← Book details Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Masarautar Mu Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

 MASARAUTAR MU!

2

Littafin

SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]

SADAUKARWA
Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi.

JINJINA
Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration.

GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali.

MASARAUTAR MU 2
Ya kara tattaro dan sauran karfin gwiwar da ya rage masa, yace cikin kwantar da murya, kodayake kodayaushe muryarsa a kwance take.
"Baturiyar Asia ce, Jew (bayahudiya), ta yarda zata karbi addinin muslunci in dai zan aure ta".
Daga sarki har Ya Gumsu a razane suka dube shi. Mai martaba ya kasa cewa komai kamar an dinke masa baki. Ya mutu a zaune cikin kujerar sa. Ya Gumsu ta mike tsaye tana nuna shi da dan yatsa "....ka yi kadan Yarima, karya kake ka tozarta ni a idon duniya da idon kishiyoyi na masu son ganin faduwa ta!. Ko mata sun kare ban yarje maka auren nan ba, da yawun baki na bazan taba saka albarka ta ba!!!".
Sarki Yusufu ya ce "kana iya tafiya Yareema zamu yi shawara, duk abinda muka yanke Waziri zai kira ka". Ya Gumsu ta zaro ido tana kallon Mai Askira tamkar idanun ta zasu fado. Tunda har ya amince zai tattauna zancen nan da Waziri ta san karshen alewa kasa.....ba ya kai zance ga Waziri sai ya fara yin na'am da shi a karan - kansa. Ta fashe da kuka ta tashi ta bar falon. Yarima ya mike zai bi bayan ta. Sarki ya ce ya kyaleta sai ta huce yanzu bazata taba sauraron sa ba.
Ya koma ya zauna jikin sa a sanyaye, da wannan damar Sarki Yusufu yayi amfani ya dinga tambayarsa abubuwa akan Rose din, da yadda suka hadu, shi kuma ya gaya masa duk abinda ya kamata ya sani banda wanda bai kamata ba. Ya kare zancen sa da cewa yana mata kwadayin musulunci ta hannun sa don jihadi, sabida kyawawan halayen ta, sannan ita din ma tana sha'awar addinin muslunci a karan - kanta. Ta zabi ta bar kowa nata in dai za'a bar shi ya aure ta.
Alanguburo ya fahimce shi sabida saukin kansa, a lokaci guda yana kokawar ture nasa BURIN akan Yarima Sageer can gefe daga zuciyar sa, yana fadawa zuciyar sa ya bar shi yayi jihadin; wani ya shiryu ta hannun ka yafi a baka jajayen Rakuma tunda Allah bai haramta ba. Ba duk abinda muka yi burin tabbatuwar sa ne yake tabbata ba. Wasu mafarkan a mafarkai kawai suke tsayawa, ba sa zama REALITY yadda muke burin su. Wasu kuma Allah kan jinkirtawa bawa zuwa lokaci mafi dacewa. Ya sallame shi da cewa ya saurari kiran Waziri idan sun tattauna gobe.
****
Sarki Yusufu da Wazirin sa Ibrahim suna tattaunawa akan al'amarin Yarima bayan sun kadaice a falon ganawar sirrin su, Waziri yace su bar Yarima yayi auren su samu ladan muslunci, amma bisa sharuddan cewa zata biyo shi gida su zauna tare dasu cikin MASARAUTA a matsayin sa na Yarima mai jiran gado. Dole ya dawo gida gabadaya ya zauna cikin ahalin sa.
Lokacin da Waziri ya kira Yarima ya gaya masa hukuncin da suka yanke, Yarima Sageer yayi dan jim! Domin nan kusa bai shirya dawowa gida ba, ba zai iya rayuwar karamin gari kamar Askira ba, zai takura, ba zai shana yadda ya saba ba, sannan Rose ma zata takura, ga zafin Maiduguri, bata taba zuwa Africa ba haifaffiyar South - Korea ce. Aiki ya kai iyayenta Amsterdam. Ba abinda ya tsana irin ace shine 'mai jiran gado', bayan ba shikadai ne namiji ba, shi sarauta sam bata cikin tsarin sa, Yarima Sageer bakin bature ne kawai wanda ya rungumi affluent western lifestyle ya manta da asalin sa tsayin shekaru masu yawa, wannan kuma ya faru ne da laifin su iyayen sa da suke ganin yin nisa da gida fintinkau shine abinda zai nutsar musu da shi; don nutsuwa ya nutsu irin wanda tarin shekaru ke haifarwa da namiji, amma ba nutsuwa irin wadda su suke zato ba.
Karewa ma, ya goge ne yayi mastering akan harkar neman mata, har wadanda ba addinin su daya ba. Amma in ka gan shi a fuska tsammani zakayi wani saint ne shi din (waliyyi) sabida tsabar iya badda-kama a gaban iyaye. Abu daya Allah ya tserar da Yarima akan sa shine shan giya, ko sha'awar ta bai taba yi ba. Yana matukar kyamar ta. A cewar sa ai sai da hankali ake sallah dai-dai, kuma a yi ta akan lokaci. Hatta sigari tun lokacin tashen samartakar sa ya bar ta.
Amma da ya duba wannan alfarma da iyayen sa suka yi masa wadda bai taba zaton zata zo masa da sauki haka ba, sun bar shi ya auri zabin sa dai-dai da ra'ayin sa, sannan sun toshe kunnuwan su daga duk abinda zasu ji akan auren nasa, auren da a tarihin masarautar su ba'a taba yin irin sa ba, sai ya ga cewa ya zama dole shima ya amince da tasu bukatar na dawowa Askira tare da matar sa. Kafin nan zai roke su su bashi lokaci, ya kammala phd din sa, ya tattaro kasuwancin sa zuwa Nigeria ya kuma nemi aikin da zai rike shi in ya dawo, ba zai zo ya dogara da mahaifin sa ba kamar yadda akasarin 'ya'yan sarauta ke yi.
Koda ya yiwa Waziri wannan bayanin take ya amince, ya kuma ce sun bashi shekaru biyu ya kammala komai, ya dawo tare da matar a musuluntar da ita a daura auren su. Awaisu was shocked lokacin da yaji labarin nan domin bai taba zaton iyayen su zasu amince da zancen Rose ba, haka bai taba zaton Yarima is serious akan maganar Rose ba, ya dauka yana fada ne kawai for fun irin nasa. Shikam tuni Ba'ana ta zaba masa mata 'yar kanwar ta mai suna Asiya suna dawowa za'a hada auren nasu lokaci guda shi da Yarima, don yarinyar bata kare sakandire ba ma.
Kwanan su bakwai suka koma Amsterdam with nostalgia (cike da begen gida) a yadda suka tsammaci masarautar ta su sai suka tarar akwai cigaba na zamani sosai fiye da yadda suka tafi suka bar ta. Suka kuma fara tunanin hanyoyin da zasu kara kawo mata daukaka da cigaba na zamani ta kara zama zakaran gwajin dafi a masarautun jihar Borno tsararrakin ta. Tuni Yarima ya tsara sababbin gine-gine da za'a kara cikin masarautar, da yadda za'ayi renovating din ta daga kamfanin gine-gine da tsare-tsaren gidaje na COSIMCO na kasar Amsterdam (Neitherlands).
Yana komawa abinda ya maida hankali akai kenan, wato project da cosimco akan masarautar su. Daga can suka taho suka fara ayyukan su a masarautar Askira. Gininnika na zamani masu tsayi da nagarta suka kara fiddo da martabar masarautar Askira. "Lallai dan zaki an girma" Sarki ya fadawa Waziri cikin murmushi a lokacin da suke zagaye cikin masarautar da wajen ta, suna kallon renovation din da Yarima ya tsara da kansa ya kuma turo COSIMCO construction company suka yi. Waziri da sauran 'king-makers' sai albarka suke sanyawa Yarima, fatan su bada jimawa ba ya dawo ya karbi sarautar mahaifin sa tun yana raye. Wanda basu sani ba wannan baya cikin tsarin Yarima Sageer ko kadan. Bar shi dai a gogaggen dan bokon sa. Awaisu ne kawai ya san hakan.
****

