← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba kam cikin farin cikin ganin ta ya kwashe komai ya fad'a mata.

Maimakon ta yi bak'in ciki sai ta yi farin ciki ta ce.

" Toh ai shi ke nan, amma gaskiya sai dai su d'auketa aiki su ringa biyan ta duk wata, dan ba a aiki banza a kano".

Jamil ne ya ce.

" Ba matsala kud'i ba matsalar mu ba ce, za mu biya ta in sha Allahu".

Dariya kawai take yi dan ita kad'ai ta san tuggun da ta had'a.

Baba ne ya ce.

" Toh madallah, saura maganar wayar da ya bata".

Murmushi ta yi ta ce.

" Allah sarki ni kuma mai nene had'i na da wayar ta?".

Kallonta Lami ta yi ta ce.

" Laraba ki ji tsoron Allah ke kika karb'e wayar fa, a gabana kika karba".

Kukan munafurci ta saka ta ce.

" Yanzu malam a gaban ka a ke min wannan cin mutuncin amma baza ka ce komai ba".

B'ata fuska baba ya yi ya ce.

" Ya isa haka, idan ma ta karb'e ai ta isa ne, kar na sake jin maganar waya a gidan nan, tun da yanzu za ku tattara ku tafi da Amanah".

Sunkuyar da kai mama lami ta yi ta ce.

" Allah ya baka hak'uri malam in sha Allahu hakan bazata sake faruwa ba".

Laraba ta shi ta yi ta fita.

Ita ma lami fita ta yi, cikin rashin sa'a lami ta rutsa laraba cikin d'akin ta, ihu ta saka ta ce.

" B'arawo!!".

Da gudu Jamil ya fito ya sun kuci tab'arya, d'akin ya shiga, bai yi wata wata ba ya zabgawa laraba a kafad'arta.

Ihu ta saki ta ce.

" Ni ce fa, laraba ce, wayyo Allah na".

Amanah kam ta ga shigar laraba d'akin tun farko, ai kam mai za ta yi banda dariya.

Lami ma dariya ta ringa yi.

Jamil kam ya na Sani ya zabga mata domin ya ga fuskarta.

Baba ne ya hau kiran lami domin jin abinda ke faruwa.

Da taimako Jamila laraba ta samu ta shiga d'akin ta, sai kuka take.

Baba kam koda a ka fad'a masa abinda ya faru fad'a ya hau yi sosai, ya ce.

" Jamilu d'auki khadeejah ku tafi, idan har ka cutar da ita ban yafe maka ba".

Kallon sa Amanah ta yi dan neman k'arin bayani.

Lami ce ta yi mata bayanin komai.

Ita ma ta yi farin ciki da jin za ta je ta yi rayuwa da Ahyan, domin tun da suka dawo gida ya na cikin ranta.

Affah

Ji ya yi duk duniya ba Wanda ya tsana kamar Ahyan

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)

PAID BOOK NE ZA KI BIYA 400 ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WHATSAPP.

KINA YIN SANA'AH AMMA BA KI DA ABOKAN KASUWNCI. TOH GA DAMA TA SAMU DOMIN DA KUDI KADAN ZAN TALLATA MIKI HAJAR KI KUMA DA YARDAR ALLAH ZA KI SAMU ABOKAN CINIKI. IDAN KINA BUKATA KI YI MIN MAGANA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

TALLAH TALLAH TALLAH 💃💃💃💃

MUNA SIYAR DA DATA MAI INGANCI DUK MAI SO YA YI MIN MAGANA DOMIN SIYA

08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU 🧕)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE1️⃣2️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

BAWO

Maganin da Boka ya bata ta ke barbad'awa a k'ofar d'akin Zulai domin Affah ya kore ta.

Affah kam duk abinda ta ke yi ya na kallon ta ta CCTV CAMERA, kallon ikon Allah ka wai ya ke.

Zulai kam ta kasa shiga d'akin ta ne sabida jira ta ke yaran ta su dawo, daga makaranta,waya ta d'auka ta tura wa babban yaron ta sak'o.

Junaid idan an ta shi su Adnan daga makaranta ka je ka d'auko su, na ji su shiru, kuma lokacin ta shi ya yi.

Momma ta na zaune ta na kallon Ahyan da ya ke ta kuka ya dafe kansa sai kiran Ahmanah ya ke.

Bud'e k'ofar parlorn a ka yi.

Da sauri momma ta juya ji ta ke Jamil ne.

Junaid ne ya shigo parlorn ya na rik'e da Jawad.

Kallon k'yama momma ta yi musu ta ce.

" Junaid ku fitar min daga gida".

Murmushi Jawad ya yi ya ce.

" Haba mommancy ya za ki ce haka?, ni dai kin san ba ni da in da ya fi nan ko?".

Tsaki ta ja ta ce.

" Kai dallah rufe min baki, shashasha mara tunani, yanzu duk jan kunnen da na yi maka ba ka dai na shaye shayen da ka ke ba ko?".

Dafe kansa ya yi ya ce.

" Dan Allah ki daina wannan zan ce, yanzu dai k'arar Junaid na kawo miki, ya je ya yi lalata da budurwa ta".

Dafe k'irji momma ta yi ta ce.

" Na shiga uku!!!, ni Maryam yanzu abin na ku har ya kai ku ringa hakke wa yaran mutane?, wai dan Allah mai ya ke damun ku ne".

