalillahi wa’innailaihirrajiun!ya Allah wannan jarabawar ka ce,ya Allah ka sa na gama lfy,Allah kar ka sa hankali na ya gushe……. Mu hadu MATAR MU KASHI NA BIYU…. Ta ku Khadija Sidi. mu 2 by khady sidi Posted by UMMU-ABDOUL on NOVEMBER 1, 2016 [01/11 22:47] Salma Ateeku: [2:30pm, 11/27/2014] Salma Ateeku: [10:57pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 1;2;3: Cikin sauri Jiddah ta shigo ta na fadin haba sis,dan Allah sis ki yi hakuri,kar ki manta ko wani tsananani ya na tare da sauki.. Cikin kuka na ce Jiddah aure fa,aure fa ai aure ba zaman wasa ba ne,bare kuma ace da Suleman zan yi,aminin tsohon miji na. Jiddah ta tausaya min matuka. Ta ja ni mu ka je dadi ki ta ta rarrashi na,har ta samu na dan yi shiru sai shassheka da ajiyar zuciya kawai na ke. A can birnin kano kuwa Suleman ya je gidan Anty Sa’a ya shedawa General yanda su ka yi da Inna,General ya ji dadi dama abunda ya ke so kenan dan shi ya na maraba da kudirin C. Suleman. General ya ce tinda haka ne sai Sa’a ta fadawa su baffa a sa rana mu je mu gabatar da kan mu wajen dangin mahaifin Jaudar ko?Anty Sa’a da ke zaune gefe uhum kawai tace. General ya ce toh kai Sule menene plan din ka? Kamar zuwa yaushe ka ke son auren ya kasance? C. Suleman ya dukar da kai ya ce san samu asa kamar watanni tara,ba dan komai ya zabi wattanni mai tsaho haka ba,sai dan ya samu lokacin ya yi daf da dawowar Aliyu. Nan fa General da C. Suleman su ka raba gari,General ya ce wata tara? Ina ba wannan maganar,wata tara fa? Me ya rasa da har sai ya kai wata tara zai yi aure? C. Suleman ya sosa keya,ya ma rasa karyar da zai yi,kawai sai zancen gida ya fado masa ya ce dama gidan da za mu zauna ne sai an karasa gini dan gidan da na ke ciki yanzu ya mana kadan. General ya dara aw matsalar gida ne? Indai wannan ne kar ka damu ka shiga gidana da yake first gate,ka ga tsakanin mu ma ba nisa sosai,ma ke duba ku ma….gaban C. Suleman ya fadi cikin ran shi fadi ya ke hasbinallahu wani’imal wakilu,dan a tsarin maganar shi da Aliyu ba zancen tariya ma. Be gushe ba General ya ci gaba da fadin saboda haka a wata daya za mu yi komai da komai matar ka ta tare. Kash ya zai yi ba daman musu,dole ya ce toh Allah ya saka da Alkhairi sir. General ya na washe baki a tunanin shi gwanin ta ya yiwa C. Suleman,nan kuwa gaba daya ya ruguza masa lissafi,ya ce ai yiwa kai ne. Ya na komawa gida ya yi kiran Aliyu,Aliyu na dagawa ya ce dashi Aliyu ka kunto min kura!nan ya fada ma sa yanda su ka yi da General. Aliyu ya ce duk yanda za a yi ya yi kar ya yarda a yi auren kwana kusa, C. Suleman ya ce zai jarraba ya gani,shi ma ba zai yarda a sa shi cikin keji ba. Har sun yi sallama zai aje wayar Aliyu ya ce Suleman Jauda fa? Ya ta karbi zancen aure? C. Suleman ya ce be sani ba,amma basan ba za ta so ba. Aliyu ya yi ajiyar zuciya. Su ka ki sallama. Bayan ya aje wayar ya dau taba ya fara sana’a…… [10:58pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: [4:58pm, 11/17/2014] Salmah Ateeku: 