← Book details Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 18

Sashe 18

Matar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

sak! Ya na hanya Jiddah ta yi kiran sa cikin hanzari ya daga tare da fadin Jiddah ya? Ta ce S.Man an sami karuwa,cikin farin ciki ya ce Alhamdulillah,ya ce ya lafiyar mata ta? Ta ce lfynta lau,ya ce MashaAllahu,me aka samu?ta ce baby boi….be ankara ba ashe wata katuwar mota ta shawo kwana daidai da lokacin da shima ta shi motar ta sha,tini ta gwabji motar S.man motar ta wuntsila gefe guda…! mutane su ka sa ihu aka zo ceton ran Captain Suleman. Shiru shiru na haihu,an gyara ni an kai ni dakin hutu amma banga C. Suleman ba shi da ya ce ranar da na haihu zai zuba ruwa a kasa ya sha. Ina nan kwance Jiddah ruke da baby na Anty Sa’a ta shigo idanun ta sun yi jajur,ta karbi baby a hannun Jiddah ta matso kusa da ni ta min sannu,ko da na kalli fuskar ta sai na ji gabana ya fadi,na ce Anty Sa’a lfy? Ta kau da kai ta ce lfy lau Jauda,sannu. Na ce ban ga Suleman ba,ba a fada ma sa na haihu ba ne? Ta ce eh wayar shi ba ya shiga,ta ce jidda zo ruke shi ina zuwa,ta fita da sauri. Na kalli Jiddah na ce Jidda ba lfy,taimaka min na tashi dan Allah,ta ce ki tashi ki je ina? Na ce ma ta kawai ki taimaka min dan Allah. Ta zo na dafa ta na tashi,na sanya mayafi na,na fito ina taku da kyar saboda dinkin da aka min,Jiddah biye da ni hannun ta dauke da baby. [11:30pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 73;74;75: Bayan Anty Sa’a mu ka bi,na ga ta shiga office din Doctor Usman,na bi ta zan shiga muryar General ya dakatar da ni ya na fadin yanzu Doctor ina mafita?ko za a fitar da shi ne? Cikin mamaki na ce shi wa? Na ji muryar Doctor Usman ya ce with all respect Sir,amma sorry to say idan Captain Suleman ya dade shi ne ya kai 24hours da rai saboda ribs din sa gaba daya sun lalace Sir. Gaba daya ji na yi kamar an sheka min ruwan sanyi,na daskare a tsaye. Cikin office kuwa Anty Sa’a dake tsaye a bayan General da Captain Aliyu kuka ta sa,yayinda shi kuma Captain Aliyu ya runtse ido. General ya fara ma ta fada ya na fadin Haba Sa’a,idan kuka za kiyi toh ki fita ki ba mu waje. Sai ta yi shiru ta na hawaye kawai. General ya ce toh dan Allah Doctor kar matar shi ta sani ka ga tana cikin danyan jego. Ban san sanda na bude kofa na ce da Doctor Usman kai ni wajan miji na Usman. Ya girgiza kai ya tashi ya fito na bi bayan shi,suma su Anty Sa’a,Jiddah,General da Aliyu su ka biyo mu. Da shiga ta dakin da Suleman ke kwance gaba daya tsigar jiki na ya tashi,ganin shi kwance karafuna sarke a kirjin sa,duk sanda yayi tari ko amai jini ke zuba. Na tsaya ban karasa gaban sa ba ina hawaye,a hankali ya bude ido ya kalli in da nake tsaye,ya murmusa. Anty Sa’a da General suka shigo,biye da su Aliyu ne da Jiddah,ta miko min baby jiki ba laka na karba na karasa gadon S.man,ina kuka na ce Suleman ba ka cika alkawari ba,na haihu ba ka zuba ruwa a kasa ka sha ba. Abun mamaki sai na ji bakin shi radau ya amsa da ki yi hakuri Jauda,Allah be nufa,juyo min dashi na ga fuskar shi. Na juyo da fuskar baby,ya murmusa ya ce da ni an masa hudu ba? Na girgiza kai alamar ah ah. Ya kalli Aliyu ya ce Aliyu ka yiwa dan na ka huduba. Aliyu ya sa hannu ya karbi baby ya masa huduba,ya mikawa Jidda ta karbe she. Captain Suleman ya kalle ni ya ce daya