← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mace wacce ta amsa sunan ta mace,fara ce sol kamar balarabiya,doguwa ga ta a dire ba maza kadai ba ko yan uwanta mata su ka kalle ta sai sun kara,sai na ga na zama mummuna a gaban ta. Sai dai kash shigar da ta yi ba na yan mutunci ba ne,riga ce body fitting gown,gaba ya ya bi jikin ta ya kwanta,kai ba dankwali sai wani dan mayafi karami da ta yana,ta na taunar cingum. Ba sallama bare sannu ta kalle ni ta ce ke Ina Suleman? Na kalleta na watsar na cigaba da karatu,ta kara so ciki sosai ta tsaya tsakiyar falon ta shiga kwalla ma sa kira. Ni ko duk da na kule sai na nuna ban ma san ta na yi ba. Da ta yi kiran ta ji shiru sai ta dawo gare ni,ke wai a masu aikin wata iriyar mara kunya ce?ko ki na nufin dadiro ya ke da ke? Na ma ta banza,ta zo ta rufe min qur’ani ta ce ke ba da ke na ke magana ba? Na dago ido na watsa ma ta harara sai da ta dan ja baya, na aje qur’ani a gefe,ina murmushi na ce ban ga laifin ki ba,shi wanda ki ka zo nema shi ya jawo ko wani kare da biri ya ke iya tinkara ta. Tace what?ni ce kare da birin?ina daga zaune na murmusa sunayen sun miki kadan ko? May b ana kara miki da shasha,mahaukaciya wacce ba ta san darajar kanta ba ko? A fusace ta damko ni yau sai na san waye ubanki,waye mai daure mi ki gindi a garin nan! [10:56am, 11/22/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 40;41;43: let go of my wife!C. Suleman ya daka ma ta tsawa yayinda ya ke saukowa da ga bene,a firgice ta sake ni,a hankali ta maimaita your wife?cikin takama ya karasa saukowa,da muryar umarni ya ce da ni Jauda shiga ciki,na kalle shi da niyar yin musu amma karfin kallan da ya min ya sa na hukara na shige na bar su su kadai. Ta bi ni da kallo ta ce matar ka fa Suleman,aure ka yi dama dan cin amana? Me wannan ta fini in banda namiji ma butulu ne!ya zauna kamar ba da shi ta ke magana ba,ya kunna sigari ya busa hayakin sama. Cikin takaici ta ce da kai na ke magana fa,for your information ina dauke da cikin ka wata uku! Ya saki murmushin mugunta toh ki gaggauta fadawa uban sa ya baki kudin abortion ko na ragon suna…ta fusata wani uban na sa da ya wuce kai! Ya ce na zaci rabona da ke four month kenan? Ta iska na dura mi ki cikin ko yaya? Kin san hali na Ramsy wai dan na tattaka ki ba karamin aiki na bane,maza ki je ki samo mai cikin nan,kar ki sake sa kafa a gidan nan,in kuma ba haka ba sai kin yabawa aya zakin ta,shasha kawai. Ramsy ta fashe da kuka kan wannan baka mummumnar matar ta ka ka wulakanta ni? Wlh sai ka san ka yi da yar halas!ta fita fuuu,C. Suleman ya bi bayan ta ya ce da Ema duk randa ya sake bari ta shigo gidan a bakin aikin sa. Ema ya ce i swear Sir i no go let dat happen,C. Suleman ya ce good for you. Ranar ko da wasa ban sake yarda mun hadu C. Suleman ba,shi ma kuma be zauna a gidan ba. Gashi dai ba san C. Suleman na ke ba amma gaba daya rai na baci ya ke duk sanda na tuna fuskar Ramsy. Sam C. Suleman be sake kawo zancen ta ba,ni ma kuma ban masa ba,na ciki na ciki. Kwanci tashi ciki na ya kai wata biyar,ya fito sosai amma dadinta be min muni ba sai ma dada budewa da hips dina yayi kuma kirgina ya cika sosai ba kamar da ba. Anty Sa’a kance daga ganin yanda cikin yayi tsini baby boy ne,ni ko dariya kawai na ke ma ta. Anan asibitin barrack na ke awo na. C. Suleman kuwa wasa wasa cikin nan ke hada mu magana. Wani yawon dare duk ya sauke,kusan kullum a gida ya ke kwana. Wata rana bacci mai nauyi ya danne ni,alarm di na yayi kara na kasa tashi, ashe shi kuma Oga ya na falo ya na jira na tashi shi ma yau dai mu yi sallan tare,ko da ya ji shiru kawai sai ya shigo dakin da kan shi,ya tadda ni kwance na yi dai-dai ina bacci,da ke ana zafi riga ta da kadan ya dara cinyata mara hannu,na saki gashin kaina ba tare da na daura dankwali ba dan na sami iska,ga shi ciki na da ya dan fito sai ya kara min kyau. Gaba daya yanayin C. Suleman ya canza,ba tare da ya san abunda ya ke ba ya zauna bakin gado kusa dani ya daura hannun sa bisa ciki na,da mamakin sa sai ya ji motsi yayi sauri ya dauke hannun sa,da fari yayi zaton tunanin sa ne kawai,ko da ya mayar karo na biyu