Sashe 11
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
labe nake musu ba, da karfi suke magana, ni ina daki na ma" Fulani tace "na fahimta, amma ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kiyi pretending as if baki ji komai ba, fadan mata da miji sai Allah, kwana biyu zaki ga sun shirya. Tunda dai ba takura miki suke ba to ba ruwan ki dasu" da haka Fulani ta samu ta lallasheta ta daina kukan, tace tayi alwallah tayi sallah tayi azkar tayi shirin tafiya makaranta. Yadda Fulani tace ta yi haka ta yi, da misalin karfe 8:30 ta fito rataye da jakarta, tayi shirinta tsaf. Hannun ta rungume da manyan littafan ta na chemistry. Da Yarima ta fara tozali yana sipping shayi akan dining, gabadaya ya birkice kamar bashi ba smart guy mai tafiya da imanin mai kallon sa, gashin kansa ya cukurkude kuma ga dukkan alamu ko wanka bai yi ba. Ta gefen idon ta ta saci kallon sa, a ranta tana fadin how comes this perfect and handsome gentleman is adulterer? Ga goshin sa har da tabon sujjadah. Watakila matar sa ta dai fada ne don ta bata masa rai tunda shima ya ce tana shan giya. Ta dan russuna daga bakin kofar dakin ta ta ce ciki-ciki "barka da asubah". Ya dago lumsassun idanun shi ya dube ta wadanda suka canza kala zuwa brownish sabida rashin barci. Ta ki yarda su hada ido ta sunkuyar da kanta wanda hakan ya bashi damar ganin yadda idanun ta suka tasa, kada dai kuka tayi? Kada dai ta ji fadan su shi da Sultana? Tabbas da ya shiga uku ya lalace. Murya a cunkushe ya ce "come take your tea" cikin rawar murya ta ce "i'm ok" tasa kai zata wuce ya daka mata tsawar data firgitata "kina nufin haka za ki fita baki ci komai ba? Me ya samu idanun ki haka? Have you slept yesterday night?" Jikin Sa'ade ya soma rawa sabida bai taba yi mata magana cikin tsawa ba. Ta tuna Fulani ta gargadeta akan ta nuna bata ji komai ba. Sai tayi narai-narai da ido gab take da sakin kuka ta ce "na tashi da ciwon ciki ne" Yarima ya ji wani irin relief ya sauko masa, ya nuna mata kujerar dake gefen sa "zauna ki sha tea ko kadan ne, bai kamata ki fita haka ba, sai in baki magani" ta bi umarnin sa kan ba yadda zata yi, amma kwarai take so ta bar gidan ko ta samu sa'ida. Da kansa ya hada mata tea din, wanda shi ya dafa shi da kansa. Uche ya masa waya cewa ya tafi garin su Ogun mahaifiyar shi ta rasu a safiyar yau. Ta karbi tea din da yake mika mata ba don ranta ya so ba, amma kaifin idanun sa da ya tsare ta dasu ya sa ta kasa kurbar shayin. Yarima ya mike ya bar dining din zuwa dakin sa don ya bata dama ta sha shayin, ya lura yau wani tsoro-tsoron shi take ji, jiya kuwa har labarin karatunsu ta bashi. Yana tashi tayi maza ta kurbe shayin, saura kadan ta kware, ya fito a daidai lokacin da ta mike tana daukar handbag dinta, hannunsa rike da kwalbar gestid. Ya jijjiga ya zuba a murfin ya mika mata. Hannu na rawa ta karba daidai lokacin da Sultana ta fito daga daki cikin nata shirin na tafiya ofis. Wani kallon banza tayi musu sannan ta dauke kai ta wuce su fuuuu! Sa'ade na fadin "good morning aunty" ko kula ta bata yi ba. Salis ya soma horn don ta gane ya iso yana jiranta. Kallon Yarima tayi ta kasa-kasan ido tana jiran ya bata umarnin tafiya sai ta samu idanun sa a kanta suke. Da sauri ta kara sadda kanta. Ya ce "in kin dawo kin yi abinci ki sa da ni, Uche ya tafi garin su Maman sa ta rasu" kai kawai ta gyada tana mamaki a cikin ranta. Ita wacece da zata yi abincin da Uncle Yarima zai iya ci? Har suka isa makaranta tana kakabin abin cikin ranta, in matarsa ta ce ta yi mata shishshigi fa? In Uche baya nan meye amfanin matar sa? Koda yake wannan mai jan kunnen bata taba ganin ta tana dafa ko da ruwan zafi ba. Gara dai ta fara tambayar Fulani, kada ta yi abinda ba dai-dai ba. Data gama lectures din yau zata fito ne ta tadda Salis a parking lot ta kira Fulani tana cigaba da tafiya a gefen hanya, bayan sun gaisa tace "Fulani wai uncle Yarima ne yace yau in zan yi abinci na in sa da shi, sabida Uche yayi tafiya, ina tsoron kada in yi abinda ba shikenan ba" Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce "meye gamin ki da Yariman da har kuke hira?" "Ba hira muke ba, dazu ne da safe da zan fito ya gaya mini" Fulani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Sa'adatu! Ki kula da kan ki kin ji? Ba zan hana ki bashi abinci ba tunda Yayanki ne, amma bana son wata mu'amala mai zurfi a tsakanin ku bayan kasancewar shi guardian din ki. Maza duka ba