← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 18

Sashe 6

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya koma mota,har motar ta su ta fita ina daga mu su hannu,na juya na koma ciki ina kewar Oga. Da la’asar sakaliya gaba daya na ji jiki na ba dadi,gaba na sai faduwa ya ke. da kyar na lallaba na shiga kitchen na hadawa Oga abunda ya sauwaka. Tin wajen 12 ya sanar da ni ya gama da ministry,amma sai yamma sosai zai juyo. Na samu na gama komai na shiga na yi wanka,na sanya wata rigata wacce ke tsayawa iya ka gwiwa ta,kai na ya na sarawa saboda haka sai na saki gashi na,ya sauko har kafada ta. na duba waya ta domin jin inda Oga ya ke,na ji shirun ya yi yawa,amma sama ko kasa na nema na rasa,har na gaji na hakura,na haye gado na na dan kishingida. An yi haka ba da dadewa ba na ji ana buga min kofa,daga kwance na ce yes,karima ce? Da ga waje ta ce ita ne. Na ce shigo. Ta shigo dauke da ruwan faro da kofi. Na kalle ta dan ni na san ban ce ta kawo min ruwa ba,ya aka yi Karima? Ta ce Madam ruwa ne na kawo maka. Na ce but Karima I did nt ask for it,did I?ta na dan murtsika ido ta ce Madam na yi tunanin za ka bukata ne. Da kamar zan ce ta tafi dashi sai na sake shawara,owk thank you,mi ko min. Ta miko min na bude na dan kurbi kadan na aje sauran kan bedside,karima ta juya ta fita ta na dan soshe soshe. Banyi cikakken minti goma da shan ruwan ba na na ji kasala ta karu,jikina too weak gaba daya na rasa abunda ke min dadi,a haka bacci mai nauyi ya sace ni. Oga ya kira waya ta tin kafin jirgin su ya tashi amma sai ya ji ta a kashe,haka ya hakura ya taho ba a san ran shi ba. Direban da ya kai shi Airport shi ya dauko su shi.da isha’i Oga ya iso gida,suna ta hon amma mai gadi be bude musu ba,Oga ya fito ya ce da direban may be mai gadin sallah ya ke,bari na sauka a nan kawai. Ya sallame shi ya tafi. Oga ya shigo cike da mamaki,babu mai gadi babu alamar sa. Ciki ya wuce kai tsaye,ga mamakin sa sai ya ga wutar falon a kashe,hankalin sa ya tashi ya na fadin ina Jauda!da gudu ya shige daki ya bankada kofar daki na,me zai gani? Wani katan gardi ne,daga shi sai gajeran wando,ya kwanta dai dai kusa da ni hannu shi zagaye da jiki na yayi hugn di na,ga dogon wandon shi aje kan gado na… [11:59am, 11/24/2014] Khadija Sidi: [1:57pm, 11/15/2014] Khadija Sidi: Matar mu 28;29;30;31:Oga ya tsaya cak,ya kasa fahimtar abunda ke faruwa. Ko da gardin nan ya ga Oga ya tashi a guje,ko wandon shi be iya dauka,ya bangaji Oga da ya tsaya a hanya ya fita a guje. Nan Oga ya dawo cikin hankalin sa ya yi wuf ya bi gardi,ina tini ya tsere ma sa. Da gudu ya dawo ciki,ya tadda ni ina baccina hankali kwance. Kawai saukan mari na ji ban san hawa ba,ban san sauka ba! A gigice na tashi ina fadin Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Be bari na gama wartsakewa ba ya ciro belt din jikin shi ya rufe ni da duka,fadi na ke wayyo Allah,Aliyu me na ma ka haka,dan Allah Aliyu za ka kashe! Idon shi ya rufe!ya ce gwara na kashe ki tin da nufin ki ki kashe ni,macuciya,azzaluma,maciya amana. Ashe cikin na ki ma na shege ne! Na sake! Na wuntsilo daga kan godo na fado kasa tsabar zafin duka,na ruke kafar Aliyu ina fadin dan Allah Aliyu,dan Allah dan Allah! Abunda baki na ke iya furtawa kenan! Ya cigaba na tsane ki,na sake ki,na sake saki uku! Na kurma ihu na kamkame kafar shi,ya janye kafar yayi wurgi da ni gefe.Nan na fadi sumammiya. Ya sa kai ya fice ya barni kwance cikin jini. Daga nan ban sake sannin inda na ke ba,sai bude ido na yi na ganni kwance kan gadon asibiti,a hankali na ke bin dakin da kallo,Anty Sa’a da Jiddah na gani zaune sun yi tagumi,daga bakin kofa kuma C. Sulaiman ne tsaye,da shi mu ka hada ido,da sauri ya ce babbar yaya ta farfado. Da sauri su ka zo su ka tsaya kai na. Anty Sa’a ta ce Jiddah kira doctor,Jiddah ta fita a guje,ni ko na kasa magana sai ido kawai. Anty Sa’a sai sannu ta ke min. Jim kadan Jiddah ta shigo tare da Doc. Usman,ya dube ni sannu madam,ya yi dan dube dube,sannan ya ce bayan jiki akwai abun da ke mi ki ciwo? Maimakon na bashi amsa,kawai sai na fashe da kuka mai ban tausayi,hankalin Anty Sa’a da Jiddah ya dada tashi,Jiddah ta sa kuka C. Suleman ne ya ke rarrashin ta,yayinda Doc. Usman ya ce ina bukatar hutu,ya min allura,tini bacci ya sace ni. Bayan fitar doctor Anty Sa’a ta ce da C. Suleman,Sule ka ga halin da jauda ke ciki