Sashe 4
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
SHEKARU GOMA SHA TARA A BAYA! Mu 'yan kabilar "Baggara" ne wadanda aka fi sani da "Shuwa-Arabs", asalin mu makiyaya ne masu yawo da dabbobin su a kasashen Africa, mun fito daga kasar Chadi wadda take daga yammacin Ifriqiyyah, yawanci zaki samu yan kabilar Baggara sun watsu a kasashe irin Sudan, Cameroon, Niger, Chad, Nigeria, da kuma Central African Republic. Baggara musulmi ne na haqiqa masu rikon addini tun karni na goma sha uku, harshen mu shine "Chadian Arabic" wanda muke yin shi da shuwa-dialect, Allah ya zubawa Baggara kyawun surah na kirar jiki data fuska, da wata irin kalar fata mai sheki da kyau, wanda ya samo asali daga cakuduwar su da larabawan Sudan. Mahaifina Malam Soumana ya baro kasar Chadi tare da mahaifiyata a lokacin tana da cikina tare da 'yan uwan su Baggara zuwa Nigeria inda suka yada zango a yankin Borno, daga baya suka koma Damaturu bayan an haifeni da shekaru hudu, inda mahaifina yake sana'ar kiwo, shanu yake kiwo da tumaki ya sayar a karshen kowacce shekara ya sayi wasu ya sake sabon kiwo. Mahaifiyata Roumana tunda ta haife ni bata sake haihuwa ba, inada shekaru biyar Allah yayi mata rasuwa. Babana shi ya cigaba da raino na, yasa ni a makarantar firamare, daga baya jarin kiwon nasa duk ya balbalce, wani abokin sa ya yaudare shi ya saye su da zummar washegari zai kawo masa kudin gabadaya, cikin dare ya bar Damaturu da dabbobin gabadaya, wanda hakan yayi silar talaucewar mahaifi na, muka koma rayuwa cikin kaka-ni-kayi, abinda zamu ci kansa ba kullum muke samu ba, mahaifina ya koma yin dako a kasuwa duk don mu samu abinci baya ko zancen aure don tsoron matan borno wadanda ba kabilar sa ba. A haka na rayu hannun mahaifina cikin kwanciyar hankali don talaucin mu bai hana mana kwanciyar hankali ba, duk wata buga-buga da dan adam zai yi don ya samu abinci mahaifi na yayi ta har na gama makarantar firamare, inada shekaru goma sha uku watarana mahaifina ya zo da dabbobi masu yawa, ya dinga yi musu turke yana daure su daya bayan daya, na tambayeshi inda ya samo su sai ya ce ya karbe su ne yayiwa wani kiwon su zai dinga bashi ladan kiwo duk karshen wata. Sabida zai yi tafiya Kano ci-rani bashi da wanda zai dinga kula masa da su. Watarana muka wayi gari dabbobinnan babu ko daya, an biyo dare an sace su. Mahaifina ya shiga tsananin tashin hankali, domin mai dabbobi ya kusa zuwa gida, duk bayan wata uku yake zuwa, sabida tashin hankali mahaifina har kwanciya yayi ciwo don bai san bayanin da zai yiwa mai dabbobi ba. Bansan yaya suka kare ba, illa a wani dare mahaifina yana kuka ya gayamin gobe zai daura min aure, bashi da abinda zai biya mai dabbobi, shikuma ya ce sai ya biya shi, ko ya bashi aure na madadin dabbobin sa. Na rasa a wane yanayi na karbi wannan zance na mahaifina. "Auren biyan bashi" zai yi dani, sai kace ni din ba mutum bace mai darajah. Ban taba yiwa mahaifina musu ba amma wannan karon na ce a'ah, bazan auri mutumin da ban sani ba ban taba gani ba, sannan kuma tafiya zai yi dani can wajen ci-ranin sa ya rabani da mahaifina wanda shi kadai nake da shi a duniya. Amma rashin yardar tawa bata kara komai ba, washegari mahaifina ya daura min aure. Bayan gama daurin auren yana kokarin shiga gida ya fadi, faduwar da ta zamo numfashin sa na karshe. Kwana uku da rasuwar mahaifina makota sun tayani zaman makoki, kowa ya tausaya mun, na zama abun tausayi, hankalina ba ya kara tashi sai na tuna auren da mahaifina ya daura min. Na tsani auren na tsani mai dabbobin tunda bashi da zuciyar musulunci da ba zai iya yafewa mahaifina asarar data same shi ba, zai ce ayi masa biyan bashi dani sabida rashin sanin darajar dan adam. Washegari sai ga mata uku sun zo wai sun zo tafiya da ni, daya tace sunan ta Yagana matar Yayan mijin nawa ce, sai matan abokinsa guda biyu. Ina kuka ina komai haka suka fidda ni daga gidan mu ko wanka babu, a gidan Yayan sa Malam Kyari aka bamu daki wai zuwa sati mai zuwa zamu wuce Kano inda yake ci-ranin sa. Ban ga mijin ba sai da daddare. Ya manyanta sosai, ga shi bakikkirin ga rashin kyawun gani, ni duk ba wannan ne damuwata ba yadda zan zauna daki daya da shi. Ga dakin ciki daya falle daya. Ya cire babbar rigar sa ya rataye ya jawo ledar da ya shigo da ita yana ta far'a yace "Amarya Bilkisu taho ki ci, ki kwantar da hankalin ki ni mai kaunar ki ne, na dade ina son ki, kuma na gayawa Babanki yace shi bazai aurawa kowa ke ba sabida baki da kowa a kasar nan, burin sa shine ku koma Chadi