Hutun su Sa'ade na karewa suka koma makaranta, ashe wani abin alhini ke can yana jiran ta, shiru-shiru tana zuba idon ganin dawowar Raheema amma har ta share sati biyu da komawa Raheema bata dawo ba.
Sa'ade ta kasa sukuni, ta kasa walwala ta kuma kasa cigaba da harkokin karatun ta yadda ta saba a dalilin babu Rahima, ta kuma rasa wanda zata tambaya ko ya san abinda ya hana Rahima dowowa don kowa ita yake tambaya. Ga wani kuskure data yi bata taba karbar adireshin Raheema ba, sabida tana ganin ko ta karba babu wanda zai kaita, Fulani bazata taba barin ta ta je ba.
Da abin ya isheta sai ta tafi ofishin principal, tayi gaisuwa ga principal sannan ta soma share hawaye. Principal tace "what's wrong Sa'adatu Hashim?" Sa'ade ta idasa fashewa da kuka a gabanta sannan ta gaya mata yau sati uku kenan Raheema Kyari bata dawo ba.
Principal tasa aka yi bincike akan rashin dawowar Raheema, nan malamin dake kula da dawowar dalibai ya sanar da ita sakon da mahaifin Raheema ya aiko na cewa sun bar kasar Najeriya. Wanda ke nufin Raheema ta bar makarantar gabadaya.
Damuwar Sa'ade sai ta nunku akan ta da, me ya sa Raheema za ta bar kasar ba tare da ta yi mata sallama ba? Laifin me ta yi mata? Amincin dake tsakanin su ya fi gaban haka. Bata san ta yi mugun shaquwa da Raheema ba sai yau data wayi gari babu ita cikin kwalejin El-Kanemi. Rayuwar Sa'ade gabadaya sai ta sauya a makaranta ta zama ba umh ba umh-umh. Haka ta dukufa yi wa Raheema addu'a ba dare ba rana kan Allah yasa tana lafiya, tana kuma rokon Allah ya sake hada su cikin gaggawa.
Sannan a fannin karatu ta kara dagewa, don yanzun shi kadai ne abinda ke debe mata kewa. Tana yawan tunanin Zarah da Fulani, amma kullum tana sawa a ranta Fulani bata son ta don haka is a waste of time yawan tunanin ta data ke yi, har addu'a take yi a kowacce sallahr farillarta Allah ya rage mata son da ta ke yi wa mahaifiyar ta Fulani Bilkisu!
****
Chapter 1 · 0% Book details