← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 22

Sashe 5

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

zafin kiyayyar namiji sai wadda aka yiwa irin auren da aka yi min. Auren dole is a challenge da ba duka mata ne zasu iya jure shi ba. Kwana bakwai a tsakani na sayarwa da makocinmu gidan, na kulle kudi na sai tasha, na hau motar Maiduguri, don na kudurce a raina ni da Damaturu har duniya ta nade. **** Aka sauke mu a tashar Bama, daga nan na rasa ina zan nufa. Ga yunwa ga gajiya. Haka na hau tafiya a gefen titi dauke da kullin kaya na. Tunani yayi min yawa har bansan na hau bisa titi ba, a yayin da zungureriyar motar ta shararo a guje, duk kokarin da direban yayi bai yi nasarar kauce min ba sai da ya kwashe ni ya watsar bisa titi. Jini kuwa ya balle ko ta ina, baka jin komai sai salatin mutane. Sauran motocin dake biye dasu in convoy duk suka dakata a gefen titi. Fadawa suka fito bisa umarni suka ciccibe ni suka saka a mota sai asibiti. Ban samu kai na ba sai bayan awanni uku. Na farka na ganni a wani hamshakin asibiti. Likitoci farar fata fal a kaina, ga karin ruwa ga karin jini, juyawar nan da zan yi sai na yi tozali da wani babarbaren mutum ma'abocin zati da kamala, mai yawan murmushi, yasha nadin rawanin da ya tabbatar min yana da alaqa da babbar sarauta. Baza'a kira shi tsoho ba, amma kuma ba yaro bane ko kusa. A bayan sa Fadawa ne guda biyu a tsaye sai muzurai suke. Ya fara da bani hakuri, sannan ya gaya min an dauko shi ne daga Airport zasu wuce garin su direbansa yayi duk kokarin da zai yi ya kauce min Allah ya rubuta sai sun kade ni. Ya tambaye ni sunana na gaya masa. Ya ce in bada kwatancen gidan mu aje azo dasu sabida na samu karaya a kafa da hannu bazai yiwu a sallame ni a yau ba. "Bani da uwa bani da uba, bani da 'yan uwa, nikadai ce. Ban da kowa, kuma bani da inda zani". Na bashi amsa cikin kuka na zafin ciwo. Maimartaba Sarki Yusufu mai Askira, ya dade yana kallo na kafin ya ce "Kin yarda ki bini masarautar Askira cikin amana in zame miki uwa da uba sannan MIJI abokin rayuwa?" Haka naji furucin sa tamkar cikin mafarki, na kasa yarda da abinda kunnuwa na suka jiye min, na kasa amincewa ido na biyu it was just in a dream..... (and that was how I became a QUEEN) wannan ne silar zamowata Sarauniyar amaryar sarkin Askira, wanda daga kallo na farko na ji ya kwantamin a rai, da wani irin exceptional feelings..., wata irin kwantacciyar soyayya da kauna, da ban taba ji a rayuwa ta ba. Komai ka ga ya faru da bawa to dama can rubutacce ne a lauhul-mahfuz, na yarda rabon Sa'adatu ne ya sabbaba aure na da mahaifin ta, ban taba jin son sa ba, domin soyayya ta Allah ce. Shi yake kimsa ta a zuciyar bayin sa. Haka itama kiyayya. Amma a ganina da ba ta hanyar da Hashimu ya bi ya aure ni ba kenan zan iya hakurin cigaba da zama da shi ko don maraici na dacrashin gata na. Bayan na gama iddah a gidan Liman inda aka yi min masauki, Limamin Askira shi ya zama waliyyi na, Wazirin gari Ibrahim ya zama waliyyin Sarki Yusufu suka daura mana aure, auren da ya jawo cece-kuce mai yawa a masarautar Askira domin Sarki Yusufu bai taba auren diyar talaka ba balle mara asali mara dangi. Duka matansa 'ya'yan sarakuna ne daga masarautu daban-daban na jihar Borno. Gorin kishiyoyi da damuwar rashin dangi dana shiga shi yasa maimartaba maida hankali ya binciko min dangin mahaifana, wadanda suka zo kasar Nigeria tare, ta hanyar su ne aka bi aka cimma sauran a Chadi duk da cewa da yawa sun watsu cikin duniya wasu kuma sun murmutu. Kusan mutum biyar aka samu masu alaqar jini da iyaye na a kasar Chadi. Sannan ne na samu kaina daga gorin rashin asali dana dangi daga wajen kishiyoyi na. Aka maida gorin kan ('yar talakawa). Rayuwar gidan sarauta rayuwa ce mai wahala, musamman ga ni da ban ta so cikin sarauta ba, na sha wahala ba 'yar kadan ba a hannun Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma bata da matsala sosai, ita kuwa Hibbani sai munafurci da tsugudidi da daukar zance. Sa'a ta guda daya ce; matsanancin son da miji na ke yi mun, wanda yayi maganin kowacce damuwa da kowanne kalubale dake cikin babban gidan sarautar Askira. Sarki Yusufu bai kyale ni haka ba cikakken ilmin addini dana boko ba, malama ya dauka mai digiri take zuwa har gida tana koyar dani karatu da rubutu na zamani, sannan ya daukar min malamar karatun addini, don haka daidai gwargwado inada sani a duka fannonin har fiye da kishiyoyi na wadanda girman kai ya hana su zama daukar karatu wurin kowa. A cewar su wanda suka yo a gidan iyayen su ya ishe su. A haka nayi haihuwa har biyar 'ya'yan basa sati a duniya suke komawa. A cewar maimartaba alhakin SA'ADEN dana baro a lokacin da tafi bukatata ne, ko hakan ne ko ba hakan bane a halin yanzu na yarda na amince akwai hakkin Sa'ade a kaina, wanda ya zama dole in nemi yafiyar ta, ban taba ganin yarinya mai hakuri da son mahaifiya irin Sa'adatu ba. Mahaifiyar da ko sau daya bata taba kyautata mata ba!!! Amma kullum ta zo gaba na sai annurin fuskarta ya canza. Walwalar ta ta karu. Sai ta nuna kaunar da ta ke mun cikin fararen kwayan idanun ta. Meye laifin ta akan tsakanina da mahaifin ta? Bata san komai ba, bata san an yi ba. Don haka cikin mu'amalar mu ta Uwa da Da na amince akwai daukar hakki......
Chapter 5 · 0% Book details