Sashe 1
Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Posted by UMMU-ABDOUL on NOVEMBER 1, 2016 [3:36pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 1 Babban falo ne wanda aka kawata shi da kayan more rayuwa.captain Sulaiman mamallakin gidan kwance kan doguwar kujera,ya ta faman danna waya,dogo ne,wankan tarwada mai kimanin shekaru 38 a duniya,Allah ya ma sa kyau da farin jini matuka domin kuwa kallo daya za ka masa ka tabbatar da baiwar da Allah ya bashi,ance mutum tara ya ke be kai goma ba,toh shi captain sulaiman abunda ya hana shi cika goma shi ne bin matan banza da karuwai.can gefe guda kuma Captain Aliyu ne aminin Captain sulaiman kwance a kan carpet,ya yi matashi da hannun sa ya na karanta littafi mai suna don’t be sad.Captain Aliyu sabanin captain sulaiman fari ne sol,dogo mai tarin suma irin na larabawa,ya na da kyau ga kyan hali da nutsuwa. Captain Aliyu ya nisa gami da duba agogo,a razane ya tashi zaune tare da fadin oh ma God,oh good God ashe haka lokaci ya ja Sulaiman?Captain sulaiman ba tare da ya kalle shi ba ya ce toh ni ina ruwa na da lokaci officer? Captain Aliyu ya gyada kai haka fa,mu da mu ke da iyali mu muka da mu da lokaci,su tuzurai ko sai dai a tabin yarima a sha kidamtsw Captain Sulaiman ya ja tsaki ka ga kar fa ka takura min,saban shiga kawai,dan ka yi aure kowa sai yayi?an fada ma da ka yi auren fi na jin dadi ka yi?duk abunda ake ma ina samu ni ma,sa ma ni ina da damar zabi,yau inna sami fara,gobe na dau baka,jibi na dau leba..Allah ya sauwake ma,haka dai za ka kare,wlh rabin dadin da na ke ji ba ka samu mu,ko kwata ma,ka yi aure ko ka sake hali pls,Captain suleman ya dubi Captain Aliyu wani hali kenan?Captai Aliyu ya murmusa kwartanci.captain sulaiman ya koma ya kishingida ai Aliyu ko na yi aure ba zan dai na ba,ba ka san tuwo tuwo ne ba,amma na makota ya fi sweet,ya ja tsaki gami da mikewa tsaye,duk randa ka ji ka a kabari ka dai na…ina!captain Sulaiman ya katse shi,ai kafin lokacin na shiryu.ba a yiwa Allah wayo dan ubankaya doki kafadar sa,captain Sulaiman ya na sosa in da ya dake shi ya ce dan Allah ka gaishe min da matar mu,matar ku kai da wa? Captain Sulaiman ya kanne ido ni da kai abokinaAllah ya sauwake,jauda mata ta ce ni kadai…haba ai na zaci abun ka abu na ne,matar ka mata ta ce…ba tare da ya kara sauransa ba ya wuce zai fita,ka ci gaba da fadin haka watarana sai na zubar ma da hakora,ya fita ya doka masa kofa,Captain Sulaiman ya kwashe da dariya,dama abunda ya ke so kenan,dan ya ga Aliyu ya tsani ya kira sunan matar shi da matar mu,shi ko tin da ya gane ya sami mafaka….. [7:03pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2:Jauda sunana,Jauda Mansur Alkasim,Allah ya yi wa Mahaifina marshal Mansur Alkasim rasuwa kusan shekaru goma da su ka shude,Alhamdulillah Allah ya rufawa bayan mahaifin mu asari,sam ba mu wulakanta ba.Mu biyu ne gun iyayen mu,ni da kanwata hauwa wacce mu ke kira jidda.maihaifiyar mu ta ba mu tarbiya sosai da kuma taimakon General Abubakar