ko?tin jiya fa da mai gadi ya kira ya sanarda mu ba ta farfado ba sai yanzu,kuma mai gadi ya tabbatar ma na mijin ta ne ya mata wannan dukan kawo wukar a dalilin da shi ma be sani ba. Ku ma Aliyun be zo ba har yanzu. C. Suleman ya nisa babbar yaya tinda ki ka min waya na ke neman Aliyu a waya amma wayar shi a kashe,amma yanzu gidan zan je na same shi.Anty Sa’a ta ce toh,ka fada masa ya yi sa’ar zubdawa yar mutane da jiki,dama be da mutunci haka Sule?wallahi duk na tsane shi,ga shi general baya nan,na ma kasa fada ma sa. C. Suleman ya ce ai gwara kar ki fada ma sa ki bari sai ya dawo.bari na je wajan Aliyun.Anty Sa’a ta ce toh. Haka ya tafi ya barta cikin jimami,ita ko jiddah kuka kawai ta ke. Da fitar shi ya sake kiran numbar Aliyu,ya yi sa’a ta shiga,bugu biyu ya daga,C. Suleman ya ce ka na ina? Ya ce da shi ya na gida,ya ce toh gashinan zuwa. Be zame ko ina ba sai gidan Aliyu. A waje ya tadda shi,ya tsaya gaban shi,Aliyu ya bude mota ya shiga ba tare da ya kalle shi ba ya ce kai ni gidan Hajiya. C. Suleman ya kalle shi ya ga duk ya fita daga hayyacin shi,ba musu ya tada mota sai gidan Hajiya. Sun tadda wata mota na kokarin fitowa daga gidan Hajiya,C. Suleman ya dakata ya na jira motar ta fito su shiga. Gaba daya hankalin Aliyu ya koma kan motar,ya kurawa direban ido har sai da ya gama fitowa,a hankali kamanin shi ke dawowa cikin idon shi sanda ya gan shi kwance da dani..da karfi ya dakatar da C. Suleman ya ce kar ka shiga,shi ne,mu bishi!mu bi waccar mota! Da sauri C. Sulaiman ya juya akalar motar har sai da kora ta tashi ya na fadin shi ne wa? Yayinda ya bi motar. Aliyu ya ce zan ma ka bayani daga baya. trafic lyt ya tsaida su,Aliyu ji ya ke kamar ya zama tsuntsu ya tashi ya caf ko gardin nan. Ko da C. Suleman ya gane,sai ya fita ya barwa Aliyu motar ya ce da Aliyu ya biyo bayan shi. Hankali kwance ya kutsa tsakankanin motoci,ko da ya je motar da suke bi sai ya bude ya shiga. A tsorace mai motar ya ce lfy? Kai malam ba ka hankali za ka shigo min mota? Goshin bindiga ya fara nuna masa ta yanda mutanen da ke waje ba za su gani ba,ya daga masa I.D card tare da fadin sunana Captain Suleman Matazu,ina bukatar ka rage min hanya zuwa gida na. Tini zufa ya rufe mai mota,murya na rawa ya ce toh toh,ba laifi Captain. Aka ba su hannu,da kyar ya ke iya driver,C. Suleman ya sa shi a hanya,Aliyu na biye da su… [1:57pm, 11/15/2014] Khadija Sidi: Matar mu 32;33;34;35:kai tsaye gidan C. Suleman suka nufa,ko da mai gadi ya leko ya ga oga ne da wani sai ya yi sauri ya bude gate su ka shiga,Aliyu ma ya biyo bayan su,ya ja ya yi fakin a gefe. C. Sulaiman ya ce ai sai ka fito mu shiga ko?mai mota ya dibirbirce dan Allah dan annabi officer ka yi hakuri..! C. Suleman ya fito ya daka ma sa tsawa get down!ciki na rawa ya fito, C. Suleman ya karbe mukullin ya tisa kyeyar shi suka shiga ciki.da shigar su falo Aliyu ya biyo su,ko da mai motar ya ga Aliyu sai ya durkusa ya na fadin ashe soja ne,wallahi ba su fada min ba,ni babba tawa ta kare! Cikin mamaki C. Suleman ya tsaya ya na kallan su. A fusace Aliyu ya ci kwalar Babba,ya zuba masa mari har sau hudu sannan ya sake shi ya zube kasa hanci na jini,shi ma ya durkusa gaban shi ya dago fuskar shi ya na fadin tin yaushe ku ke cin amana ta?tin yaushe ka fara kwartanci da mata ta? C. Suleman ya ce what the hell?dan uban ka!dan ba ka da kunya?duk matan da ke garin nan ka rasa wacce za ka na tumurmushewa sai Matar mu?matar soja dan uban ka! Na ga alamar ba a sha ka ba ka na yaro,yau zan maka kaciya da harsashi dan ubanka! Ya fara jan wandan Babba. Babba ya sa ihu,wallahi shiri ne,shirya mu ku aka yi,sharri mu ka mata,babu abunda ya taba hada ni da ita,akasali ma ban taba ganin ta ba…Aliyu ya zube a kasa jiki ba laka,C. Suleman ya dada marin Babba me ka ke nufi? Waya sa ka? Baki fashe ya ce Hajiya Mairo ce,ita da Indija….hawaye na zuba daga idanun Aliyu ya ce da C. Suleman shikenan Hajiya ta ta kashe ni! C. Suleman ya ce da Babba fada min yanda abun ya faru. jiki na rawa ya fara labarta mu su.Indija ce ta yi kirana wai suna da aiki,kuma Hajiya ta yi alkarin mallaka min mota idan har aikin ya yi kyau,ni kuwa yanda na ke san mota zan iya aikata komai,amma wallahi da na san soja ne,da bazan yi ba. Bayan na amince,su ka hada ni da yar aikin gidan ka Karima,wacce aka sa ta sace wayar matar ka,aka
Chapter 6 · 0% Book details