Ahyan kam mik'ewa ya yi da gudu ya nufi k'ofa, momma ba ta kula ba sai jin muryar Jamil ta yi ya na cewa.

" What is this?".

Amanah kam ta san k'ame domin abin ya zo mata a bazata.

Momma ce ta ce.

" Adamu cika ta mana".

K'in sakin ta ya yi sai dariya ya ke, Amanah ce ta ce.

" Toh cika ni na zauna mu yi wasa".

Kamar wanda ya ke jira haka ya ci ka ta.

Jamil kam sakin baki ya yi ya na kallon ikon Allah.

Junaid ne ya ce.

" Momma mai ya samu Yaya haka?, naga ya dawo kamar wani yaro".

Tsaki ta yi ta ce.

" Ku da kuke sab'on ubangiji in da ma ku Allah ya d'orawa abinda ya d'orawa Adamu, domin shi yaron kirki ne, amma nasan jarabawar rayuwa ce, Allah ya ba shi ikon cinye ta".

Jawad kam tun da Amanah ta yi magana ta tafi da imaninsa, gaskiya ta yi masa, wannan ita ce irin matar da ya ke mafarkin aure.

Momma ce ta ce.

" Khadeejah sannu da zuwa, ya jikin abban naki?".

Murmushi ta yi ta ce.

" Alhamdulillahi momma ya jikin Ya Ahyan?".

Murmushin ta mayar mata ta ce.

" Jiki alhamdulillahi ga shi nan sai kiran ki ya ke".

Dariya ta d'an yi ta ce.

" Tohm ga ni Ai".

Jawad ne ya mik'a mata hannu ya ce.

" My name is Jawad, you can call me Jay".

Ba tare da ta mik'a masa na ta hannun ba ta ce.

" Masha Allahu, ni kuma Amanah".

Cikin son ya ga ya burge ta ya ce.

" Wow nice name, nice to meet you".

Ita kam haka kawai ta ji bai yi mata ba Sam.

Momma ce ta kalli Jamil ta ce.

" Zo zauna yaron kirki, dan Allah ka ringa yi wa way'annan shashashan fad'a, wai Jawad ne ya kawo min k'arar junaid, wai ya yi lalata da budurwarsa, kai banda zamanin ya kai zamani mai zai had'a yaran nan da matan banza".

Jawad kam bai tab'a jin kunyar da ya ji yau ba, dan sai ya ji dama bai tab'a aikata sab'o ba.

Amanah kam jikin ta ya yi mugun sanyi da jin halayyar su Jawad duk da yau ne had'uwar su ta farko, amma ji ta yi ta tsane su.

Shiru Jamil ya yi can kuma ya ce.

" Allah ya shiryar da su idan masu shiryuwa ne".

Amanah kam zama ta yi, Ahyan ma zama ya yi a kusa da ita, har cinyarsa na gogar ta ta, da sauri ta d'an matsa gefe.

Idon Jamil na kan su, duk abinda ke faruwa a kan Idon sa ne.

Momma kam masifa ta ringa zazzagawa su Jawad.

BAYAN KWANA BIYU

Laraba sai jinya ta ke, domin ta samu gocewar k'ashi a hannunka.

Lami kam ta yi kewar Amanah sosai, waya ta gani a cikin kayanta, lokacin da ta na gyaran kayan, da har za ta nunawa baba amma ta fasa.

Baba ma ya yi kewar ta domin duk cikin yaran nasa ita kad'aice ta ke girmama shi.

Jummai kuwa sun yi fad'a da Jawad sabida ya farka ya ganta ita da junaid suna cin amanar sa.

Laraba tun da ta yi wa junaid text bai dawo mata da amsa ba ga shi ba baki ne da ita ba, bare ta yi wa Affah bayanin su Adnan basu dawo gida ba, tun shekaran jiya.

Bawo kam sai bak'in ciki ta ke domin Laraba ba ta taka Maganin ba, har lokaci ya wuce.

Affah gaba d'aya tunanin kowa ya goge a kansa, sai na Bawo kawai, ya na son tuna wani abu amma ya kasa.

Sosai Amanah take kula da Ahyan har sun Saba sosai, momma kam ba k'aramin dad'i take ji ba, yadda Amanah ke kula da Ahyan ya na yi mata dad'i sosai.

Jamil kam ya mayar da hankali da tunaninsa kan Amanah, duk wani motsin ta a kan Idon sa ya ke.

Jawad ma ya dai na fita ko ina domin so ya ke ya samu kusanci da Amanah, domin in dai za ta yarda zai bar duk wasu mugayen d'abi'unsa ya aure ta.

Ita kam duk basa basa gaban ta, kula da Ahyan kawai take yi.

Zulai sak'o ta tura wa Affah ta WhatsApp kamar haka.

" Affah dan Allah ka taimaka ka taya ni neman su Adnan tun shekaran jiya basu dawo gida ba".

Shiru ba amsa har wani lokaci.

Bawo kam ta dage da aiki da magani domin ta na ganin amfanin hakan.

Suna zaune ta na bashi madara a baki, ya kalleta ya ce.

" Amanah, za ki goya ni?".

Dariya ta yi ta ce.

" Ai ba zan iya goya ka ba, ka yi min girma".

Dai na shan madarar ya yi ya b'ata rai.

Murmishi ta yi ta ce.

" Tohm shikenan sha zan goya ka".

Dariya ya hau yi ya ce.

" Yeeee za a goya ni".
Chapter 9 · 0% Book details