Sashe 2
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read
BAYAN SHEKARA BIYU!
Abubuwa da yawa sun faru cikin shekaru biyun nan, wadanda yawanci rigingimu ne na kishi a cikin gida tsakanin Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Sun ki zama lafiya da juna, amma kashi 80% na rigingimun in ka bincika zaka tarar laifin Ya Gumsu ne, tana kishi da Fulani Bilkisu ba dan kadan ba, a bisa abubuwa da dama; muhimmi shine son da Askirama ke mata wanda ya zarce na kowacce cikin matan auren sa, kuma ba ya iya boyewa. Yayin da ita Ya Gumsu a wurin ta ita ta cancanci wannan fifitawar a matsayin ta na uwar Yarima kuma uwar manyan 'ya'yan sa.
A haka dai ake rayuwar, da dadi ba dadi a gidan sarkin Askira, kamar kowanne gidan sarauta, duk wani babban gida ko ba na sarauta ba ya gaji haka, girma na kara kama kowaccen su, kamar kuma suna girma ana kara rura wutar kishi a tsakanin su.
A yau Litinin, gidan sarautar Askira an tashi da hidimar shirin tarbar Yarima Sageer wanda zai sauka a yammacin yau tareda matar da zai aura, 'Rose Hathaway'. Labari ya gama baza cikin gida na inda Yarima ya nemo aure. Surutu ba irin wanda ba'ayi a sassan kowacce daga cikin matan gidan in ka dauke unguwar Fulani Bilkisu, ita kadaice ta goyawa Yarima baya akan auren da yake so kuma bata yi Allah wadai da zabin nasa ba, ko dama kusan koyaushe ra'ayinta na zuwa daidai dana maimartaba ne.
Yamma lis Yarima Sageer da dan uwansa Awaisu da Rose wadda ta sha doguwar riga har kasa da mayafinta kamar balarabiya suka iso masarautar Askira karkashin rakiyar dogarawan fada masu yawa, wadanda suka dauko su daga filin jirgi daga Maiduguri a mota civilian ta Askira Emirate.
A wannan lokacin Sa'ade na makaranta tana zana jarrabawar shiga aji biyar SS 2. Ya Gumsu ta yi tsalle ta dire tace ba dai baturiyar Yarima a sassanta ba, babu ita babu wannan auren koda za'a sa mata wuka a makoshi. Don haka Mai Askira ya ce a kaita unguwar Fulani Bilkisu ta zauna karkashin kulawar ta.
Dakin Sa'ade ta sa Fanna ta gyarawa matar Yareema, duk abinda zata bukata Fulani ta tanadar mata, to saidai hira ta gagara tsakanin su don Fulani bata iya turanci ba, saidai ta yi magana da Yarima a waya shikuma ya kira Fulani ya gaya mata abinda ta ce. Kwanan su biyu da dawowa aka musuluntar da Rose a masauratar Askira aka daura auren ta da Yarima Sagir, babu wata gayya ta kunya da sarki yayi iya jama'ar gari ne kawai da king-makers suka shaida auren Yarima Sagir, bai gayyato 'yan uwan sa sarakuna ba, shi kansa bai san meyasa a can kasan ran sa baya farin ciki ko kadan da auren ba, duk da cewa bisa amincewar sa da yardar sa ne. Ya dauka Rose zata zo tare da wani nata, sai ya ganta zikau daga ita sai jakar kayan ta... sai ya soma tambayar kansa ranar da 'ya'yan Yarima suka tambayi dangin mahaifiyar su me zai ce musu???
Ko dai uwar Yareema, Ya Gumsu, ta fi shi gaskiya ne???
****
Babu wani shagalin biki kamar ba auren Yarima guda ba, haka aka dauki amaryar aka kaita gidan da Maimartaba ya ginawa Yarima wanda ke gefen masarauta. Gida ne tankarere ginin sarauta kuma ginin zamani, wanda ya lashe miliyoyin kudi har ya zarta ginin masarauta tsari sabida an yi amfani da hikimar kamfanin cosimco. In ka ji ana aljannar duniya to gidan Yareema Sageer ne. Auren Awaisu sai bayan shekara biyu don matar da aka bashi bata gama makarantar sakandire ba.
