Sashe 14
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hankali don tabbatar da Sa'ade ce yake gani a motar wani ko wacece? Fasa bude motar yayi ya kafa musu manyan lumsassun idon sa har Sa'idu ya kashe motar Sa'ade ta bude ta fito tana masa godiya. Sa'idu ya so ya fito ya gaida Yayan Sa'ade amma yadda yaga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas dole ya kama kansa, ya ja motar sa da gudu ya bar harabar gidan don kwarjinin Yarima da haibar sa da cikar kamalar sa kadai ya tabbatar masa ba karamin mutum bane, kada yaje ya gane shi ma wani abu ya samu karatun sa, duk da ya so ya fito ya gaisheshi ya gaya masa taimaka mata kawai yayi shi dan ajin su ne, amma ina! Tsoro ya hana shi. Makarantar ma bai koma ba ya gudu gidan su a unguwar Maitama. Ta gaban sa Sa'ade ta zo ta wuce amma ga mamakin sa ko kallon sa bata yi ba ta wuce ciki. Mamaki ya kusan kayar da shi, bin bayan ta yayi cikin takunsa na kasaita. Tana saka kafa a dakinta ta turo kofar yasa hannu ya dafe kofar. Sai ta sakar masa, ta juya ciki ta na kokarin sauke jakar dake goye a bayan ta wadda ta lamushe dukkan komatsanta harda laptop. Muryar Yarima har tsakar kanta, babu alamun wasa ko kadan a tattare da shi. Zata iya rantsewa bata taba jin sa yayi magana da irin wannan muryar ba. So furious, angry and jeolous.....! "Sa'adatu who is this boy?" Bata san yaya aka yi ba, bata san wa ya kitsa mata ba, kawai sai ta samu bakin ta da cewa "saurayi na ne" bayan ita kanta bata gama sanin ma'anar kalmar saurayin ba. Kawai ta san ta tsani Uncle Yarima ne yanzu, tunda dukan matar sa yake yi, in ta sha giya ai shi ya bata dama. Idanunsa sun rikide sun juye zuwa wani yanayi da bazata iya fassarawa ba. "Look into my eyes...and tell me he's your boy friend" kokarin ja da baya take. Data rasa mafita, ga zuciyarta na wani irin azalzala da mixed feelings; haushi, tsana, da zazzafar soyayyah duka a lokaci daya, kawai sai ta saka kuka. "Ni dai a maida ni Askira, wallahi na gama zaman gidan ku" Yarima ya ja da baya sabida da karfi ta fasa kukan. "Da mu kayi miki mene?" Ya fada yana hararar ta, in wani yaji irin kukan da ta fasa tsammani zai yi wani abun yayi mata. Ba ta ce komai ba sai cigaba da kukanta. Da zata iya da ta ce dashi sabida dukkanku fasikai ne marasa tsoron Allah. Amma ta san ko giyar wake tasha bazata iya dubar tsabar idon Dr. Sageer ta gaya masa haka ba. Apart from all these she respects him so much. Yana da wata irin kima a idanun ta da bata san yaushe ta samu matsugunni a zuciyarta ba. Tafi danganta hakan da kulawar sa da kyautatawar sa gareta. Yarima ya dubeta a fusace, ya rasa yanayin da yake ciki yau, amma ya tabbata bai taba ganin abinda ya bata masa rai a duniya irin Sa'adatu da saurayin ta a mota ba, yaga yadda hawaye ke gudu akan kundukukinta kai ka ce wani mugun abin aka yi mata. Ya nunata da dan yatsa ba tare da ya bari hawayen da take zubarwa sun yi tasiri akan sa ba "Yau ta zama rana ta karshe da zai kuma tako min gida, ba shi kadai ba kowanne rubabben saurayin ki ma, in ba haka ba in gayawa Fulani da maimartaba su cireki a makarantar su yi miki aure tunda hakan kike so". Sa'ade ta zaro ido abin dariya abin tausayi "Uncle Yarima wasa nake ba saurayi na bane ba, wallahi, dan ajin mu ne" ya juya ya fice bai saurareta ba, damuwar duniya Sa'adatu ta shigeta, ba abinda take tsoro, taki jini take kuma gudu a rayuwar ta irin AURE! Saida yayi kwana uku bai kara kula ta ba, bai kara nemanta ba, he's really suffering a ruhi da zuciyar sa akan ganin Sa'ade da saurayi akan dalilin da bai sani ba. A haka su Sa'ade suka fara jarrabawar karshen zango babu shiri ko kankani tsakanin ta da Yayan nata Yarima. Ranar da sukayi takardar karshe ta kira Fulani ta gaya mata, Fulani ta gayawa maimartaba, shikuma ya kira Yarima yace yasa direba ya kawo Sa'ade gida tayi hutu. Yarima yace dama shima zai shigo Askiran jibi, zai taho da ita da kansa. Sa'adatu na kwance a gadon ta tana karanta mujallar turanci ta 'Thrills and Boom' taji knocking a kofar ta. Ta gyara kwanciyarta da dankwalin ta daya cire sannan tace "yes". Yarima ya sanyo kai a dakin, t/shirt ce a jikin sa fara kal an rubuta Marks&Spencer da bakin rubutu, sai bakin wandon jeans mai kauri. Hararar ta Yarima yayi sannan ya jingina da kofar, a hankali ya ce. "Sabida na hanaki kula samari, shine kika daina gaishe ni ko?" Sa'ade ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, amma sosai taji kunya, wai wa yace ma Uncle Yarima Sa'idu saurayin ta ne? Bata cika son magana tayi tsayi a tsakanin su