← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 22

Sashe 12

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ya ce da ke wani abu bayn wannan?" "Wallahi iya abinda ya fada kawai kenan, sai cewa kema uwar sa ce har fiye da ni" Fulani ta yi murmushi ta ce "bakomai ki dinga dafa masan in har kina gida, kinsan turawa basu daukarwa kansu irin wannan wahalar, shikuma watakila yana marmarin abincin mace ne". Da wannan Sa'ade ta cigaba da dafawa Yarima Sageer abinci har tsayin kwana uku, wanda ya haifar da wata 'yar kwarya-kwaryar shakuwa a tsakanin su, duk da Yarima ba sakar mata fuska yake ba itama kuma hakan, amma yana nuna concern akan al'amarin karatun ta. Da tabbatar da ta ci abinci akan lokaci don in tasa kwamfuta a gaba mantawa take da cikin ta. Aisha Sultana bata san me suke ciki ba, ta dai lura yanzu tana bashi abincin ta tun tafiyar Uche, hakan kuma bai dadata da kasa ba don ta san ita bazata iya ba. Ga yarinyar da shegen zafin nama cikin 'yan mintuna ta sarrafa abinci mai wahala. Ko suna shiri a tsakanin su ko basa yi ita dai Sa'ade bata sani ba. Yau da Sultana ta dawo hatta firjin kicin sai da ta cika shi taf da kwalaben giya bana dakin ta kadai ba. Sabida za'a shiga weekend bazata samu zuwa bar ba ta san Yarima bai barin ta fita koina a karshen mako. Yarima ya fito falo misalin karfe na goma na safe yayi wanka yayi fresh da shi cikin kananan kaya DKNY ash colour, tsammani zakayi saurayi ne dan shekaru ashirin da biyar ba magidancin dake neman talatin da biyar ba. Maganar da maimartaba yayi masa a daren jiya a waya da ita ya wayi gari tana cin zuciyar sa, ya kuma yanke tunkarar Sultana da maganar. "Kai da matar ka sai yaushe zaku kawo min jika? Ko sai na mutu ban ga kwan ka a duniya ba? Aure shekara biyar ana neman ta shidda babu ko labarin bari a gidan ka Yarima? A matsayin ka na mai jiran gado?" Wannan magana ce da maimartaba bai taba yi masa ba sai wannan lokacin, don haka sai yaji tamkar an yi masa tuni ne akan abinda ya manta. Sultana ta fito sanye cikin wando 3 quater da yar karamar rigar shan iska armless ta nemi waje ta zauna a nesa da shi duk don ta nuna masa har yanzu fushi take. Ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a makogaro sakamakon kallon zara-zaran kafafun ta da suka sha adon jan farce purple abinda ya hanata sawa sabida ya gaya mata baya sallah amma ta ki daina shafawa. "Ki shirya mu tafi asibiti yanzu, a bincika a ga shin ni da ke waye baya haihuwa?" Ba karamin duka maganarsa ta yiwa Aisha -Sultana ba, amma bata bari fuskarta ta nuna ba. Mikewa yayi tareda daukar mukullin mota yayi waje yace yana jiran ta a mota. Ta bata lokaci kafin ta fito cikin shigar atampa hiterget, suka tafi zuwa Nizamiye Hospital inda suke da file. Da tana da yadda zata hana zuwa asibitinnan da ta yi, amma yadda ta ga fuskar Yarima ta san babu wani excuse da zai karba, fargabar dake ranta kadai ta isheta don bata taba zaton watarana Yarima zai taba sha'awar haihuwa ba. Ita kuma duk son da take masa bata shirya haihuwa da bakar fata ba, ta aure shi ne domin ya dinga satisfying soyayyar da take masa ba don su tara 'ya 'ya ba. A gaban sa likita ya duba ta, tayi fuska kamar bata san abinda ta aikata ba, ya kuma