cikin dangin ku. Nayi duk iya kokari na ba abinda ban bashi ba amma ya ki karba. Sabida haka ne na bashi ajiyar dabbobi na kuma biyo dare na kwashe abina don in samu hanyar mallakar ki. Gashi dabara ta tayi min amfani, saidai ban ji dadi ba da ya rasu ban nemi gafarar sa ba. Na so bayan auren mu in gaya masa cewa ni na kwashe dabbobin". Na daga rinannun idanuna ina kallon mutumin nan da wata irin tsana...tsanar da ban taba yiwa wani dan adam a duniya ba, kawai sai na sa kuka mai cin rai. Ya kawo hannu wai zai lallashe ni na kai masa mahangurbar data sa dole ya ja da baya. Ya sake kokarin kamo ni na buga tsalle na bar dakin da gudu. A ranar a dakin Yagana na kwana. A gabadaya kwana bakwai din da aka ce zamu yi a garin Damaturu ban kara yarda na shiga wancan dakin ba, nasiha da lallashin duniya matar Kyari ta yi da shi kanshi Yaya Kyarin, amma bana ce musu komai sai kuka. Tunanin makomar rayuwata nake da ba uwa, ba uba, babu dangi sannan bansan asali na ba, abinda na sani kawai shine daga Western Chad muke. Bayan wannan bansan komai akan iyayena da asalin su ba. Sannan ga auren wannan azzalumin mutumin! Yo azzalumi mana! Wanda ya sanya mahaifina cikin kaka-ni-kayi don biyan bukatar zuciyar sa. Ya raba mu, rabuwa ta har abada. Don na tabbatar bakin cikin irin auren da yayi min ne ya sa ya fadi, faduwar da ta zamo ajalin sa. Kwana bakwai ta cika, Yaya Kyari ya sameni shi da matarsa, ya fara da yimin nasiha da nuna min girman hakkin aure a wurin Ubangiji, sannan ya kuma tabbatar min kanin sa mutumin kirki ne zai kula dani, in kwantar da hankali na in bi shi, duk abinda yayi min wanda bai kwanta min ba yayi alkawarin tsaya mini, yace daga yau shi uba ne a gare ni ba suruki ba, in na yarda da hakan to in bi Hashimu mu tafi garin Kano. Haka ina kuka ina komai muka shiga motar da zata kai mu Kano, ko fuskarsa ban yarda na kalla ba, don yadda na tsani Hashimu da za'a bani wuka ace kisa halal ne da na caka masa na huta. Duk wata kulawa da tarairaya yayi min a mota, komai ya gani sai ya saya mani duk da bana yarda in karba balle in ci. A haka muka iso Kano, daganan muka hau motar unguwar da yake zaune. Gidan karami ne sosai, sana'ar kayan gwari yake yi (kayan miya) a kasuwar 'yan Kaba, idan ya fita tun goma na safe sai magariba yake dawowa, kafin ya dawo kuwa na gama duka abinda zanyi na dau abinci na na shige daki na sanya sakata. Bana kara budewa sai washegari inna tabbata ya fita kasuwa. Mun dauki watanni a haka, a wani dare da bazan iya tantancewa ba, cikin barci na ji kamar ana kokarin balla kofar daki na, kafin a yi haka na ganshi a kaina. Na soma kurma ihu ya toshe min baki ya sa igiya ba tausayi ba imani ya daure ni jikin karfen gado. A wannan bakin daren ne na samu cikin SA'ADATU. Kuma daga ranar bai kara kusantata ba, domin ya tausaya min azabar da ya gana mini. Washegari ba irin kyautatawar da Hashimu bai yi min ba, amma ba abinda hakan ya kara min banda tsanar sa. Ban taba sanin alamun shigar ciki ba, sabida ban tashi tare da mace ba, koda naga cikin ma yana turowa ban taba kawowa a raina cikin bane, don bansan me ake a samu cikin ba. Balle in yi tunanin na samu. A haka ciki na yayi ta girma, sai da na soma jin motsi da wutsilniya na tabbatar cikin Hashimu ne a jiki na. To dama haka ake samun cikin kamar kiftawar ido? Kamar azal? Fadin tashin hankalin da na samu kaina abu ne da bazai fadu ba, nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. A karshe dole na dangana, ina ji ina gani na haifewa Hashimu 'ya. Tunda na samu kaina na ce saidai ya sake ni ko in kai karar sa. Shikuma a lokacin ba abinda yake so a duniya irin rayuwar jaririyar sa, na fice mai a ka, sabida duk iya kyautatawar da namiji zai yiwa mace a duniya domin ta so shi yayimin, amma na kasa kallon shi da kauna komai kankantar ta. Ba don komai ba sai don abinda yayi wa mahaifi na, da hanyar da ya bi ya samu aure na. Sai yace "mu yi jinga, na yarda zan sake ki, amma bayan kin shayar min da yarinyar nan na tsayin shekara daya kacal, ni kuma zan sawwaka miki kije duk inda kike son zuwa". Da wannan yarjejeniyar na yarda na shayar da Sa'adatu na tsayin shekara daya. A ranar da ta cika shekara daya ya cika alkawarin sa ya sake ni saki daya. Yace ga gida nan ya mallaka mini albarkacin haihuwar Sa'adatu, ya san bani da kowa, ya san bani da inda zani, amma tunda haka na zabawa kaina shi ya bar min gidan, ya dauki 'yar sa yace kauye zai koma ya raine ta. Wannan ba damuwa ta bace tunda na samu 'yancin kaina. Ba wadda zata san