Rayuwar Yareema da amaryar sa Rose wadda ta karbi suna (Aisha - Sultana), sun dora ta ne daga inda suka tsaya a Amsterdam, wato rayuwar nasara zallah, don su kan manta cikin masarautar Askira su ke, Yareema na matukar son Sultana yayin da ita kuma ta karbi muslunci ne don son data ke wa Yareema ba don tana ra'ayi ba, don ya ce mata shine kadai hanyar da iyayen sa zasu yarje mishi auren ta.
Don haka kusan zamu iya cewa addinin ta karbe shi ne kawai a baka, amma daga sanda suka bar cikin gida zuwa nasu gidan ta jinginar da sallahr data fara a sassan Fulani Bilkisu, ta gayawa Yareema ita bazata iya kullum ba, akwai wahala sai ta saba tukunna, yayin da Yareema ya nuna ba zai lamunci hakan ba sai take yi a gaban sa, in baya nan kuwa a hadu a gaba.
Sati hudu ana barzar amarci, an cika musu gida da bayi da hadimai, Sultana sai a lokacin take lakantar ko wanene Yareema Sageer Yusuf Askira? Ashe a baya bata san komai a kan shi ba? Banda kasancewar shi abokin shashancin ta, ta fahimci a yanzun tana sahun gaba na mata masu sa'a a rayuwa, domin Sageer daya ne cikin dubu, wanda irin sa ta fannin nunawa matan su soyayya tsiraru ne a cikin al'umma.
He's genius a halayya da dabi'a, superb a rayuwar auratayya, splendid a tafiyar da matar sa.... Ko don ta cigaba da rayuwa da Yareema zata cigaba da zama cikin rigar addinin sa mai wahala, amma ba don ya dadata da kasa ba.
Watanni ukku Yareema ba ya komai sai neman aiki ta yanar gizo ba da sanin maimartaba ba, sai amarci da mai jan kunnen sa, Fulani Bilkisu ta zama uwar dakin Sultana ita ke kula da komai da ya shafe ta don Ya Gumsu ko gaisheta tayi bata amsawa, haka Ya Maira bata taba takowa gidan ta ba sai Humaira da Naja'atu, mazan kam suna zuwa sosai wajen Yareema musamman Ashgar wanda ya maida gidan wajen hirar sa sabida yadda Yarima ke jan sa a jiki, don yana tsananin tausaya masa, kuma yana samun sauki sosai daga rehabilitation din da Yarima yasa shi ya samu a kasar Amsterdam.
Ayyuka har biyu Yareema ya samu a lokaci daya, NTNU (Nigerian Turkish Nile University) dake Abuja sun bashi aikin koyarwa (lecturing) kamar yadda ya zaba a tsangayar (Pure and Applied Chemistry), haka OAU (Obafemi Awolawo University, Ile-Ife) suma sun dauke shi da gaggawa, tun kafin dawowar sa ya yanke shawarar komawa academia wani professsion da 'ya'yan sarauta basu fiya karba ba. Kamar yadda komai nasa yake daban da na sauran mutane, haka tunanin sa ma ya ke. Ba ya danganta kansa da sarauta ko kadan kamar yadda mahaifin sa ke so, a ganin sa tana hana 'yanci, sannan takura ce. Gashi shikuma mutum ne mai tsananin son rayuwar da babu takura, kuma babu matsantawa a cikin ta.
Mutum ne mai (tsinkaye) da tsantseni a cikin dukkan mu'amalolin rayuwar sa, mai son dogaro da kai, mai zafin nema, mai zafin nama, sannan mai nasara a kan duk abinda yasa a gaba. Bar shi dai da son matan sa (his only shortcoming) abinda zamu iya kira nature a jikin maza jinin sarauta, wanda zamu iya cewa tun bayan auren nan wata irin nutsuwa ta saukarwa Yareema Sageer Askira; Mata suka rage burge shi banda matarsa Aisha-Sultana. Haka ya zauna yana deleting numbobin mata kala-kala yare daban daban dake kan wayar sa, ya na fadawa kansa da kansa; yadda ya bar Amsterdam gabadaya, haka ya baro ta tareda dukkan matan da ya baro cikin ta.