tabbatarwa Yarima Sageer babu mahaifa ma a jikin matar sa, an cire ta gabadaya. Yarima ya daga kai yana kallon Sultana wadda ta sunkuyar da kai, girar idon sa har wani irin tattarewa take yi sabida bacin rai, har suka zo gida bai iya ya ce mata komai ba. Suna shigowa gida kowa ya nufi dakin sa rai a bace. Har zai wuce daki yayi tozali da abincin da Sa'ade ta shirya masa akan dining, ya kuma jiyo kamar jan majina irin na kuka da sheshsheka daga dakin nata. Sai ya ji bazai iya wucewa ba tareda ya dubata ba, haka yau bacin rai bazai bar shi ya iya cin abincin ta ba. Knocking yayi mata har sau biyu, daga ciki ta amsa cikin dusashshiyar muryar data ci kuka. "Waye anan?" "Sunana Sagir" Murmushi tayi sabida yadda ya fadi sunan cikin lallashi? Ta taso ta bude kofar, tareda dan ja da baya don ta bashi damar shigowa. Cikin idanunta ya kalla, wadanda suka kada zuwa brown, "kukan me kike yi?" Akwai alamun hankalin sa ya tashi da ganin halin da take ciki, ai kamar jira take ya tambaya sai ta idasa rushewa da kuka. Da kyar Yarima ya samu tayi shiru, sannan ta rufe ido ta gaya masa ta fadi kwas din Physiology shine dalilin kukan ta. Ajiyar zuciya ta kwacewa Yarima, ya dauka wani abu ne terrible. Kai Sa'adatu 'yar maman ta. "Do you have issue with some of your courses baki taba gaya mun ba?" "Ai Fulani ce ta ce kada mu dinga hira" dariya ta kama shi sabida wautar ta data fito fili a yayin maganar. Ya tako zuwa gaban ta, gab da ita ya tsaya duk invictus ya mamaye ta. She can feels him breathing softly.... "gaya min abinda yasa Fulani ta ce kada mu dinga hira" gabadaya ta daburce ta kuma ga wautar kanta data fada masa hakan. Sannan bai bada space a tsakanin su wanda zata yi masa musu ba. Da sauri ta ja baya, amma sai taji bayan ta ya hadu da kofar dakin "umh...umh nima ban sani ba Uncle Sageer" "ni na sani, in kin amince in gaya miki....." da sauri Sa'ade ta girgiza kai "don Allah kada ka gaya min ni ba son sani nake ba" ta fada, her voice trembling. Kai gabadaya tsokar zuciyar ta ma rawa take sabida closeness din dake tsakanin su da kamshin Paco Rabbanne da yake hargitsa ta. A hankali ya ja da baya yana murmushi yace "ki ce ma Fulani, ai mutum baya cutar da abinda yake so ya zama nasa gabadaya. Ta bar ki kiyi hira da Yayanki. Fi-amanallah, har zuwa lokacin da zai dau ajiyar da ya bata". Bata gane zaurancen sa ba amma ta ce "toh" da sauri don ta samu ya bar ta haka, tayi jinyar sababbin abubuwan da ke ziyartar ta, a zuciya, ruhi da gangar jiki gabadaya. "Gobe zamu fara karatu ni da ke, physiology will never fail you again. Na bar ki lafiya". Har ya fita bata san meyasa ta kasa dauke ido akan sa ba, al'amuran sa na yau masu ban mamaki ne data kasa gane inda yasa gaba. A hankali tabi lafiyar gadon ta, ta lumshe ido tana tariyo maganganun Yarima Sageer daya bayan daya. In wani yace mata yana magana haka zata karyata. To me ya canza shi haka? Me ya kawo canjin? Sai dai kuma ga mamakin ta ta kasa kiran Fulani ta gaya mata abinda yace din duk da bata iya boye mata komai. Amma wannan karon sai ta ji ta kasa. Kamar tana jin kunya.... Kamar yadda barci ma ya gagare ta. Sai scenes din Uncle Yareema ke mata gifcin gizon makauniya. ****
Chapter 12 · 0% Book details