ya ji dagaske motsin ne kuma cikin nawa ne ke yi,shi kadai ya ke murmushi har sai da cikin ya dai na. Ya sunkuya ya sunbaci ciki,a hankali ya shafa gashin kai na ya ce my child is growing in your womb Jauda,nd i love the child,thank you for bearing him. Ya bi jiki na da kallo,tin ranar da ya min wanka ya ke yaki da zuciyar shi akan abunda ta ke aiyana masa akai na,saboda haka ne ko matan banza be iya kusanta dan da ya kusance su ni ce ke zuwa ransa,balain sha’awata ya ke amma karfin zumuncin shi da Aliyu ya hana shi kusantata ya na cikin hayyacin shi,ga shi wanda zai dan rage zafi da su a waje gaba daya tawa bukatar ta danne ta su. Ya saki ajiyar zuciya,da da yanda zai yi ya sake zuciyar shi da ya sake,da ya yarda da ita ya huta. Ya sake kissn ciki wanda hakan yayi daidai da farkawata,ko da na bude ido sosai na ganshi zaune kusa da ni sai na yi sauri na ja bargo na rufe jiki na. Ya murmusa irin wannan murmushin na yarinya ai na ga komai,ya ce na ji ki shiru ne na zo na tashe ki mu yi sallah. Ba tare da ya jira amsa ta ba ya tashi,idan kin yi alwala ki same ni a falo sai mu yi nafilan tare. Ya fice. Na yi ajiyar zuciya har ga Allah tsoran C. Suleman na ke,da zai gane da ya dai na shigo min daki,sai da na dau tsahon wasu mintina hankali na ya kwanta sannan na tashi na yi alwala. Shi ko S.man da ya koma falo tuni ya shiga sakar yanda zai yi ya sa na saki jiki da shi na dai na jin tsora. Na fito sanye da hijab,ya bini da kallo mu ka hada ido gaba na ya fadi na yi saurin kau da kai na. Wani abu ya dasu cikin ranshi,wato ba Aliyu ba,babu dalilin da zai sa ya cigaba da cutar da kan shi akan abunda Allah ya halatta masa,abunda ya ke fada cikin ransa kenan yayin da na zo bayan shi na shimfida dadduma ta,ya juyo ya na kallo na cikin ran shi ya na fadin i can’t hold on to this any more,i want her i must have her ko da kuwa shi ne abu na karshe da zai aikata a duniya ba zai iya sake wani jinkirin ba… [10:56am, 11/22/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 44;45;46:Da kyar ya tashi mu ka yi sallah,ni ko cikin zuciya ta fadi na ke ko dai S.Man ba lfy ne? Mu na idar da sallah na yi sauri na koma daki. Ya kishin gida ya na murmushi ya ce ki gama gudun ki Jauda mu na nan tare,zuciya ba ta da kashi hakan ya sa tawa ta kamu da son ki..da sauri ya tashi zaune jin abunda ya fada,wai so fa ya ce,ya sake komawa ya kishingida ya na muhawara da zuciyar shi,shin so ko sha’awa kadai wanne ya ke min ne? Washagari gidan Anty Sa’a na wuni,kullum nasihar ta na bi miji na,na ja shi a jiki na taimaka ya sauya halaye,ni ko gani na ke na yi kadan da na ja S.Man a jiki har ya sauya hali kai na,yanda na ga mata na bin shi tun abun ya na bani haushi har na zo na saba da ganin su suna zuwa neman shi ,gasu duk babu wanda na fi kyau sai dai su fini,amma ko da wasa ban taba fadawa Anty Sa’a ba. Kafin Sallah magrib Anty Sa’a tace na koma gida na kar dare ya min,na ce yanzu korata ki ke Anty Sa’a,ta dara ta ce ba haka ba ne,kin san with your condition be kamata ki na yawo ke kadai ba,da daidai kin haife min yaro na ne sai ma ki kai daya ban damu ba. Ina dariya na ce ashe abun ba dan ni ake ba,san kai ne. Ta ce ya za ta yi da ai yafi kanwa. Duka mu ka yi dariya. Ina shiga gida ana magrib,na sallami Jummai sannan na shiga na yi wanka. Da ke idan dare ya yi cikin daki na nake wuni sai na sanya tight dina iya gwiwa da riga ta body hug mara hannu,ta dame ciki na abun sha’awa. Na shafe jikina da humrah. Na taje kai na ina shirin tifkewa waya ta ta fara kara,na bari na je na dauka,Jidda ce ke kira na cikin farin ciki na daga ina fadin yan mata na,bayan mun gaisa ne take fada min yau fa S.man ya je yola. Na ce ya je yalo? shi ne be fada min ba ko ina da sako?ta ce ai ya ce aiki ne ya kawosu be ma dade ba ya juya kafin magrib ma ya kira Inna ya ce sun iso lfy,Inna ce ta ce ma na yi kiran ki na fada mi ki ki masa godiyan alkhairina da ya ma ta. Toh kawai na ce ba tare da na tambayi abunda ya ma ta. Har mun yi sallama ta yi sauri ta ce dani Sis an koma makaranta fa,an kuma baki admision amma da Inna ta fadawa S.Man yace ba
Chapter 13 · 0% Book details