← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 22

Sashe 16

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Rami ne mai tsananin zurfi, wanda har baya iya hango karshen sa sabida zurfin sa, ya leka ciki sabida ya ji kamar muryar Yarima yana kuka yana neman taimako. Bai ga ta inda ta bullo ba kawai ya ganta ne a bakin ramin, tana rike da igiya mai tsayi, tana zuwa bakin ramin ta jefa masa igiyar tace "Kama ka fito da iznin Ubangiji".
Bai ga fuskarta ba sabida ta sunkuya ne akan ramin, gashin kanta ya sakko ya rufe fuskar tata gabadaya, saida tayi magana sannan ya shaida muryar ta.
Ba jimawa ya ga ta kama igiyar nan tana janyo wanda ke ciki har ta fiddo shi tsaf, yana fitowa suka rungume juna suna hawaye. A lokacin ne ya samu damar ganin fuskokin su gabadaya; Sa'adatu ce da dan lelen sa YARIMA SAGEER.
Tamkar an warware masa dukkan baccin da ke kansa ya farka firgigit misalin karfe biyu na sulusin dare, lokaci ne da aka tabbatar mafarki yana iya zama reality. To ko me wannan mafarkin da yayi yake nufi? Sa'adatu as saviour of Sageer? Ba don babu kyau bayyana mafarki ga wani ba, da ya nemi Limamin Askira ya gaya masa mafarkin da yayi. Duk da haka a nasa hankalin, ya fahimci tamkar wani hannun ka mai sanda ne Ubangiji yayi masa, mai nufin akwai wani babban al'amari tsakanin Sageer da Sa'adatu kamar yadda ya so hakan ta kasance a baya.
Bai san sanda ya sa hannu ya soma tashin Fulani Bilkisu wadda ke barci sadidan a gefen sa. Ta tashi tana yamutsa fuska tana mutstsikar ido. Ya ce "Bilkisu bude idon ki ki dube ni". A yanayin da Askirama yayi maganar cikin rauni yasa ta dole watstsakewa.
"Lafiya Askirama? Lafiya gatan mara gata? Lafiya giwan ASKIRA?"
Ta fada cikin tausasa murya, mai Askira ya kama hannayenta duka biyu ya rike cikin nasa. "Alfarma nake nema wajen ki irin wadda ban taba nema ba...... ki bani Sa'adatu in aurawa Yarima a gobe".
Fulani Bilkisu ta ji maganar ne tamkar saukar aradu a kunnen ta, kwakwalwarta ta kasa digesting maganar yadda ya kamata sabida wani abu ne da bata tsammani ba a rayuwar ta. Bata kin Yarima don tamkar dan cikin ta ta dauke shi. To amma neman matan da ake cewa yana yi fa tun bai san kansa ba har girman sa har ita Sa'adatun ma ta shaida da bakin ta? Shin Sa'ade ta cancanci hada rayuwa da wayayyen mutum irin Yarima? Ina Sa'aden ta ina hada kishi da Aisha-Sultana?
Don haka Fulani ta rasa amsar da zata baiwa mijinta mai Askira, sai bin shi da ido, a zaton ta makuwa yayi cikin barcin sa. Amma da ya girgiza kafadun ta ya sake maimaitawa sai ta tabbatarwa kanta mai Askira yana nufin abinda yake fada ne.
"Kin amince ko Bilkisu? Hankalina bazai kara kwanciya ba batare da na tabbatar da sunnah tsakanin Sageer da Sa'adatu ba, jikina na bani itace zata zamo maganin dukkan matsalolin sa, don ban taba yin mafarkin da bai zama gaskiya ba".
Ya kwashe mafarkin da yayi duka yanzun nan ya fada mata.
Fulani Bilkisu ta rasa abinda zata ce, she's mute for some minutes, tana mai tariyo tarin alkhairin Sarki Yusufu ga Sa'ade tun zuwanta Askira, shin bazata manta da komi ba ta bisu da addu'a ta zama mai rama khairan da khairan?
Ta lumshe idon ta cikin na Askirama, wanda ke tabbatar masa da ta karbi alfarmar sa, bata da abin cewa. Itada Sa'adatu duka abin ikon sa ne sai abinda ya hukunta a gare su.
****
Chapter 16 · 0% Book details