← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 22

Sashe 10

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kayan barci ne na RALPH LAUREN farare sol a jikin sa. He never looked so handsome in her eyes like today. Ya tsaya a kanta ya harde hannayensa a kirji yana kallon ta with furious eyes... "Sultana why? Ba na hana ki shan giya ba? Ko syrup ban hana ki sha ba? Ban gaya miki haramun ne a muslunci ba? Idan da kin yi na kyale ki yanzu kin sani ba mu kadai bane a gidannan, a slight mistake will probably go to my father, har yanzu jiki na na bani spy ce ya sanya mun. Ki yi a hankali idan ba kina son janyo min bala'i ba". Ta daga rinannun idanun ta ta dube shi, cikin maye tace "I....i cannot live without beer, a haka ka ganni ka aure ni, kai ma ka sani bazan taba iya barin giya ba". "Sai ki zaba ko aure na ko giya, tunda na sanar dake addinina ya haramta kika ce kin amince zaki daina, tunda kika fara aiki na san kin koma shan beer, sallah kin dade da daina ta, na sa miki ido ne don in ga iya gudun ruwan ki, and now na lura duk musluncin ki ba na gaskiya bane kin dade da daina sallah. Ni kuma bazan zauna da kafira ba". Ya fadi yana watso kwalaben dake jere cikin firji, ya hada su da bango ji kake taratsatsa! "Kika sake shigo min da wannan kazantar gida, zaki ga yadda zamu kwashe, i'm not that fool and i respect my religion......". Wani wulakantaccen kallo Sultana tayi masa....tace "addini! Kai nan har kana da bakin cewa ka san addini? Addinin naka ne ya baka damar yin adultery? Tunda na san ka na san you are an adultrer wanda baya iya rayuwa sai da mata. Na dauka in mun yi aure shikenan zaka bari, gara ni giya da kayan maye kawai nake sha amma bana zina, balle da aure na". Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka fuskarsa ta koma, bai taba sanin ta san wannan side din nashi ba, abinda bai sani ba shine tana bibiyar wayar sa. Sultana ta lura da efffect din kalamanta akan sa, sai ta yi wani miskilin murmushi "tunda na barka kana zina, ban taba takura maka ba, sai ka bar ni in sha giya, ko wannan yarinyar ta bar min gida......" ta mike tana layi tayi toilet ta bar shi a wajen. **** Kwana biyu basa magana da juna, abinda basu taba yi ba a rayuwar auren su, wani abu da Sultana ta tsiro da shi don ta baiwa Yarima haushi shine ta daina boye shan giyar da kayan mayen ta, nan falo take zama ta baje tana abin ta. A ranta ta kudure duk ranar da ya gayawa iyayensa tana shan giya itama tace musu yana neman mata. Gara ma yayi hakuri su ci gaba da zaman su yadda suke yin sa, wata figigiyar yarinya bakauyiya bata isa ta canza mata rayuwa ba. Sa'ade ta shigo falon da sallama, misalin karfe shidda na yamma, direbanta Salis ya riko mata manyan littafan chemistry har zuwa kofar shiga falo, ya mika mata tayi masa godiya. Tana kokarin shiga Yarima na parking. Ta juya suka hada ido ta cikin gilashin motar sa, sai ya yafito ta, yace "Sa'adatu help me with these files" ta karasa cikin nutsuwa ta karba, shi kuma ya dauko daurin answer sheets na daliban sa ya bi bayan ta suka shiga falon tare. Nan idanun sa suka yi kyakkyawan gani. Kamewa yayi a inda yake tsaye, a lokacin ta kai bottle na whisky bakin ta, ta gefen idon sa ya saci kallon Sa'ade don ganin reaction din ta, sai ya ga babu wani sauyi a tare da ita, ga dukkan alamu bata san menene a hannun Sultana ba, ta dauka just lemo ne. Sannu da gida kawai ta yiwa Sultana ta ajiye masa takardunsa bisa centre table, daga nan bata kara kallon su ba tayi shigewar ta daki. Yayi catching breadth din sa da karfi tana bada baya ya wankawa Sultana mari, ya sake wanka mata, sai da ta nemi jin ta da ganin ta na wucin gadi ta rasa. Tana farfadowa ta kai hannu zata rama ya kama hannun ya murde shi. Ta saki karar data kai kunnen Sa'ade. Har zata fito da gudu ta tuna hudubar Fulani (ba ruwan ki da shiga shirgin da ba'a sanya ki ba) tunda dai ta san su biyu ta bar su. Kwanan tashin hankali aka yi tsakanin ma'auratan, irin wanda bai taba faruwa tsakanin su ba, zagi ta uwa ta uba babu irin wanda Sultana bata yi wa Dr. Sageer ba, har tace duk da kasancewarta kafira kamar yadda yake kiranta bata taba zina ba shi ya koya mata, shi yayi disvirgining din ta, musluncin sa bai kare shi da komai ba, fasiqi mara tsoron Allah. Gara ita giya kawai take sha. Duka wannan a kunnen Sa'ade, wadda hayaniyar su ta hanata barci, ta tsaya jikin kofar dakin ta sai shivering take (karkarwa). Bata taba jin abinda ya kada ta ya gigitata irin wannan