abin yarda bane you have to be careful!" "To Fulani in ce bazan bayar ba mana? Wani abu ne?" "A'ah kar ki ce hakan, just cook and keep it on dining ki shige dakin ki, ban yarda da hira mai tsayi tsakanin ku ba" da haka suka yi sallama. Tana shiga gida ta ajiye littafanta tasa apron ta shiga kicin. Girki na nutsuwa ta yi, wanda ta inganta da kayan kamshi na gargajiya, lallausan tuwon semovita miyar danyar kubewa data ji ganda da busashshen kifi. Sannan ta markada abarba ta hada da zobo da pinapple flavour. Sai tayi farfesun kayan ciki mai rai da motsi. Sugar kadan ta sanya. Tana gamawa ta shirya masa a dining ta shige dakin ta ta kulle ta hau yin assignment din da aka bata yau daga laptop dinta. Yarima ya riga Sultana dawowa domin data tashi aiki Bar ta wuce ko don ta sauke bacin ran data kwana ta kuma wuni da shi, domin hakika tana shakkar sake shan giyar a gaban sa don yadda ta ga ya rikide mata jiya ta san komai zai iya faruwa da auren ta, one thing shine tana son Yarima bazata iya rabuwa da shi ba. Yana shigowa falon, falmaran din black Italian suit din jikin sa ya fara cirewa, yayi loosen tie din wuyan sa, kai tsaye dining ya nufa, a yunwace yake sosai, rabonsa da abinci tun tea din safe. Yana budewa ya ja kujera ya zauna ya soma ci cikin nutsuwa irin tasa, kunnen sa har wani irin motsi yake yi. "She's blessed in cooking!" Ya fada a hankali. Yana so ya kira ta, bai san in ta zo mai zai ce mata ba, he just want to check she is well, don haka yasa murya a tausashe ya kira ta. "Sa'adah!" Ta ji kiran nasa amma sai ta kasa yarda kiran nata yake yi, it sound so weird, don bai taba kiranta da wannan sunan ba, sannan amon muryar ya taimaka wajen sawa taji kiran kamar ba nata bane, don haka ta cigaba da aikin ta, hankalin ta ya rabu biyu, ya kan kirata Sa'adatu ne in full. Da ya ji shiru kai tsaye ya mike zuwa dakin nata, bayan ya wanke hannun sa a sink din dake manne a gefen dining din, ya tsane da karamin tawul. Kanta a sunkuye tana sarrafa na'ura mai kwakwalwar ta, riga da wando ne na pakistan a jikin ta ruwan goro turarre, ta yane mayafin su a kanta. Bata ji karar bude kofar sa ba sabida yadda hankalin ta yayi nisa kan abinda take yi. Sai sassanyan kamshin INVICTUS (By Paco Rabbanne) ya ziyarci hancin ta, ya kuma sauya atmosphere na dakin bakidaya wanda ke cakude da rabar iya kwandishan. Har gabanta Yarima ya zo ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu, a hankali Sa'ade ta dago ido sai idon ta cikin na Yarima.....wani abu mai karfi tamkar magnet ya manne idanun su wuri guda. Yarima Sageer ya tuna wannan kanwar sa ce a gaban sa (step-sister) kuma amanar mahaifin sa.... amma akwai wasu abubuwa cikin idanun yarinyar da ke da matukar tasiri akan sa, wadanda yake kasa controlling din su, wadanda bai san yadda zai fassara su ba. Watakila kyawun idanun ta ne ko hasken da ke cikin su? Juyawa ya yi ya bata baya don kaucewa kaifin idanun ta. Murya cunkushe ya ce "I just want to check on you. Have you eaten?" Kai ta gyada duk da ba kallon ta yake ba "zan ci in na gama" ta fada da sassanyan sauti. Taku daya, biyu yayi kamar zai fita, sai kuma ya juyo gabadayan sa. "Sa'adatu will you help me with your food har Uche ya dawo?" Ba tare da ta dago ba tana cigaba da typing din ta ta motsa dan bakin ta a hankali "sai na tambayi Fulani" yadda tayi maganar innocently ya burgeshi, ta nuna bata da wani ra'ayi kai tsaye sai na uwar ta. "Fulani bazata hana ki sammin abinci ba, nima uwata ce har fiye da ke" murmushi tayi wanda ya kara fiddo kyawun karan hancin ta. "Har fiye da ni? Ai daga ni sai Zarah ta haifa. Ka ga kuwa bata da kamar mu" ya dubeta straight cikin idon ta duk da ba shi take kallo ba "ni ta fara haifa kafin ta haife ku" murmushin ta ya zarce zuwa dariya "ai watakila ma ka girmeta Uncle Yarima" "sabida kin ganni da furfura?" "Ni ban gani ba, amma ko baka girme ta ba zakuyi age mates" ya juya ya fita yana murmushi cikin fadin "i look forward to my dinner Sa'adah. Na bar ki lafiya". Bin sa ta yi da kallo har ya fice, amma dakin ta bai bar INVICTUS perfume ba. Abinda ta ji jiya ya fado mata a rai. A fili ta ce "ba kama....". Sannan tayi ajiyar zuciya ta cigaba da aikin ta. Wannan baturiyar ta yi sa'ar zankadeden miji wanke hannu ka taba, amma don asara ko abinci bata bashi... tadin Sa'ade kenan ita da zuciyar ta. Ta kira Fulani ta gaya mata yadda sukai da Yarima, Fulani ta shiga dan rudani, ta ce "Sa'adatu