Sashe 21
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 2 min read
gabansa ya fadi. Wani abu ne ya faru da ita? Ya tambaya in subdued (cikin karayar murya). Awaisu ya gyara kwalar rigarshi yana murmushi, ya ce, Ita wa ke nan? Ita Saadatun da ka ce kada in kira. Ya fada cikin daure fuska don ya kasa gane inda Awaisu ya dosa. Awaisu ya sake sakin murmushi, in dai wannan damuwar da ya gani kwance a kan fuskar Yarima a kan Saadatu ne, to insha Allahu komai zai zo wa Maimartaba da sauki, Yarima ba ya taba damuwa da lamarin wanda ba ya so, ko da kuwa ba so ne na soyayya ba, to akwai alamun shakuwa da aminci. Babu abin da ya faru da ita, tana dakin uwarta. You better call your wife not Saadatu, bana tunanin tunda ka zo ka kira ta. A hakan ake mana ikirarin duk duniya ba wadda ake so sai ita. Ita ma ko za ka kira ta, to fa sai gobe, in ka fito daga turakar Maimartaba Ya fada yana dariya, tare da kwashe wayoyin Yarima guda uku da ke bisa center table din gabansa, ya zuba a aljihun jamfarsa. Ya zabi daki daya cikin 3 bedrooms din da ke falon ya shige yana ce da Yarima, Lemme take a shower, ko na samu saukin gajiya ta. Yarima ya bi shi da kallo, ya kasa cewa komai, lamarin Awaisu sai shi. Sai ya dauki kan telephone ya yi dialling lambobin da yake bada umarnin a kawo masa abinci, ya yi wa Awaisu odar abin da zai ci. Daga haka ya maida hankalinsa kan macbook dinsa yana ci gaba da abin da ke gabansa. Sai dai kuma duk hankalinsa ya rabu biyu, jikinsa ya ba shi akwai muhimmin abin da ke faruwa a cikin gida da Awaisu ba ya son gaya masa, ya fi so ya ji kai tsaye daga bakin Maimartaba. Kuma da kyar in alamarin bai shafi Saadah ba, in ba haka ba don me Awaisu zai ce kada ya kira ta? Yana aiki yana ta tunane-tunane, duk a kan Saadatu da alamarinta da ya yi wa zuciyarsa karan tsaye, ya hana shi sukuni ya kuma hana shi enjoying komai da yake yi sabida rashin ganinta cikin kwanakin nan, sai dai ya kudire a ransa suna isa Askira da ya ga Maimartaba zai je har unguwar Fulani Bilkisu don kawai ya ga Saadatu.