Sashe 15
Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
da bakin da zata bashi hakuri. Mika mata turarenta yayi yana dubanta ta kasan ido yace a hankali "idan matata taji kamshin turaren ki a jiki na what do you expect?" Sa'ade ta runtse ido tace "ni fa ban bayar da wata manufa ba, don ya kashe smell din aman ne" "idan kuma ni son smell din aman nake fa?" Kallon sa tayi da budaddun idanuwa.... mamakin ta ya bayyana karara cikin idanun ta Ba jimawa jirgin su yayi landing a Maiduguri. Motocin ASKIRA EMIRATE har guda biyar manya da kanana suka zo tafiya dasu, da fadawa da dogarai cikin uniform din su na bayin masarautar. Mota guda suka yi amfani amma da yake babba ce sosai kirar (4matic) mai kujeru takwas ba kujera daya suka zauna ba, Sa'ade na daga kujerar baya Yarima na owner side. Suka dauki hanya. Ji take kamar tayi fiffike ta ganta a dakin mahaifiyar ta. Har suka zo Askira barci take wanda a jirgi takuruwar zama kusa da Yarima bai barta ta yi ba. Ana bude musu motar ta fice da azama bata jira fitowar Yarima ba, wanda tun shigowar su Askira taga kamar komai nasa ya canza, simplicity din da annurin ya tafi, ya juye ya rikide ya zama cikakken Prince din sa. Da gudu ta karasa unguwar Fulani Bilkisu ko jakarta bata dauko ba sai biyota aka yi da ita. Da Zarah ta fara tozali, suka ruga da gudu suka makalkale juna. Zarah na tambayar me ta taho mata dashi daga Abuja? Tace "everything, sweetheart". Fulani ta fito daga shigifarta cikin wata irin kyakkyawar shiga ta alfarma, ta tsaya daga bakin kofa tana kallon su da murmushi, kamshin ta ne yasa Sa'ade ta lura da ita, ta ajiye Zarah ta kwasa da gudu ta rungume Fulani, kawai kuma sai ta fara hawaye. Fulani tace "yau nake ganin sakarci, me aka yi na kuka? Ko suna miki wani abu ne?" Ta girgiza kai "babu komai, kukan farin cikin sake ganin ki nake yi, watanni shidda ba kwana shidda ba". Fulani ta hau tureta daga jikin ta jin takun ana shigowa, Fanna ce ta taho dauke da abinci a makeken tray ta ajiye a dining. Tana murmushi tace da Fulani "Allah ya taimakeki yau tare na hada muku abinci da uwar daki na, don Allah ku ci tare" Sa'ade ta sa dariya cikin dadi tana kallon uwartata. Fulani ta gimtse fuska tace "Fanna yaushe na koma abokiyar wasan ki?" Fanna tayi nara-narai da ido tana murmushi tace "Allah ya ja da ranki Alfarma ce muke nema, wata shidda cif bamu ganki ba". Babu wanda ya gayawa Fanna Sa'ade 'yar Fulani ce ta cikin ta amma ta dade da fahimtar hakan. Yadda aka yi ta samu 'yar ne bata sani ba. Tana gama fadin hakan ta juya ta fita, Sa'ade tayi wata irin super ta dane jikin Fulani saura kadan ta kada ita, Zarah sai dariya take yi. A haka suka ci abincin cike da begen juna su uku. Tana gamawa tayi wanka ta sauya kayan jikin ta zuwa marasa nauyi ta dauko waya ta kira Sa'id. Yace "Sa'adatu, yaya kwana biyu kuma ya hutu? Ina fatan kina bitar Physiology textbook dinnan?" Sa'ade tace "ni yanzu ina garin mu bana Abuja ka kyale ni in huta da wani karatu, ina tare da uwata rabin raina" Sa'id yayi murmushi yace "sai na zo Askira kawo gaisuwar neman iri" Sa'ade tayi tsaki tace "Allah ya sawwake inyi saurayi da classmate dina, wani dan yaro da kai, ni dinnan da kake gani matar manya ce inji Fanna" dariya sosai Sa'id yayi, ya ce "me yafi ka auri yaro sabon jini kamar ka? Ya sa ka dariya kaima ka saka shi? In yaga dama ya goyaki ya yi ta zagaye gida dake?" Sai ganin Fulani tayi tsaye a kanta. Ba karamin firgita tayi ba ganin expression na fuskarta. Tayi maza ta kashe wayar ba tareda ta yiwa Sa'idu sallama ba. Tana zazzare ido na rashin gaskiya. "Keda wa kike waya?" Fulani ta tambaya fuskarta babu annuri. A tsorace tace "dan ajin mu ne kawai" Fulani ta juya bata ce komai ba. Saidai kwarai ta so ta magantu din, but she don't want to be too strict har Sa'ade ta koyi boye mata sirrikan ta. Saida ta kai bakin kofa sannan tace mata ta tafi wajen Askirama kada ta nemeta..... ****