← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 22

Sashe 7

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar sai ta zama ranar reunion ta soyayyar uwa da 'yar ta. Kusan kwanan zaune suka yi a dakin Sa'ade, tana bata labarin rayuwar data yi tare da mahaifin ta a garin Tsanyawa tun tana karama har girmanta, da rayuwar wahalar data yi a hannun inna Laure da kuma yadda mutuwar mahaifinta ta kasance, har zuwa yadda suka yi suka zo Askira ita da Baba Saleh. Sai ga Fulani Bilkisu tana share hawaye, "nikuma na zo na yi shekaru shidda ina cuzguna miki, a matsayi na na mahaifiyar data haife ki. Bayan a lokacin ne ya kamata ki ji dadi kamar kowanne da a hannun uwarsa...don Allah Sa'adatu ki yafe mini". "Na yafe miki Fulani ban taba rike ki ba, kullum ina gayawa raina ne kina da hujjar ki, haka kawai uwa bazata ki dan ta ba, Allah ya yafe mana bakidaya". Tun daga ranar, mu'amalar Fulani Bilkisu da diyar ta Sa'ade ya canza, ta cire mata takunkumin fita, ta bata damar shiga ko'ina take so cikin masarauta, bata ki ba don gaskiya ta fito gaban kishiyoyin ta a yanzu cewa Sa'ade 'yar ta ce, tunda ta san ba shegiya bace da uban ta. Ta ja ta a jiki har fiye da kima, idan zata shirya abincin mai Askira kasancewar da kansu suke masa abinci sai ta kirata sun shiga kicin tare, tana yi tana mata bayanin yadda ake komai, anan Sa'ade ta koyi girkin sarauta iri-iri dana zamani, kasancewar Fulani Bilkisu kwararriyar kuku. Ta kuma dinga koyawa Sa'adatu tsaftar jiki data muhalli da amfani da turarukan Borno a jiki da tufafin ta. Duk da ta bawa Sa'ade damar shiga koina cikin masarauta Sa'ade bata yawon, kullum tana sassan su ko dakin Fulani, ko kuma suna kicin suna girkin Askirama idan ita ce da girki. Hatta gashin kan Sa'ade Fulani da kanta ke zama ta gyara mata yanzu, gyara na masu kwarewa akan kula da gashi, wata irin shaquwa suke yi cikin 'yan watannin nan wadda basu taba yin ta a shekara shidda da suka yi tare ba, ta yadda har Fulani ta soma zullumin zuwan ranar tafiyar Sa'ade makaranta Abuja. Maimartaba ya fi kowa jin dadin wannan sauyi da ya ke gani a tattare da Bilkisu da 'yar ta Sa'adatu, 'yar da yake jin kamar shi ya haifeta saboda son da yake wa mahaifiyar ta. Jin dadin hakan yasa ya hada musu tafiya umrah karshen wannan watan don dai su kara shaquwa da juna ba idon kowa tare dasu, amma dole tareda Fanna zasu tafi sabida kula da hidimar Fulani. A saudiyyah ba abinda Fulani Bilkisu ke roko a wurin Ubangiji sai miji nagari ga Sa'adatun ta, wanda zai rike mata ita amana ya rike maraicin ta, wanda ba zai taba duban asalin ta ya wulakantata a kan sa ba. Wanda zai zame mata miji kuma uba sannan Yayan da bata da shi a kafatanin rayuwarta. Ta kuma sakankance cewa an amshi rokon ta, don wannan shine ladabin addu'a. Ba son tafiyar Sa'ade jamia'ar Turkawa take ba, amma ta yarda da hujjojin Maimartaba, na cewa gara Sa'ade tayi karatu kafin Allah ya zaba mata mijin aure. Karatun zai zamo gata kuma majingina a agareta ranar da babu su. Suna dawowa suka tarar da sakamakon su Sa'ade ya fito, Mai