← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 22

Sashe 8

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

zame masa kamar motsatsiyar tsohuwa, ya dinga tambayar kansa tun farko me ya gani a tare da ita ya yarda ya daukota har kasar sa ya aureta??? Tsaki yayi ya tsallake ta ya wuce dakin sa. Wanka ya fara yi ya tsaftace kansa, yana jin wani abu na tsirga masa a zuci da gangar jiki, wanda yafi kama da jin kunyar Ubangiji. Wankan janabar da bata aure ba alhalin ga matar sunnar ya tsallake tana nata sabon Allahn. Wannan wace irin rayuwa ce??? Idanun sa a rufe ya hau gadon sa ya kwanta. Addu'a yake cikin ransa in yana da rabon dainawa kafin ya mutu, Allah yasa ya daina......!!! **** Tunda Askirama da kansa ya shigo ya ce da Fulani gobe ne tafiyar Sa'ade gidan Yarima jikin ta yake a sanyaye, don bata san wane irin riko da karba Sultana zata yi mata ba, tunda ita ba jinin gidan bace, duk da su Humaira suna fadin bata da matsala. Amma ga Sa'aden sai murna take, very enthusiastic ga tafiya makaranta, bata tunanin komai da ya danganci abinda zata ta tarar banda kasancewa dalibar Turkish University. Don a daren Fulani ta zaunar da ita a gabanta. Don ta ga murnar tata har ta so ta yi yawa, tun azahar ta kammala daure kayanta tsaf. Kadan ta bari wadanda bata cika amfani dasu ba. Allah-Allah take garin Allah ya waye ta kama hanyar birnin tarayyah. "Sa'adatu bani hankalin ki nan" inji Fulani. Ta dago fararen idanun ta ta dubeta, wadanda a lokuta da dama suke wani irin sheki da walainiya (sparkling eyes) wanda shine babban sirrin kyawun Sa'adatun. Fulani tace. "Na ga sai rawar kai kike, ki kama kan ki, gidan Yarima zaki je, sannan matarsa asali ba musulma bace, sannan ba bahaushiya bace, don haka dole ki kula da tarbiyyar kan ki da kan ki, ki maida hankali akan abinda ya kai ki kawai, ba ruwan ki da rayuwar su, ban da sa-ido, banda daukar zance, banda shiga shirgin da ba'a sanya ki ba. Tsakanin ki da su yi na yi bari na bari. Ki dinga taimaka mata da girki da ayyukan gida tunda ita ma'aikaciya ce. Na hore ki da kama mutuncin kanki, ko ya kike da namiji kada ki yarda ki kebe da shi, Ko hannun ki namiji ya taba cikin shege zaki yi, kin ji na gaya miki?" Sa'ade ta gyada kai cikin fahimta, sannan ta dan zaro ido ta ce "to ai gidan ba maza ko?" Fulani ta hana kan ta yin dariya sabida yadda muryar Sa'ade ta koma razana zallah. Tace "shi mai gidan ma ai namiji ne, kuma ba muharramin ki bane ba, don haka matsayin uba yake a gare ki, ki kama kan ki, ki rike mutuncin ki. Allah yayi miki albarka ya saka albarka a neman ilmin ki. Ga waya karama na saya miki duk halin da kike ciki ni zaki kira ki gaya min, ban yarda ki bawa kowa lambar ki ba". Sa'ade ta gyada kai cikin murna a lokaci guda tana mika hannu don karbar karamar wayar siemens da Fulani ke mika mata. Kawai sai ta ji Fulani ta hada da hannun ta ta janyota jikin ta ta rungumeta... "Ki yafe min Sa'adatu don Allah ki yafe mini..." "ni baki yi min komai ba Fulani, na yafe miki abinda na sani da wanda ban sani ba. Nima ki yafe mini!" Sallamar tasu is very emotional da ta fiddo hawaye daga idanun kowaccen su. Washegari daya daga cikin direbobin gidan karkashin rakiyar kuyangin Fulani Bilkisu mata guda biyu maimartaba yasa suka dauki Sa'ade zuwa Abuja a daya daga cikin motocin 'Askira Emirate'. Tun asussuba suka kama hanya basu isa Abuja ba sai karfe takwas na dare. Inda Allah ya taimake su shine sun yo guzurin abinci da abin sha wadatacce wanda har suka iso Abuja sallah ce kawai take tsayar dasu a gidajen mai na gefen hanya. Suna fitowa daga mota Sa'ade tayi mika....ta ware ido tana kallon kyawawan gidajen estate din malamai na NTNU kamar kana kasar Istanbul. Ashe ba ginin masarauta kadai ne gini mai kyau ba, ginin Turkawa