4;5;6; Na zama abar tausayi abunci ma ba na ci na kirki,gaba daya na lalace,hatta gashin kai na sai da ya karye dan rashin kula dan Allah ma ya sa ban taba sa relaxer ba.. Ina kwance Jiddah ta shigo ta ke fada min wai General da Anty Sa’a sun zo,kafin ta gama rufe bakin ta Anty Sa’a ta shigo da gudu na tashi na rungume ta ina fadin dan Allah Anty Sa’a ba na so,wallahi ba na san shi,dan Allah ki taimaka min kar a min dole tin da ni ba budurwa ba ce ina da zabi….Da gaskiyar ki Jauda ki na da zabi a musulunce haka ya ke!muryar General mu ka ji kamar daga sama,ashe ya na biye da Anty Sa’a,ta jani kan gado mu ka zauna,General ya ce mun san damar ki ce,amma sai mu ka nemi alfarma,bazan boye mi ki ba da cewa na yi ba zan goyawa Suleman baya ba akan zancen nan,amma ganin alkhairan da ke ciki da kuma yanda Inna ta ke son lamarin a dole na sa baki. Babu mai miki dole,amma mu na neman alfarmar amincewar ki dan mun san ki da biyayya,idan kin amince gobe za mu zo da baffanin Suleman wajan waliyan ki,idan kuma ba ki amince ba,toh hakan ba zai faru ba…na fashe da kuka ina fadin na yi biyayya,na amince. General ya ce Allah ya mi ki albarka. Ya fice. Anty Sa’a har da kwallan ta ta ce Allah ya saka mi ki da alkhairi,gaskiya kin isa ‘ya kin yi biyayya. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba,aka sa ranar aure na da C.Suleman wata daya dal. Ba ni ba shi kan shi C.Suleman da ya tsokano gobarar hankalin sa a tashe ya ke,sam be yi tunanin General za su ma sa wannan denyan aiki ba. Ya kira layin Aliyu ya ki shiga har ya gaji ya fara tunanin komawa ya ce da General ya fasa auren,amma tsoro ya hana shi,haka ya hakura ya zubawa sarautar Allah ido. Ta bangare na kuwa sunanan sun dage wai su suna shirya amarya,ni ko haushi ma su ke ba ni,duk tsumi,cikwidi ko zumar da Inna da kawayenta ke bani a toilet na ke zubarwa,haka zalika duk abunda aka tambaye ni shawara sai cewa na ke duk abunda su ke so zai yi. Ango kuwa ko kira na be taba yi ba tin da aka fara wannan budirin,haka ya fi min daidai dan daga shi har Aliyun babu wanda na ke kauna. Ni kunyar jama’a na ke ji,dan surutu kan na san sai na sha,wata hudu da mutuwar aure na na auri aminin miji na. [6:30pm, 11/17/2014] Salmah Ateeku: Matar mu 2 7;8;9:Ana sauran sati daya daurin aure aka kawo lefe,lefen ya yi kyau ko na budurwa sai haka. Ni kuwa ko a jika na be ma ishe ni kallo ba. Ranar juma’a aka daura min aure da C. Suleman,rai na kamar zai fita dan kuka,kukan da na yi ya ma fi wanda na yi sanda na ke budurwa. Washagari da safe aka dauki amarya sai kano. Anan gidan da General ya bawa Suleman na tare,gidan ya yi kyau matuka,sama da kasa ne,ni aka bawa kasan C. Suleman a sama. Abokan C. Suleman sun bukaci a musu sword crossing amma ya ce sam ba zai yi ba,bayan daurin aure babu abunda ya kara yi,sai su Anty Sa’a da su ka yi yinin su. Magrib na yi Anty Sa’a ta ce mutan yola kowa ya tattaro nasa ya nasa su bar gidan amarya,ba za su yi
Chapter 10 · 0% Book details