← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 22

Sashe 19

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan daurin aure aka zarce da bushe-bushen algaita da kalankuwa, masu goge da masu ganguna kowa na baje kolin nasa. Gabadaya garin ya rude da hayaniya anata labarin Yarima ne aka daurawa aure da 'yar da kishiyar mahaifiyar sa ke riko, wasu na fadin 'yar ta ce data yi shegen ta kafin tayi aure (wa'iyazu billah) Allah ka kare harshenmu daga fadin gaibu, da abinda bamu da tabbas a kan shi. Wannan zance ya kai kunnen Ya Gumsu ta hanyar 'yan kanzagin ta da 'yan hana ruwa gudu, cewa ashe Sa'aden 'yar Bilkisu ce data yi shegenta kafin tayi aure aka kuma biyota da ita har gidan auren ta. Saura kadan Ya Gumsu ta haukace, ga Askirama yana fada bazai shigo ba sai bayan isha balle taje ta huce akansa. Me ya dace ta yi? Ban da ta je su yi wacce zasu yi itada Fulani Bilkisu? Shegiya a cikin iyalinta! Ai gara mata mara addinin! Yau babu ko mayafi haka ta ratsa ta tafi unguwar Fulani Bilkisu, ta wuce bayin ta da hadimai fuuuuuu! Ko gaisuwar da suke mata bata karba ba.... yau ko ita ko Bilkisu, koda hakan shine zaiyi sanadin igiyar aurenta. Fanna na kokarin fitowa da tsintsiya a hannun ta Ya Gumsu tayi ciki da ita, saura kadan ta fadi, sai wara ido take tana neman Fulani amma bata ganta ba, ta daga murya kamar zata tsaga gidan tace. "Bilkisu! Fito wajen ki na zo!" Wannan kira har cikin kwanyar Fulani Bilkisu, gabanta ya fadi ta dafe kirjin ta, Ya Gumsu ta soma dukan kofar dakin ta tun karfin ta, tana cewa "Da na ya fi karfin auren SHEGIYA kurwar mu kurr. Yadda kika lashe mai Askira shine kika kawo shegiya ta lashe Yarima? Wallahi sai bayan raina wannan auren zai tabbata...." dukan kofar take kamar zata ballata. Bilkisu jikin ta sai rawa yake hawaye na zubo mata, tana so ta fito ta fuskanci Gumsu ta fada mata 'yar ta ba shegiya bace da ubanta kuma itama bada son ranta bane amma ta san halin Ya Gumsu, zata tara mata mutanene aka, ta wulakantata gaban bayin ta, su taru su zubar da mutuncin mai Askira don ta tabbata Gumsu dambe take so su yi ba wani abu ba, ta samu hanyar lalata maganar auren, to ko za'a lalata zancen auren nan ba daga gareta ba, da Gumsu ta san halin da ta ke ciki akan auren da ta tausaya mata, itama bata so, ko kadan bata so. Saidai ta zabi farin cikin Askirama akan nata da na Sa'ade. Don haka ta daure ta cije bata fito ba, ta bar Ya Gumsu ita kadai tana ta zage-zage, bakaken maganganu ba irin wadanda bata fada akan Bilkisu ba, har da cewa da ganin ta dama an ga tsohuwar karuwa ta zo ta hargitsa musu miji bakidaya ya daina ganin kowa da gashi sai ita, duk wannan bai isheta ba ta zo ta hada auren masifa da bala'i a cikin zuri'arta, to ko zata yi yawo tsirara sai Yarima ya sakar mata 'yar ta. Kuyangi da bayin Fulani duk sun sunkuyar da kai ko motsi sun kasa, sai yanzu suka fahimci dawa aka daurawa Yarima aure, jikin su yayi matukar sanyi musamman Fanna, hawaye ta soma na tausayin Sa'ade don bata cancanci aure na rashin kwanciyar hankali irin wannan ba