ba, karatun ma da yace zai koya mata bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi saida ta san yadda tayi ta kaucewa hakan ta roki Sa'idu ya koya mata lokacin jarrabawar kwas din, yana da effect mai karfi kanta wanda shi bai sani ba itama bata sani ba, abinda ta sani kawai shine bata son mu'amala mai zurfi a tsakanin su. "Ki shirya gobe da asubah zamu kama hanyar Askira, maimartaba yace a kai ki kiyi hutu" bata san lokacin da ta dago zaune ba tana ta faman blushing, bai tsaya kallon ta ba yasa kai ya fita. Tun a daren ta hada duk abinda take bukatar tafiya da shi. Baccin ta ma ragagge ne sabida doki. Tayi kewar Fulani da Zarah.....Shi kansa Askirama ta yi kewarsa. Washegari data yi sallahr asubah bata koma barci ba, wanka tayi, tayi ssaukar shiga ta bakar abaya mai santsi da adon stones sosai a jikin ta. Bata shafa komai a fuskarta ba sai wet-lips ta kuma fesa sassanyan turare. Ta zauna bakin gadonta da trolley dinta a gaba tana jiran Yarima. Bai fito ba sai wajen karfe shidda na safe, kallo daya tayi masa da ya murda kofar dakin ya shigo bayan tayi masa izni, taji bazata iya jure kallon ba, kwayar idanunta ta zamo mai rauni sabida yau ya fito Prince dinsa. Ta taba ganin maimartaba da irin kayan jikin sa, yakan saka kayan in zai zauna cikin iyalinsa, kaya ne kufta da wando na sarautar Askira wadanda basu cika nauyi ba. Amma kuma sun sha aikin zare na silver da hula zanna bukar a kansa. Kasancewar kusan kullum cikin shigar suit take ganin sa yau sai ya zamo mata wani daban, classique and elegant kai kace Askirama ne ya zama yaro. "Lets go!" Inji Yarima, ganin ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bayan a badini kirjinta ne ke wani irin harbawa da sabbabin emotions da bata san daga ina suke fitowa daga karkashin zuciyarta ba. Hannu yasa ya ja trolley dinta. Ya fita ta bishi a baya bayan ta dau handbag dinta tana mamaki a cikin ranta; Yarima ya dau kayanta da kansa. Sai taji har tsigar jikin ta na tashi da wani irin feelings mai sanyi a zuciyar ta. Hakan kuma bai janye bakin fentin data ke kallon shi dashi ba. A falo suka ci karo da Aisha - Sultana, kayan barci ne a jikin ta, ta tsaya jingine da kofar dakin ta tana kallon su, ta gabanta Yarima ya wuce dauke da jakar Sa'ade, Sa'aden na gaisheta da safiya, wata harara ta zabga mata ba tareda ta amsa ba. "Mun tafi Askira Aunty, sai na dawo" jin bata amsa mata ba ta wuce ta, ta tadda Yarima a mota, Salis ne ya ja su. Ta dauka a motar zasu tafi har Askira amma sai ta gansu a filin jirgin saman Abuja. For the first time Sa'ade a jirgi, in ka gansu itada Yarima tsammani zakayi sababbin couples ne sabon aure duk da babu hira a tsakanin su. A cikin jirgin Azman ne mai zuwa Maiduguri a first-class seats, ga kujerar ta ga ta Yarima, Lokacin da waitress ta kawo abin motsa baki kasa cin komai tayi sabida uneasiness din da take ciki na zama a gefen Yarima. Ga kamshin Paco Rabbanne dinsa dake kara hargitsa ta. Shikuwa yayi amfani da wannan damar wajen kare mata kallo, kallon da bai taba yi mata ba, har ya zarta ka'idar muslunci domin kallo ne na kurullah. A zuciyar sa ba abinda bai fada ba, wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani, a zahirin sa kamar ba ita yake kallo ba. Bai fi minti goma ya rage suyi landing ba Sa'adatu ta soma jin amai na taso mata sakamakon wani Igbo da ya gifta ta gabanta yana warin qashi irin na maza, ai kuwa tana yunkurawa domin ta tashi sai amai ya kelayo a jikin Yarima Sageer, basu da yawa a first class seats din don haka hankalin sauran mutanen ya dawo gare su, Sa'ade ta hau zazzare ido cike da tsoro bakin ta na rawa tana son furta ban hakuri kalaman sun ki fitowa. Amma ga mamakin ta ko a fuska bai nuna kyama ba, wani irin kallo yayi mata yace "sai kin goge min shi tas!" Tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka don damuwar abinda tayi masa "...don Allah kayi hakuri Uncle Yarima....ban yi da sani ba" a ginshire ya ce "na ce kin yi da sani ne?" "To kayi hakuri don Allah bazan iya goge maka ba" suna wannan jayayyar sai ga waitress tazo don ta gyara wajen tana ta yiwa Sa'ade sannu don a zaton ta ciki gareta. Kasancewar kayan rubi biyu ne ta saman kamar jabba take mara nauyi akwai jamfa daga ciki yasa ya cire ta saman. Sa'ade tayi maza ta dauko turarenta a jakarta ta mika masa. Karba yayi yana jujjuya shi a hannun sa 'sapphire' itama Fulani ce ta bata, a tunanin ta zai bukaci turare tunda tayi masa kayan karni. "Me zan yi da turaren mata?" "Ka fesa saboda karni" Ta fada kamar zata saki kuka don damuwa, ta rasa