Askira da kansa ya kira Yarima ya gaya masa kowacece Sa'ade, gaskiyar ya gaya masa cewa 'yar Bilkisu ce. Ya damka masa komai na alhakin nemo mata makaranta da daura masa dukkan nauyin hidimar karatun ta. Ya kuma gaya masa a gidansa zata zauna ba a hostel ba. Wata irin zufa ce ta soma ketowa Yarima ko mu ce Chiroman Askira. A tsarin rayuwar su shi da matar sa, ko kuda basa so ya gifta a tsakanin su balle dan mutum ya zauna a cikin su. An tarbiyyance su da rashin yin musu ga magabatan su, an raine su a bisa bin umarnin na gaba, balle Mai Askira gabadaya. Don haka amsar sa ita ce kawai "toh" amma a ransa ya ce kora da hali kawai zai sa yarinyar ta bar masa gidan sa. To amma kuma Maimartaba ya ce 'yar Fulani Bilkisu ce ta cikin ta, matar da duk fadin gidan su in ka dauke mahaifiyarsa ba wadda yake gani da mutunci kamar ta, ba wadda ke kula da al'amarin sa dana matar sa kamar ta. Anya zai iya wulakanta jinin ta? Babbar damuwarsa Sultana bazata taba amincewa ba musamman sabida yadda take shaye-shayen ta babu takura, ta dauka bai sani ba, amma kallon ta kawai yake, duk abinda take ciki ya sani, baya magana ne don ya san shima da nasa guntun kashin a katara. Aka ce wai in ka ji ma'aurata masu ha'intar juna suna zaman lafiya to tabbata daya na ha'intar daya, babu yadda dayan zai yi ya hana, kada nashi asirin ya tonu. Wannan shine tsakanin Yarima Sageer da matar sa Aisha-Sultana. **** Babu yadda zai yi, haka yasa neman admission din Sa'ade a gaba a washegari a matsayin first thing da ya shiga ofis ya zauna, takardun ta duk sun yi kyau. Ya tsurawa sunan ido.... SA'ADATU HASHIM ASKIRA. Hatta course din ma nasa ta dauka......Pure and Applied Chemistry. "Does she know me?" Ya tambayi kansa cikin mamaki. Salon karatun ma mai Askira ya ce ni zan koya mata??? Tsaki yayi ya ture takardun gefe ya janyo na wasu, a lokacin da Dr. Ziyad ya turo kofar ya shigo dauke da sallama a bakin sa. "Wata hot baby na samo yanzunnan daga zuwa na Millenium Park, akwai abubuwa, kayi maza ka gama mu bar ofis dinnan". Tsaki yayi ya ce "kai baka san halin da nake ciki ba, wata yarinya za'a kawomin riko daga gida, Allah ya sa ba spy mai martaba zai kawo min ba, ko wani ya kai gulmata ban sani ba, ka san a ko'ina yana da jama'a musamman nan Abuja" ya fada kyakkyawar fuskarsa dauke da damuwa tsantsa. Dr. Ziyad yace "i don't think so. How old is she?" "JAMBITE ce fa" "whao!" Inji Dr. Ziyad. Kace sweet 16 za'a kawo mana kawai, yo meye abin damuwa banda mu dinga kwasar rabon mu kawai muna saya mata pizza muna cika mata aljihu? Gida na is very quite and secret ko Sultana bazata san muna kwasar gara ba". Wata muguwar harara Yarima Sageer ya zabga masa, ya tsartar da miyau da sauri. "Allah ya sawwake Allah ya tsare ni, ni ba dan akuya bane, ina dai neman matan bisa titi amma ban da na mutunci balle wadda ta fito daga gidan mu, daga gidan mun ma daga hannun mahaifi na, 'yar matar mahaifi na mai yawan karamci a gareni. Allah ya kiyaye! Iskancin nawa mai limit ne, and i'm hoping watarana in bari gabadaya". Dr. Ziyad ya