ko shekaru ashirin bata yi ba. Saida Ya Gumsu ta tabbatar ta gayawa Bilkisu maganganun da har ta mutu bazata manta ba, in kuma tana da zuciya to zata karbi 'yar ta daga auren Yarima sannan ta bar falon, duk wannan bai isheta ba ta so ne Bilkisu ta fito tayi mata dukan da Askirama zai kasa ganeta. Ita kuwa Sa'ade tana daki a kwance, tun shigowar Ya Gumsu data soma dukan kofar Fulani ta taka aguje ta shige toilet ta rufe kanta, a zaton ta Ya Gumsu ta samu tabin hankali ne, so yawancin duk abubuwan da take fada bata ji su ba kasancewar kofar sound proof ce. Bayan fitar Ya Gumsu data ji shirun yayi yawa sai ta fito, a guje ta nufi kofar Fulani tana kuka tana rokon ta ta bude. Kome Fulani tayi tunani? Sai kawai ta taso ta bude kofar. Halin da Sa'ade ta ganta a ciki ya matukar tada hankalinta, fuskarta ta kumbura tayi jazur idanun ta sun yi luhu-luhu. Sa'ade ta fada jikin Fulani ta wani irin rungumeta tana tambayarta "dukan ki ta yi? Is she lunatic?" Duk da halin da Fulani ke ciki sai da Sa'ade ta sanyata murmushi. Ta ja ta suka shige ciki bayan tasa mukulli ta rufe kofar. Suka zauna a tare a gefen gadon ta. "Ba duka na tayi ba, zagi na dai kawai tayi saboda an aurawa dan ta 'ya ta". Innocently Sa'ade tace "to ke ina ruwanki don an yiwa dan ta aure? Ko ke kika ce ayi masa?" Fulani tayi murmushi ta murza tausasan hannun Sa'ade cikin nata sannan tace. "Laifi na gareta shine ni na haifi 'yar da Askirama ya aurawa dan nata, bayan wannan bani da hannu a ciki". Sa'ade ta yamutse fuska tace "ban gane ba? Zarah ta isa aure ne?" Kwatakwata ta manta itama 'yar Fulani ce tsabar rudun da kalaman Fulani suka jefa ta". "Zarah kadai na haifa? Kafun in samu Zarah wa na fara samu?" Sa'ade ta luluka a duniyar a tunani, ita lallai so take ta canko wa Fulani ta haifa wanda ya isa aure amma tunanin ta ya kasa bata, domin bata ga marabarta da Zarah ba. Murmushi Fulani ta sake yi sannan ta rungume Sa'ade, "ki yi hakuri Sa'adatu kin ji? Mun yi miki laifi daga ni har Askirama, ya nemi alfarmar in bashi ke ya aurawa Yarima nikuma kinsan bazan iya juya masa baya ba. Tunda daga ni har ke zamansa muke yi cikin gidannan mu abin ikon sa ne, sannan in da halarci ko mahaukaci Askirama ya kawo yace ki aura daga ni har ke mun isa mu ce a'ah? Balle dan cikin sa mafi soyuwa a gareshi?" Sa'ade sauraron ta take absent-mindedly tana hada daya da biyu domin ya bata ma'ana. Aure.... ita da Yarima......Yarima wanne? YARIMA! Yarima!! Yarima!!! Shikadai ne mai wannan sunan duk masarautar Askira. "Don Allah Fulani ki fiddani duhun da kalamanki suka sanya ni.." ta fada cikin karkarwar jiki data murya. Ta kama hannuwan Fulani biyu ta rike tamau a cikin nata. Fulani ta ga wannan shine lokaci mafi dacewa da zata gayawa Sa'adatu komai, tunda bakin alkalami ya riga ya bushe. Tiryan- tiryan ta gaya mata mafarkin da Askirama yayi akan ta da yadda ya roketa ta bashi aurenta....da kuma auren da aka daura dazu....."Shine fa Ya Gumsu ta zo tana wannan jidalin". Ita dai Fulani ta san Sa'ade na sauraron ta amma bata san lokacin