← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Koda ta koma dakin ta a washegari bata ce da Sa'adatu komai ba, cikin dimuwa da zullumi take, sabida Mai Askira ya ce kafin su koma hutun nan da suka zo sai da igiyar aure a tsakanin su.
Sa'ade ta lura a wunin ranar bakidaya Fulani ta zama sukuku! Bata umh bata umh umh. Abinci wannan a wunin yau bata ci shi ba kuma tace ba azumi take ba. Ta lura tunda ta dawo daga turakar maigidanta take cikin wannan halin, to ko ita da Mai Askira ne suka samu sabani? Saidai hakan mawuyaci ne don bata taba ganin ma'aurata masu fahimtar juna kamar su ba.
Sai itama ta shiga damuwa, damuwar uwarka ai yana nufin taka damuwar. Damuwar Fulani shine bata san ta ina zata farawa Sa'ade zancen aure ba, she's too young and innocent, auren ma kuma da Yarima Sageer, wanda ta riga ta gama sanin sirrin su shi da matar sa, ta kuma dauke shi matsayin guardian dinta. Sama da komai bata taba tunanin yiwa Sa'ade aure nan kusa ba, ta so sai ta gama karatun ta, to kana naka Allah na nasa kuma nasan shine gaskiya.
Sa'ade sai zarya take tsakanin dakin ta dana Fulani very disturbed, ko Fulani zata kira ta tace zo kiji damuwata, amma Fulani ko kallon ta ta kasa yi, ji take kamar ta yi ba daidai ba ta kuma yi mata laifi data karba mata zancen aure bada sanin ta ba. Ba jimawa jikin ta ya dau dumi, data tuno me ake yi a gidan Yarima Sageer "Zina da Shan giya". Ba ga matar ba ba ga mijin ba kowanne shegen kansa ne, ta dauki innocent 'yar ta ta kai musu, matar ta sha giya ta rotsa mata kai, ko mijin yayo zinarsa ya goga mata cuta?
Amma kuma wanene Yarima? Dan Askirama mafi soyuwa a gare shi. Askiraman da ya maida Sa'aden mutum a lokacin da ita ta kasa karbar ta. Wannan damuwa a take ta kwantar da Fulani Bilkisu, amma sai ta mike tana rangaji ta sawa kofar ta mukulli kada Sa'ade ko Fanna su zo su dameta.
****
Ya Gumsu na tareda mai Askira a washegari, itace tayi turaka kuma itace zata wuni tare da shi a wunin yau da baya fita fada, duk ranar Jumaah daga ya dawo masallaci sallahr jumaah baya kara fita, yana zama ne ya ribaci yammacin da ibada musamman karatun Suratul-Kahfi da suratul Mulk, Yaasin da Waqi'ah. Sannan yana karanta Suratul Nouh kafa 41 a kowanne yammacin Juma'ah.
Tana hada masa shayi a cikin kofi (mug) ya dubeta da murmushi. Ya ce "Gumsun Askira, Uwargidan mai Askira....inada wani kyakkyawan albishir dauke a bakin nan nawa". Ya Gumsu ta karkace ta gyara zama bisa tattausar dardumar da maimartaba ke zaune har da tattara dukkan nutsuwar ta ta bashi, a zaton ta albishir zai mata da tafiyar su wata kasar su huta.
Amma abinda mai Askira ya fada bata taba jin abinda ya girgiza zuciyarta da rayuwarta bakidaya irin sa ba. Ya jirkita kwanyarta, ya gusar da annurin fuskarta nan take ya mayeshi da wani mummunan bacin rai da Askirama ko wani mahaluki bai taba gani a kan fuskarta ba.
"Kwanaki uku masu zuwa zan daura auren Yarima da Sa'adatu!"
Amma Ya Gumsu sai ran ta ya bata gara ta tambayeshi don ya tantance mata wace Sa'adatun yake nufi? Don haka ta hadiye komai cikin laluma ta tambayeshi.
"Allah ya taimaki Giwan Askira, ko zan iya sanin wacece Sa'adatun?"
