Sashe 22
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
******
Suna kwance a bayan mota 4-matic mai dauke da rubutun ASKIRA EMIRATE, direba na ta sharara gudu don su isa Askira cikin lokaci, ta garin Damaturu suka bi, duk da ta fi nisa amma ta fi lafiya sabida insurgency da ya fara kafuwa a daidai lokacin a jihar Borno. Zuwa Askira ta Chibok bai yiwuwa dole sai an bi ta Damaturu.
Duk hirarrakin da Awaisu yake masa don ya dauke masa tunani ya ki kulawa, jikinsa ke ba shi kawai, theres something fishy going on akan Saadatu da har ya sa Maimartaba ya yi masa kiran gaggawa.
Ana kiran sallar magriba suka shiga Askira. Inda Awaisu ya ji dadi shi ne kafatanin fadawa da dogarai da duk wanda ke wajen ya shiga masallaci sallah lokacin da suka iso, ba don haka ba da tun fitowarsu mota za a fara tarar Yarima da Allah ya sanya alkhairi. Yan tsirarun da suka hadu da su a hanya mata ne bayi suke wucewa. Gaishe su kawai suka yi suka wuce.
Suna shiga sassan Yarima da ke cikin gidan alwallah suka yi suka tada sallah, kafin su idar hadiman Yarima sun gama jera musu abinci. Awaisu ne kawai ya zauna yana ci, Yarima sai magiya yake masa ya ba shi wayoyinsa yana cewa, sai ya fito daga ganawa da Maimartaba.
Kawai sai jin sallamar Ya Gumsu suka yi a kansu, karkashin rakiyar kuyanginta. Daga bakin kofa suka tsaya ita kadai ta shigo sai huci ta ke kamar mesa. Yarima da Awaisu suka mike tsaye a tare har suna hada baki a tare wajen cewa, Ya Gumsu lafiya??
Kawai sai ta zauna a kujera ta sa fuska cikin tafuka ta fashe da kuka.
Yarima da Awaisu suka tsugunna a gabanta suka kasa magana, suna nan durkushe gaban Ya Gumsu tana kuka suka jiyo takun tafiyar Askirama. Daga kirarin da ake masa daga waje suka gane shi ne yake tahowa.
Ya karaso har dakin Yarima bakinsa dauke da sallama. Idonsa ya sauka a kan Ya Gumsu, ransa ya yi mummunan baci, da kyar in ba ta lalata komai ba.
Biyo ni Yarima.
Abin da ya ce kawai kenan ya juya ya fita. Yarima ya kasa tashi daga gurin ya bar Ya Gumsu da ke kuka har sai da ta dago idanunta jage-jage da hawaye, ta ce,
In ka karbi auren nan da ya yi maka sai na dauke maka albarka.
A razane Yarima ya cira kai ya dubi mahaifiyarsa, kafin ya samu zarafin ce mata komai ta tashi ta fice kamar kububuwa.
Yarima ya shiga cikin halin rudu mara misaltuwa. Kawai sai ya bi bayan maimartaba ya bar Awaisu a wajen.
Awaisu ya jinjina kai cike da taraddadin wannan alamari, bai yi zaton ya Gumsu ba za ta so auren nan ba in ya yi laakari da yadda ta ke adawa da auren Yarima na farko. Da ya tuna kishin da ke tsakanin matan gidan sai mamakinsa ya ragu, don Saadatu ta fito daga dakin Bilkisu ne wadda suke kishi da ita fiye da kowacce matar sarki.
Yarima bai zauna ba sai da Askirama ya fara zama a kujerar mulkinsa. Ransa a tsananin bace don a zatonsa Ya Gumsu ta riga ta yi masa riga-malam-masallaci. Ya yi kokarin boye bacin ransa sabida ba ya taba bari a gane fushinsa, ya dubi Yareema Sageer da ya samu wuri ya zauna daga kasan kafafunsa.
Kafin in ce komai Yareema idan na yi maka umarni, uwarka ma ta yi maka, na wa za ka bi a cikinmu?
Yarima ya kara rudewa, gabadaya sun rikita shi, ya kasa gane komai. Kawai sai ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Mai Askira ya yi murmushi ya ce, Aure na yi maka shi ne ta ke adawa, aure na mutunci da rufin asiri, auren da na tabbatar zai dauke dukkan kwadayi da shaawarka daga kan sauran mata kamar yadda ya dauke nawa daga kan Bilkisu ko kwarkwarorina na hakura da su daga ranar da na mallaki Bilkisu, domin matan BAGGARA daban ne. Don haka ne nake da kyakkyawan zaton cewa abin da ta haifa ma zai zamo irinta ga Sarki mai jiran gadon Askira. Na aura maka diyar Bilkisu, wato SAADATU don in raba ka da kusantar zina da matan haramun. Ya rage naka ka bi umarnina ko na mahaifiyarka. Ka tashi na sallame ka, ka je ka yi tunani kan abin da ya fi dacewa da kai. Rana ita yau za a fara biki, biki irin wanda ba a yi a aurenka na fari ba, bikin aladar gargajiya na masarautar Askira. Na kai shi zuwa rana ita yau ne don kawunta da ke kasar Italiya ya samu halarta shi da iyalinsa.
A nan Maimartaba ya gaya wa Yarima labarin asalin Saade, tun daga auren mahaifiyarta da Malam Hashimu zuwa rabuwarsu. Rayuwar Saade a kauye da ranar da abokin Babanta Malam Saleh ya kawo ta Askira ya karbe ta, wahalar da ta sha a hannun fulani kafin ta amshe ta matsayin ya, da nagartattun halayen Saade da ya dade yana fahimta. A karshe ya gaya masa tun farko ya yi niyyar aura masa Saade a matsayin matarsa ta farko sai ya kawo zancen Aisha-Sultana, shi kuma ya ba shi dama don ya fita hakkinsa. Yanzu ne yake so ya yi masa biyayya da auren Saade, duk abin da suke ciki shi da matarsa ya sani, kuma wannan shi ne matakin da zai iya dauka.
Ga mamakin Mai Askira tunda Yareema ya dukar da kai bai dago ba sai da ya kai aya, da ya dago idanunsa sun kada sun yi jazur kamar an gumbuda musu borkono, labarin Saade da ya ji daga bakin mahaifinsa ya gama kashe zuciyarsa, ya luguiguitata. Tun asali kuma ya dade da wani irin feelings a kan Saadatu wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani. Feelings din da shi kansa bai san ma'anar sa ba, bai san a muhallin da ya sanya shi ba. Yau da ya samu wannan labarin na zamowar Saadatu halalinsa, matar auren sa ta sunnah daga bakin da ba zai taba yi masa karya ba, zuciyarsa ta ki tsugunnuwa a waje daya, sai dawurwura ta ke a cikin kirjinsa kamar za ta fito ta bakinsa tsabar contentment din da ya cika zuciyar sa da wani sabon yanayi da ya samu kansa a ciki irin wanda biro ko yawun baki ba zai iya bayyanawa ba.
Lokacin da Yarima ya dago ido don ya baiwa mahaifinsa Askirama amsa, Askirama couldn't believe cewa hawaye ya gani a idon Yarima......
Hawayen da bai san na menene ba, tsakanin.... bakin cikin abin da ya yi masa, tausayin labarin Sa'ade, ko ko na farin - ciki ne kai tsaye? Ba zai iya cewa ba!!!
Mu karasa a littafi na 3.
Na yi muku alkawarin cigaban ba zai jima ba, insha Allahu.
Taku har abada;
Sumayyah Abdulkadir Takori.
27th August, 2021