Wali wanda yake almajirin mahaifiya ta sanda ta na amarya sanadiyyar mutunci da sabo mahaifiyata ta sa mahaifi na ya sa General a makarantar sojoji,hakanan nan har ya kammala karatun sa ya zama cikakken soja. Ni Jauda baka na ke,amma irin wannan bakin mai kyau,ina da manyan idanu dan shi ya fi komai girma a fuskna,ina da gashin idanu zara zara gami da gashin gira.hancina ba wani tsayi gare shi sosai ba,amma dai ba yabo ba fallasa ya na da kyau,haka zalika zagun baki.ban da tsayi sosai amma kuma ba gajera ba ce ni,ba na daga cikin matan da ake kira busty,amma ina da hips matuka da mazauna dan wani sa’in kawaye na kan tsokana ta da cewa da ga sama yar tsut,daga kasa ko kamar wacce za ta kai tusa birni ko ma wasu suce anya ko Jauda wannan kaya na ki be rinjayar ki? Da taimakon General aka daura min aure da captain Aliyu,wanda ya ke aminin kanin matar sa Anty Sa’a,wato Captain Sulaiman. [8:32pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 3:Sanye na ke cikin rigar kakin mijina,bisa da al’adata duk safiyar Allah na kan sa rigar shi ta kaki tare da p-cap din shi yayinda zan shiga kitchen.tin yana mita wai ina ci ma kaki fuska,na rasa inda zan na sawa kaki sai kitchen,har ya zo ya hakura domin kuwa duk da kakin ya min yawa nesa ba kusa ba,ya kan saukar min kasa sosai har ya dan dara gwiwa na,hakan ya sa ban damuwa na sa wando ko zani,gashi hannun rigar ya fi karfi na,haka na ke nadewa abuna.hakan ba karamin kyau na kewa oga ba dan so da yawa da ya ganni cikin shigar sai ya daga ni ya dire wai ina masa kamar yar tsana Dining area na ke,na gama hada komai na brkfast tsaf ina shirin shiga na duba oga sai ga shi ya fito sanye da kakaki,abin ka da farar fata,yamasa kyau ga wani kwarji da Allah ya ba shi.Ya ware hannun shi come hia my baby,na karasa da sauri ya daga ni ya dare,dax my baby,ya mini side hug mu ka karasa dining table,kamar yanda ya saba ya ja kujerar da zan zauna baya ya kame gami da sarawa,ya ce my lady first.Na murmusa gami da zaunawa ya yinda ya sauke hannun shi,shi ma ya ja tashi kujerar ya zauna. Na dube shi cikin jin dadi Wallahi ina san ka ogaya dara har sai da hakoran sa su ka fitoi love you more madam.ka tashi lfy? Ya ce lfy lau,gashi na ma so na makara ba ki tada ni ba,na rangwabar da kai bayan ba in na tada ka da wuri zalina ka ke ci..oh toh na gane in da ki ka dosa yarinya,ni ba babu inda na dosa oga,da na ga zai maida maganar wani abu na yi saurin janyo plate kar ka kara makara sosai,maxa mu ci abunci,ya lakaci hanci na sarkin wayo. Mu na cikin wannan ya na yi kwatsam kamar daga sama mu ka ji sallamar Hajiya babar Aliyu,biye da ita Indija ce yar kanwar hajiya rike da jakar Hajiyar.Hajiya ta shigo a fusace shin ba ki amsa sallama ne?a rikice na mike tsaye ganin Hajiya a kan mu,ina fadin Hajiya sannu da zuwa,yanda na ga ta bini da kallan banza ya sa na tuna kafafuna duk a waje su ke na yi maza na koma na zauna.Aliyu cikin ladabi ya ce Hajiya yi hakuri,ba mu ji ba ne..mstw ta doka tsaki dama ina za ka ji