Sashe 6
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A hankali Fulani Bilkisu ta sake lumshe idanun ta. Ta bi kofar dakin Sa'ade da kallo, inda take jiyo karadin su ita da Zarah.
Ko in ta baiwa Sa'adatu labarin nan zata yi mata uzuri ta yafe mata?? Domin hakika ta cuzguna mata ba dan kadan ba.
Wannan tunanin ne ya sa ta mikewa tsaye, ta doshi dakin Sa'ade cikin sanyin jiki da mutuwar zuciya......
****
"Bude bakin.....haa...in sa miki choculate" ta ji Sa'ade na fadi a lokacin ta tura kofar dakin, ta same su bisa gado itada Zarah, har sun sake wanka sun sake kayan jikin su kasancewar akwai wasu kayan Zarah a dakin Sa'ade sabida yawan yi mata wanka data ke yi idan tazo hutu. Murmushi Fulani tayi ta karasa gare su ta zauna a gefen gadon. Sa'ade ta saki baki tana kallon ta don abu ne da bata taba gani ba; Fulani a zaune gefen gadonta tana mata murmushi irin na UWA....murmushin Fulani, da zama akan gadon ta ya dugunzuma zuciyar Sa'ade. Kullum ta shigo tana tsayawa ne daga bakin kofa ta fadi sakon da ya kawo ta ta juya. Yau kuwa kyakkyawar fuskarta a sake, dauke da murmushi mai taushi. Ta lura da kallon tsoron da Sa'ade ke mata sai ta kara kashe ta da lallausar murmushi.
"Ki daina dura mata chocolate baki ga hakobranta duk sun cinye da zuma ba?" "Tana so ne Fulani, kuma da ta fara fanfara duk ficewa zasuyi masu kyau su fito". Ta sake yin murmushi, "an gama makaranta sai aure ko? Ko baki da saurayi ne?" Nan da nan Sa'ade tayi kicin-kicin da fuska kamar Fulani ta aiko mata da sakon mutuwa. Kamar zata yi kuka tace a shagwabe "to ni ina nake zuwa balle inyi saurayin? Daga makaranta sai daki na, ko tsakar gidannnan ba bari na kike in je ba, sabida bakya so a gane ni 'yar ki ce. Kuma Alanguburo yayi min alkawarin tafiya Jami'a a Abuja idan na ci SSCE dina, ke kuma kina zancen aure".
Fulani ta dora hannayenta biyu akan kafadun Sa'ade duka biyun tana murmushi tace "karatu ai ba ya hana aure Sa'adatu. Sanda ina kamar ki haihuwata uku don dai basu rayu bane, kuma shi Alanguburo ai ra'ayin ki yake bi amma ni da shi duka mun fi so mu yi muki aure....." da sauri ta tare Fulani "to sai ku bari sai Allah ya kawo mijin, ni 'yar mitsitsiyata dani....." ta fada tana zumburo baki. Fulani tayi dariya ta dalle mata siririyar fatar bakin nata "zaki je makaranta kamar yadda kike so, amma bazamu bari ki zauna a hostel ba, saidai gidan Yarima, tunda shi malami ne a makarantar zai taimaka miki, sannan gidan sa cikin jami'ar yake, zaki samu saukin zirga-zirga".
Fuskar Sa'ade ta nuna ba haka ta so ba, campus life take sha'awa, ta ganta a jami'a tana rayuwa a cikin dalibai 'yan uwan ta, rayuwa ta 'yanci ba irin ta EL-KANEMI ba. Sa'ade ta ga cewa zuwa jami'ar ma da aka barta dama ce, domin babu wadda ta samu irin wannan alfarmar a 'ya'yan gidan, da sun gama sakandire Askirama ke aurar dasu, itama ya duba maraicin ta ne da kuma tunanin karatun shine gatan da zai yi mata a rayuwa ranar da baya doron kasa.
Ta tambayi Fulani ko wanene Yarima? Da ta ce a gidan sa zata zauna a Abuja? Fulani tayi mata bayani yadda zata gane cewa babban dan maimartaba ne a maza, shine Yarima mai jiran gado, Chiroman Askira, wanda ya dawo daga kasar Amsterdam shekarun baya yayi aure.
Sa'ade ta kwantar da ido tana kallon Fulani, ganin yau akwai rahma tattare da ita, watakila in tayi sa'a ta gaya mata abinda ta dade tana son ji daga gareta....an ce Dama tana zuwar wa dan adam sau dayane a rayuwa....watakila daga yau din bazata sake ganin murmushin mahaifiyar ta ba, bazata sake ganin ta cikin wannan maternal mood din ba...don haka ta tambayeta abinda ta dade yana cin ta a zucci....
"Don Allah Fulani me yasa ba kya so na? Me babana yayi miki kika tsane shi? Meyasa kike bakin cikin kasancewata diyar ki? Fulani ko don ni babana talaka ne shine dalilin da......." ta kasa karasawa sai kuka ya kufce mata, tana tuno bad memories na tun zuwanta hannun mahaifiyar ta.....
Ga dukkan madaukakin mamakin ta, sai jin hannun Fulani tayi ya zagayeta cikin runguma kyakkyawa, ".....Ban taba kin sa don yana talaka ba, hasalima ni a mai arzikin sa na san shi. Ban taba neman komai a hannun sa na rasa ba, ya ciyar da ni ya tufatar da ni a tsayin zamana da shi. Laifin sa gare ni daya ne....hanyar da ya bi ya aure ni.....". Tiryan-tiryan ta soma bata labarin ta, labarin da ya dauki hankalin Sa'ade har bata san lokacin da tace.
"Lallai Baba bai kyauta ba. Amma ki dubi Allah Fulani ki yafe masa albarkacin ni da nake tsakanin ku, da kuma kasancewar a halin yanzu ba ya duniyar".
Ta fada tana share hawaye. Fulani ta kara jawota jikin ta, ta sanya fuskarta cikin tafukanta "daga yau kin daina zargi na akan babanki? Kin daina ganin beke na a kan sa?" A hanakali Sa'ade ta gyada kai. Ta ce "to na yafe masa duniya da lahira, kema ki yafe mini deprivation dina a gareki da yadda na tafiyar da ke a zaman mu tare. Nayi kokari in tanqwara zuciyata na kasa....amma alhamdulillahi yanzu na samu sauki daga duk wani duhu da kullaci dake cikin raina".