da ta fado jikin ta yarab! Cikin hali na unconsciousness......kamar suma, kamar fita hayyaci, cikin biyun bata san wanne Sa'aden ta ke ciki ba. Sai ta rungumeta tana kuka abin tausayi ta rasa wane irin taimako ya kamata ta bata.... MASARAUTARMU! Ba ta taba jin tausayin Saade da soyayyarta ba irin yau, yau din da ta tabbatar sun kusa rabuwa, rabuwa ba ta aje a dawo ba, aah rabuwa irin ta kowacce diya mace da iyayenta idan munzalin aure ya riske ta. Fulani ta rasa taimakon da za ta bai wa Saade da ke kwance a jikinta numfashinta na shirin barin gangar jikinta. Ta san Saade za ta razana in ta ji zancen nan, amma ba ta zaci har haka ba. Abin da ba ta sani ba shi ne, Saade ta san sirrin Yarima, ta san na matarsa Aisha-Sultana, tana kyamar dabiunsu na sabon Allah fiye da yadda ba a zato. Hakan kuma bai hana ta ganin wani irin girman Yareema Sageer ba, da kimarsa cikin idanunta, saboda iyakar kyautatawa a zamanta tare da su Yareemah ya yi mata. Amma kalmar AURE a tsakaninsu, ai is underestimated. Wani abu ne da hankalinta da tunaninta ba zai dauka ba. Kullum kallon kanta ta ke yarinya karama tamkar Zarah. A aura mata Uncle Yareema ta kai shi ina? Matarshi ta sha giya ta yi mata shegen duka ko kuwa za ta iya manta kalmar zina' da Sultana ta ce yana yi? Duk da ba ta gama sanin mene ne ainihin maanar kalmar zina ba, amma ta fahimci wani abu ne mummuna, abin kyamata a addini da alada, kuma da shi za ta ke kallon Uncle Yareema in har ba ta samu tabbacin ya tuba ya bi Allah ba daga bakinsa. Ba ta taba kawo wa ranta aure a nan kusa ba, karatu ta ke so, shi ne kuma burinta, sannan tana matukar jin dadin abunta, yau da ba Askirama ne da kansa ya yi mata wannan yankan kaunar ba, cewa za ta yi ba ya kaunarta don ba shi ya haife ta ba. Amma ta sani, ta kuma amince kaunar da Mai Askira ke mata daga Allah ne. ba zai taba yin wani abu da niyyar cutar da ita ba, amma har abada zuciyarta ba za ta yi amanna da auren Uncle Yareema ba. Kamar yadda ba za ta iya karbarsa a matsayin miji ba. Ba gara mata auren Saidu ba in ma auren ya zama dole? Shi ne tsaran aurenta. Fulani robar ruwan faro ta dauka ta yi ta shafa mata a fuska, wuya zuwa kirjinta. Ba ta fasa ba sai da ta ji Saade ta saki nannauyar ajiyar zuciya. Ta kara langwabewa a kafadar Fulani ba ta kara dagowa ba. Duk suka yi shiru cikin wannan yanayin, kowanne da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Zuwa can Saade ta yi magana a hankali. Ni bana son Uncle Yareema Fulani, kamar yadda Mamanshi ba ta sonki. Ki ba wa Maimartaba hakuri, ba zan iya ba. Ta soma wani irin kuka a hankali mai girgiza zuciyar mai sauraro, balle kuma zuciyar UWA! Sosai kukan na Saade yake motsa zuciyarta. Ta shafa kwantaccen gashin kan Saade da hannun damanta ta ce. Saadatu, me zan yi in faranta miki? Ki fadi ko mene ne, amma ban da cewa ba za ki yi auren nan ba. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Laifi kan laifi mun yi miki ni da Askirama, ina rokonki ki dubi Allah da darajar da Allah ya bai wa iyaye a kan
Chapter 19 · 0% Book details