wannan mayyar ta ka sa ta tsare,wai haka ka lalace?aikin ma ba ka fita da wuri Ali?ka na soja?Cikin ladabi ya ce yanzu na ke shirin tafiya,ya durkusa Hajiya ina kwana?lfy,ya kamata a zo a tafi dai.Ni ma na durkusa p-cap dina a hannu na ce Hajiya ina kwana? Ahasale ta ce da ban kwana ba kya ganni? Na dada sun kuyar da kai.cikin yanga Indija ta ce ya Aliyu ina kwana,lfy shine amsar da ya bata ba tare da ya kalli inda ta ke ba,na lura ya kai makura wajan bacin rai.cikin rawar murya na ce Hajiya ku zauna dan Allah na kawo mu ki brk fst..ke da dallah yi ma mutane shiru,har kin kai matsayin da zan zauna na ci jagwalgwalan ki da ki ke barbadewa da magani?cikin nuna rashin jin dadi Aliyu ya ce haba Hajiya ta,me ya yi zafi haka? Hajiya ta kame baki ikon Allah,za ka rama ma ta ne? Ya kau da kai Allah ya ba ki hakuri.ta ce amen,dama hutu na kawo indija,sai a sannan ya dago ya dubi Indija haba Hajiya ta,ya katuwar budurwa kamar indija za ta zo hutu gidan mutane?Indija ai ta wuce wannan stage din…Hajiya ta doka Salati Lailahalillallahu muhammada rasulillahi sallahu alaihi salam,Ali za ta raba ka da yan’uwan ka kenan,Indijan nawa ta ke da za ka dubi tsabar ido na ka ce wai tafi karfin hutu?cikin wayo na dan zunguri Aliyu,Hajiya dan Allah ki yi hakuri,yi min shiru mu na fuka duk ba ke ki ka jawo ba! Aliyu ce Hajiya ta Allah ba ki hakuri..ta ce amen ta ya fito indija ke zo mu je kisa mai gadi ya shigo mi ki da kayan na ki! Ya tashi hajiya ta bara na dan taka miki,yi zaman ka,ba na bukata.ta na tafiya ta ke maganar Indija biye da ita,na ce Hajiya sauka lfy,ta ce in ma ba’a ki ke min garau zan sauka,Atoh.jiki sayaye na bi bayan ta da kallo yayin da kwalla ke kokarin sauka da ga idona,da sauri Aliyu ya zo gabana ya durkusa,pls Jauda,pls i beg of u kar ki min kukan nan na ki mai daga hankali….. [10:10pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 4:kafin ka ce mai tini hawaye ya bude kamar famfo,cikin rudani Aliyu tashi ya ja hannu na ya zauna kan kujera,ya daura ni kan cinyar shi ya na rarrashi,yi hakuri Jauda,ya kamata ace kin saba da halin Hajiya kin dai na zubar da hawayen ki saboda ita,na san bata kyautawa amma ki yi hakuri komai zai wuce kin ji ko? Na gyada kai. Ya ce yauwa goge hawayen toh,ki na yar soja matar soja ki na kuka haka? Na goge hawaye ina murmushi,ya ce yauwa dax my girl bari ki ga brk fast din ma ni zan yi feedn din ki,ya jawo plate ya shiga ba ni abunci a baki. Ito ko hajiya da fitar su ta kira yaron gida ta mika ma sa katuwar jakar Indija ya kai ciki. Ta kalli Indija da fatan dai ba ki manta musabbabin zuwan ki gidan nan ba ko? Indija ta ce Hajiya ban manta ba. Hajiya ta ce toh kar ki ba ni kunya,ki tabbatar hakin mu ya cimma ruwa,in dai ni na haifi Aliyu toh sai ya rabu da yarinyar nan ya aure ki,dan ko zaman kishi ban yarda ku yi ba. Indija ta dara an gama Hajiya,ta budewa Hajiya mota ta shiga,Hajiya a sauka lfy,Hajiya ta ce Allah ya sa,duk yan da ake ciki ki na kira na a waya ki na sanar da ni Indija ta ce toh.