ma abu ne mai matukar kyau da daukar hankali. Ita dai tunda take bata taba ganin kananan gidaje masu tsari da kyawun zubin wadannan ba, ko ya mutanen cikin gidan suke? Koda yake Fulani ta ce turawa ne, ai sai turawan.... "wannan gida wanke hannu ka taba". Sa'ade ta ce cikin ranta. Daidai lokacin da daya daga cikin kuyangin da suka zo tare ta yi mata magana ganin ta shagala a kallon gidan "ranki ya dade mu karasa daga ciki ko?" Suka isa ga entrance na gidan suka hau danna kararrawa, suka yi har suka gaji ba'a bude ba, a lokacin Sultana na kwance a falo ta sha ta kai mata karo, tun misalin karfe 6 na yamma take kwance har a lokacin bata san inda kanta yake ba. Allah ya kawo Uche (kukun gidan) zai shiga da cefane, kasancewar yana da mukullin gidan ta kofar kicin ta baya. "Hey! What do you want here?" Ya tambaye su. Aka rasa mai amsawa don 'yan rakiyar Sa'aden basa jin turanci, sai itace ta gayamasa daga Askira suke, sun zo wajen masu gidan ne. Ya tambayeta ko Dr. Sageer ya san da zuwan su? Ta ce "ya sani" a takaice, domin bata da tabbacin hakan, Allah-Allah take ta sanya hakarkarinta akan shimfida sabida gajiyar zaman mota data kwaso. Wayar sa ya dauko ya kira wata lamba yayi magana cikin harshen turanci, ya kalle su, sannan ya maida wayar aljihun sa ya ce su biyo shi. Ta baya suka shiga ta kofar kitchen suka kurda zuwa falon gidan. Nan Sa'ade taga mace jajawur kwance magashiyyan a dandaryar tayals, gashin kanta ya baje ya rufe fuskarta, Uche bai ko dubi inda take ba ya bude wani daki yace su shiga nan ne dakin bakuwar. Sannan ya ce su bashi minti 15 zai kawo musu abinci. Kafinnan ga ruwa da lemo su sha. Tsaruwar dakin ya burge Sa'ade, duk da bai kai dakin ta na Askira ba amma daki ne mai tsari irin na turawa babu tarkace sam a cikin sa. Gado ta fada tana ce da Fariha daya daga cikin 'yan rakiyar ta in an kawo abincin ta tashe ta tunda ita tana fashin sallah, in taci abinci sannan tayi wanka. Uche ya kawo musu abinci mai rai da motsi suka ci suka koshi, sannan Sa'ade ta fara yin wanka, ta shirya cikin kayan barci tabi lafiyar gado bayan ta kure iyakwandishan, sukuma kuyangin suka kwanta daga kasa. Ba wanda ya nemesu har washegari. Da asubah suka kama hanyar Maiduguri lokacin Sa'ade tayi sallah ta koma barci. **** Sai karfe takwas na safe Sa'ade ta tashi, ta duba babu 'yan rakiyarta, sai ta tuna sun ce da asubah zasu kama hanya, tsaki tayi tana mitar shine ko su tashe ta su yi sallama. Wanka ta fara yi, kafin ta ji cikin ta yana kiran chiroma, a gurguje ta shirya tana fadin bari in bi su kitchen din tunda sun manta da mutum a gidan. Tana kokarin fita bayan ta murda kofar dakin taji ta yi karo da mutum....Wani irin sassanyar kamshi mai huda zuciya, coupled with his gait and geniusness, beautiful elegant face wadda babu far'a sam a cikin ta. A kiyasce yadda ta kimanta shekarunsa zasu kai talatin da biyar zuwa da shidda. Alamu sun gama nuna ya gama samun duk wasu achievements na rayuwar dan adam. Kama daga ilmi na addini dana zamani, sannan ya zauna da kafafun sa ya gama kama kasa. Da farko ta dauka Askirama ne a gabanta (mai martaba) sabida tsabar kamannin su, saidai data lura sosai sai ta fahimci wannan akwai tarin kuruciya da hasken boko a tare da shi, bi ma'ana yaro ne mai jini a jika, babu ko tsillin furfura a kwantaccen sajensa zuwa gashin kansa, wanda ya kwanta luf a gefen fuskarsa. A duniya bata taba katari da mutum mai cikar kamala da kyawun suffa kamar sa ba, ga wani irin kwarjini da ya banbanta shi da sauran maza. Sarauta ta gama bayyana kanta a komai nasa. His lips are so luscious kamar ana basu extra kulawa, fatar jikin sa fresh kamar haifafen kasar Morocco. Sai ta ga kamar ta taba ganin sa, somewhere else da bazata iya tunawa ba.
Chapter 8 · 0% Book details