"'Yar ku Sa'adatu wadda yake riko a gidan sa ta wajen Fulani Bilkisu......".
Ai bai karasa ba sai ganin Ya Gumsu yayi tsaye a kansa, idanun ta a warwaje tana huci, yau da ba shi ne sarkin Askira ba, da ba shine uban 'ya'yan ta ba, furfurarsa ko wannan himilin rawanin nasa bai hanawa ta kwashe shi da mari.
"Idan wasa kuke..... Allah ya taimake ku ku bari, bana son irin wannan wasan....." cikin mamaki Askirama ke kallon ta baki a bude, ya dauka wannan karon farin ciki zata yi da zabin da yayiwa Yarima, shi da take fushin ya auri mai jajayen kunnuwa mara addini, ga wadda suka san asalin ta suka san addinin ta suka bata tarbiyya cikin gidan amma tana neman kawo masa zancen banza.
"Ni ne nake miki wasan? Zaki ga wasa kuwa ganin idon ki".
Mikewa yayi zai bar wajen Ya Gumsu ta sha gabansa idanunta tamkar an gumbuda musu barkono "Allah ya taimake ka ashe kuwa zaka bani takardar saki na.......kafin ranar da zaka aurawa Da na aure da tsintacciyar magen da har yau bamu san asalin ta ba, da 'yar data fito daga hannun makiyiyata don su hada kai su cuce ni su ga baya na nida zuri'ata a gidannan.....na tabbata ita ta kitsa maka wannan sharrin to insha Allahu a kanta zai kare!
Ba dai Yarima ba! Ba irin tsiya irin talauci ba, irin da babu cikakken asali don ni ban yarda ma BAGGARA ne su ba sun fi kama da bororon daji......".
Mai Askira ya hadiye tsananin bacin ransa bai nuna ba ko a fuska, babu wata mace data taba yi masa irin wannan tsaurin idon a rayuwar sa....amma Gumsun Askira zata ci albarka da yawa....albarkar 'ya'yan ta...albarkar kasancewar ta uwar 'ya'yan sa. Da albarkacin kasancewarta UWA ga duk wani mahaluki dake cikin Askira.
Kawai sai ya zagayeta zai wuce, bai taba sa'in sa da kowa ba, tsakanin sa da kowa dake karkashin sa biyayya ne ana so ko ba'a so. Shiyasa ba karamin yaki yayi da zuciyar sa yau akan Ya Gumsu ba, sabida babu saki a tarihin sarautar su, babu kaskanci ga uwar iyali.
Ya Gumsu bata daddara ba ta sake jawo Alkyabbar sa..."wallahi sai ka bani amsar inda kuka samo yarinyar nan....ba tun yanzu ba nasan watarana sai ta zame min jidali, na san sai an kakabawa 'ya'yana, yadda naga uwarta ta ci buri a kanta, dama dalilin kawota gidan kenan don ta samu ta auri dan sarki.....kamar yadda ta samu tsuntsu daga sama gasashshe....to ai ba ni kadai na haifi maza ba......don haka in har inada hakki akan Yarima na haihuwa da shayarwa to ban yarda ba ban amince ba.....".
Mai Askira yayi murmushi yace "sai kace dan wani na arziki ne da kike tada haqarqari akan sa ke mai da! Dan da tun yana karamin sa ya san dadin zina......girma da aure da martabar gidan su bata sa ya daina ya kama kansa ba. Zan rufa masa asiri da 'yar mutunci don ta taimaka mana ya kintsu shine kike wannan zubar da kimar? Gumsu ina jiye miki ranar jin kunyar ki.....ranar da duniya zata san dan da kike tinkahon dashi har yanzu bai bar zina ba, matar sa shan giya take, rayuwa suke kamar ta dabbobi, musuluncin nasu duka ba maraba.....gara ita nata babu tushe amma wanda bai ji tsoron Ubangiji ba kuma girman aure bai hana shi yin zina ba ba abun tutiya da shi a matsayin Da bane....
Chapter 17 · 0% Book details