tamkar da dubu,dubu jiran mutum,Jauda kyautar ubangiji. Allah ya saka mi ki da alkhairi,abunda ki ka min Allah ya mi ki. Na ruke hannun shi ina kuka,ya kalli Aliyu ya ce Aliyu ga Matar mu,ga kuma dan ka,dan Allah ka kula da shi tamkar kai ka haife shi,ya sake cewa Aliyu ka yafe min amma ban yi danasanin auren Jauda ba,sai ma alhinin barin ta da zan yi a yau,Jauda ita ce rayuwa ta,ita ta kyautata rayuwata,yau gashi zan koma ga mahillici na a cikakken mutum. Dakin kowa ya yi shiru kamar ba kowa. Captain Suleman ya ja hannu na,na dada matsawa kusa da shi,ya na murmushi ya ce Matar mu ki koma gidan tsohon mijin ki bayan rai na,ya kalli General ya ce dan Allah Sir a mayar da wannan zuri’ar mazau nin….harshe ya karye,maganar S.man a duniya ya kare,ya ruke hannuna gam kamar zai karya yatsuna. General ya sunkuya kunnan shi na dama ya masa kalmar shahada,Aliyu ya rude Anty Sa’a da Jiddah su ka kuka,ni Jauda na nemi kuka na rasa,ina ji ina gani da karfi Suleman ya karbi kalmar Shada yayinda ya damke hannuna,sai kuma shiru,ya saki hannuna! Nan take na fadi Sumammiya. Aliyu ya rungume shi ya na kuka,su Anty Sa’a kuwa kuka har da ihu. General ya sa hannu ya rufe idanun Suleman,Doctor Usman ya ja mayafi ya rufa masa,a tare su ka sarawa gawar. General ya ce da Doctor Usman ayi a hada kayan sa ya na so da anyi sallar juma’a a sallaci Suleman dan ya sami alfarmar Jama’a.Doctor ya sara gami da cewa yes Sir. Tsaye na ke a falo,na kwantar da Suleman da na lallaba da kyar ya yi bacci a kafada ta. Yau shekara biyu da rasuwar S.man,ya rasu ya bar min dan sa mai kama da shi sak kamar yayi kaki ya tofar. Na shafa kan Suleman cikin rai na nace Baban ka mai sunan ka was very special,Allah ya baka halin sa na gari. Ban ji shigowar sa ba sai kawai ji na yi yayi hugn dina ta baya,na lumshe ido tare da fadin ka kusa ba ni tsoro Oga,ya juyo da ni,ya karbi Suleman yayi kissing din shi a goshi tunda ba dana na tsoratar ba ai da sauki. Aliyu wanda aka sake daura mana aure bayan rasuwar Suleman da kusan shekara daya na matukar san dan aminin sa tamkar na shi,hakan ya sa a kullum na ke dada kaunar shi. Ya ja hannu mu ka zauna kan kujera ya zagayo da hannun shi kafada ta,na kwantar da kai na jikin shi,yayinda Suleman ya dada kamkame Captain Aliyu cikin bacci. Alhamdulillah. Ta ku Khadija Sidi. Thanx for readn. For comment or correction txt dis number 07018583783 SHARE THIS: Twitter Facebook Google Advertisements    Loading... RELATED Ina daraja 3d post Diya mace 2nd post Matar mu na khadija sidi PREVIOUS POST Ina daraja final post NEXT POST Matar mu na khadija sidi Notify me of new comments via email. Blog at WordPress.com. RECENT POSTS Kururuwan Shaiɗan 3rd December 11, 2016 KARNINMU 4 November 23, 2016 KARNINMU 3 November 18, 2016 KARNINMU 2 November 16, 2016 KARNINMU 1 November 15, 2016 Matar mu na khadija sidi November 1, 2016 Matarmu 2 by khady sidi November 1, 2016 Ina daraja final post October 18, 2016 TEXT WIDGET This is a text widget. The Text Widget allows you to add text or HTML to your sidebar. You can use a text widget to display text, links, images, HTML, or a combination of these. Edit them in the Widget section of the Customizer . ARCHIVES December 2016 November 2016 October 2016 September 2016 May 2016 ummu -abdoul MENU

   

Chapter 18 · 0% Book details