kyabe baki tareda mikewa tsaye yana dariya yace "kai din? Na yarda bazaka iya neman ta gidan ku ba, ko don kada asirin ka ya tonu, amma bazaka iya barin mata ba i swear ...." Yarima ya dauki mukullan dake bisa teburin sa ya jefe shi dasu, Dr. Ziyad ya dafe keya ya fice da gudu yana masa dariyar data kara masa takaici kan wanda yake ciki, na yarinyar da za'a turo masa babu gaira babu dalili. Cikin sati daya ya gamawa Sa'ade duk shirye-shiryen ta, an dauke ta a NTNU a tsangayar da yake koyarwa (B. Sc Pure and Applied Chemistry). Ya aikawa Askirama admission letter din ta ta email. Abinda ke gabansa yanzu shine ta yadda zai tunkari Sulatana da maganar. Amma abin mamaki da ya koma gida da yamma, ya tarar ta riga shi dawowa, ta shawo ta yi mankas tana kwance dai-dai a tsakiyar falo. Haka ya tsallake ta yana tsaki ya wuce dakin sa ya sunce ya shiga wanka. Yana fitowa ya shiga kitchen don neman abinda zai ci, ya bude firji, abin takaici babu komai sai Giya nau'i nau'i, yanzu Sultana ta daina shakkar ya san shaye-shayen ta, kai tsaye take komai don ta ga baya daga ido balle ya nuna ya san tana yi. Wani mugun tsaki ya saki ya rufe firinjin da karfi, yanzu in yarinyar nan ta zo ta gani fa? Mai Askira yace rana ita yau za'a kawo ta tare da kayan ta su gyara mata daki. Ji yayi yunwar da yake ji ta kama gaban ta, da sauri ya fito ya sa kafa ya shuri Sultana da karfi. Ta bude idanu jazur dasu, ta sauke su a kan shi, dama gasu tun asali kamar na mage (brown eyes). A fusace yace "ki tashi ki kwashe abubuwan da kika cika min firji dasu, we're having a guest from Askira, and she's going to stay with us for years, so mind yourself else.....duk abinda ya biyo baya ba ruwa na". Sultana tayi mici-mici da ido "bakuwa? A gidannan? Daga Askira? To ban yarda ba" ya galla mata harara yana hango wani irin muni a tare da ita da bai taba gani ba wanda yake bayyana in ta sha giya "sai ki kira maimartaba ki gaya masa" ya jefa mata wayar hannun sa. Har dare suna fafatawa, ta dage sai ya kira Babansa ya ce bata yarda ba, shi kuma yace ba tarbiyyar da aka yi musu kenan ba but she's free to call him herself. "To ko dai aure suka yi maka shine za'a fake da karatu don nasan mamanka bata so na!" Sultana ta fada cikin kuka. Shi don mamakin kalamanta ma dariya yayi, wai aure! Wa ya isa yayi masa aure ba da yardarsa ba? Besides, su gidan su ba'a auren dole. Sannan ya gama aure a rayuwar sa ba zai taba yin mata biyu ba duk da kasancewarsa basarake. Tashi yayi ya dau motar sa ya bar gidan zuwa inda ya tabbatar za'a faranta masa rai, yau ranar kwata-kwata a birkice ta zo masa. He's upset, sannan wannan mahaukaciyar Sultanar ta kara masa bacin rai. Ai kuwa ya samu Dr. Ziyad ya dauko musu baby din da ya gaya masa sun hadu a millenium park, nan ya manta da zancen Sa'ade da Maimartaba ya shantake acan har karfe daya na dare. Sanda ya shigo gida ya tadda Sultana ta baje kwalabe sun fi biyar duk tayi emptying din su. Ta koma zukar marijiuana cikin tsumma, gashin kanta a birkice, gabadaya sai ta
Chapter 7 · 0% Book details