ba, gidan masu zina da shan giya aka kawo ta! Uncle Yarima da take gani da matukar girma da kima shine mai yin zinar? Ko dai Sultana karya take yi? Abinda ta gani tana sha dazu shine giyar kenan kuma shi ya hada fadan? Tana jiyo kukan Sultana da alama marin ta ya kara yi, jikin ta na rawa ta dauki waya ta kira Fulani, hawayena zuba mata tace "Fulani! Ni dai gobe a zo a dauke ni bazan iya zama a gidannan ba, zan koma hostel" cikin muryar kwantar da hankali Fulani tace "take it easy....gaya min me ya faru? Ana miki wani abu da ba kya so ne?" Cikin kuka tace "no, Uncle Yarima is very nice to me....amma yana dukan matar sa....gata can sai ihu take.....kuma ta ce shi mazinaci ne...." ba shiri Fulani ta dauke wayar daga kunnen ta ta juya, sai idon ta cikin na Askirama da ke gefen ta da alama shima sauraron wayar yake yi don ta manta a (hands-free) take. Yanayin da ta ga fuskar sa a ciki yasa ta jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaqe Sa'ade har sai ta daina numfashi. "Wallahi maganar Sa'ade shirme ce ni na tabbata....". Fulani ta fada muryar ta na rawa, kwalla cike da idon ta. Daga taimako Sa'ade zata baro musu tashin hankali da yake ita butulu ce, ina ruwan ta da abinda ke faruwa tsakanin Yarima da matar sa? Bayan ta gargadeta? Sai ta tuna Sa'aden bata san tana turakar Askirama ba, kuma ita ta bata damar duk halin da take ciki ko karfe nawa ne ta kira ta ta gaya mata. "Ba shirme bace Bilkisu..... he has this taboo since childhoood". Ya fada muryar sa abin tausayi. Har yaran bayi yake raping...na dauka ya bari, na dauka girma ya sa ya nutsu, na dauka aure ya canza shi...ashe i'm mistaken. To aikin zai bari ya dawo gida kusa da ni kawai ya karbi sarautar gidan su, in cika masa gida da mata da kwarkwara tunda hakan yake so.....da raina da lafiya ta bazan bar shi ya karasa rayuwar sa a haka ba........". The way Mai Askira ke magana ya taba zuciyar Bilkisu, bata taba ganin sa cikin wannan sad mood din ba. A muryarsa da fuskarsa bakin ciki ne zallah. Ya kare zancen sa da cewa "zan raba Sa'adatu da gidan sa, tsoro na Allah yanzu tsoro na kada itama ya taba ta......" "Haba-haba Askirama! Kada bacin rai ya kai ku ga yi masa mugun fata, ni na tabbata ko Yarima na neman mata bazai nemi na cikin gida ba balle Sa'adatu kanwar sa, don Allah a kyautata masa zato, kada a raba shi da aikin sa he is very young da karbar sarauta yanzu, sannan kaima in ka zauna a gida me zaka yi? Da cikar lafiyar ka da shekarun da basu kai 70 ba. A yi masa hakuri ayi masa addu'a, ita ce kawai mafita. Kuma daga Sa'ade ta fadi abu ai bai kamata mu yarda ba tunda bamu gani da idon mu ba". Mai Askira yayi murmushi mai ciwo "baki san Yarima ba!" Da kyar, da lallashi da ban baki Fulani ta ciwo fushin maimartaba ya fasa cewa Yarima Sageer ya dawo gida, amma ya ce dole zai dauki mataki. Shi ya gama amincewa Sa'ade ba karya take ba, ta fadi abinda ta gani ne da abinda ta ji tabbas. Koda ya tura Sa'ade gidan Yarima yana da dalilin sa, gashi tun ba'a je koina ba zuwan ta ya sa yanzu ya san halin da Yarima yake ciki. **** Da asubah Fulani ta koma daki ta kira Sa'ade, wadda ta kwana zungurgur a bakin kofa, ta dade bata ji ma'auratan sun gama fadan nasu ba, ta ji abubuwa da yawa da suka razanata, Sultana ta dage in ya takura mata akan shan giya to zata koma addinin ta na Jew (ridda). Shikuma ya ce ta koma din, amma ta sani muddin ta bar muslunci a bakin auren ta. Zina kuma yanzu ya fara in ita uwarsa ce ta hana shi. Sa'ade bata taba fadawa tashin hankali irin na yau ba, ta ji ta tsani Yarima da matar sa bata ko marmarin sake ganin munanan fuskokin su. Kuma sai gwada wayar Fulani take ta tubure mata azo a dauketa ta kasa samun ta, sai goshin asubahi sannan ta samu kiranta. Jiki na rawa ta amsa wayar, cikin kuka tace "Don Allah Fulani....don Annabi ki aiko a dauke ni, bazan kuma kwana a gidan nan ba, ko na minti daya ban yi barci ba, they are fighting....." Fulani tace "Ki nutsu Sa'adatu ki saurareni, babu inda zaki, ba ruwanki da fadan su tunda basu sanya ki a ciki ba, kiyi kamar baki ji komai ba ki cigaba da harkokin karatun ki. You are not there for Yarima or matar sa, you are here to study. Kada ki kara sauraron maganganun su kin ji na gaya miki. Yanzu baki san abinda wayar ki ta jawo ba. Askirama ya ji duk abinda kika fada kuma ya ce sai ya dau mataki akan dan sa, duk akan surutun ki, ina ruwan ki?" Cikin kuka Sa'ade tace "wallahi ba sauraron su nake ba, ba
Chapter 10 · 0% Book details