← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ta shiga gida domin yin sallah, dan yau ta makara, sakamakon wanda ya ke jire mata kayan siyar war bai zo da wuri ba, d'akin ta ta shiga da niyyar shiga toilet, amma wata bushshiyar mata ta kira ta da.

" Ke Amanah uban mai ya dawo da ke?".

Jikin ta ne ya fara rawa, cikin girmamawa ta ce.

" Mama sallah na dawo yi".

Kallon banza ta yi mata ta ce.

" Sannu sallau, wato sallah ki ka dawo yi ko?, toh dan uban ki wu ce ki koma, salon wani ya kwashe min kud'in ko?".

Rok'on ta ta hau yi akan ta barta ta yi sallah sai ta koma amma fir mama ta k'i yarda.

Ju yawa ta yi za ta fita daga d'akin, sai ta ja ta tsaya ganin Mama Lami, za ta shigo d'akin.

MAMA LAMI

Kallon Mama ta yi ta ce.

" Wai dan Allah Laraba ke wacce irin mata ce?, kin hana yarinya sakat a gidan uban ta, ke kin tura yaran ki makaranta ita kuma kin d'ora mata tallah, yanzu abin da ki ke yi daidai ne?, ke ma fa uwa ce (My next book in sha Allahu) kuma ki na da yara ba kya tunanin ki mutu ki barsu a hannun wata, ta yi musu irin yadda ki ke yi wa Amanah, ko kuma ki na da tabbacin baza su zauna da KISHIYOYIN UWAH ba? ".

Kallon up and down ta yi wa mama Lami ta ce.

" Lami ki fita daga idona na rufe, ke har yaushe ki ka samu y'ancin yin magana a gaba na?, ko dan kinga kwana biyu ina d'aga miki k'afa shi ne ki ka raina ni, toh idan bacci ki ke ki farka, kin sanni na san ki".

Dariya Mama Lami ta yi ta ce.

" Ai da ne na ke tsoron ki amma banda yanzu, domin yanzu na rik'e Allah shi ne madogara ta, ke kam har yanzu ki na hanyar b'ata".

Rass Laraba ta ji gaban ta ya fad'i, shi ya sa idan ta je wurin Boka sai ya ce ba ya iya ganin Lami, lallai ne dole ta nemo wata hanyar.

AMANAH

Ganin suna ta cece ku ce ta shiga toilet ta d'auro alwala, fita ta yi ta shiga d'akin mama Lami ta yi sallah, ko Addu'oin da ta saba yi ba ta tsaya yi ba ta fita wurin sana'ar ta.

Su kam sun dad'e suna fad'a kafin daga baya Lami ta bar mata d'akin.

Wayar sa ya ciro daga aljihun wandon sa, text message ya shiga ya duba sak'on da Affah ya turo masa, kamar haka.

" My Ahyan ya kake, ya momma ina su Jawad da Mus'ab fatan ka sa me su lafiya,

Magana na ke son yi da kai, gobe ka zo gida mu yi magana,

Adam Abdullahi Affah".

Murmushin gefen baki ya yi ya tura masa da amsa.

" Da fatan Affah na ya na cikin k'oshin lafiya, su momma duk suna lafiya, amma Affah kasan ba na iya yin magana, kuma idan na zo gidan Anty za ta ganni, kar a samu matsala idan ba damuwa mu yi magana ko ta WhatsApp ne,

Adam Abdullahi Adam".

Momma kam ba tasan Ahyan ba ya magana ba, ta yi zaton halin nasa ne ya motsa na rashin son yin magana, dan shi mutum ne wanda bai fi ya yin magana ba.

Jawad wanda da shi su ke shiri ne ya kalli Ahyan ya ce.

" Bro wai mai ke damunka ne?, naga tun da kazo ko momma ba ka yi wa magana ba, lafiya dai ko?".

Kai kawai ya d'aga masa, ba ce ko mai ba.

Kuka sosai Amanah ta ke a gaban mahaifin ta, sai ratsuwa ta ke yi akan ba abin da ya had'a ta Laraba amma ya k'i yarda bulala ya d'auko ya hau dukan ta, jin abin ba na k'are ba ne yasa mama Lami fitowa daga d'akin ta, tana zuwa ta kamo Amanah ai kam ba zato kawai sai ta ji ya had'a da ita ya na dukan su.

AKWAI BOOK DIN SAJJAD DA NA RUBUTA IN DA MAI SON SIYA SHI MA DAI KAMAR WANAN 400 NE BA TSADA

ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WHATSAPP

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DAoXdILRZKjC042FBN7HEK?mode=r_c Kina neman inda zaki samu kaya masu sauqi da quality taho nan mamana kayanmu sunada kyau ga sauki farashin sarine muna aika kayan mu ko ina in sha Allah

https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

PAID BOOK NE MAI BUKATA ZA TA BIYA 400

ACCOUNT 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WHATSAPP

INA WACCE TA KE SON ABOKAN CINIKI TOH GA DAMA TA SAMU DOMIN DA KUDI KADAN ZAN TALLATA MIKI HAJAR KI KI SAMI COSTORMER KE DAI KI YI MIN MAGANA TA NUMBER NA👇👇

08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

TALLAH TALLAH TALLAH 💃💃💃💃

KO KUN SA MU NA DATA MAI INGANCI

DATAR MTN 1 GB 900 30DAYS

AIRTEL 1 GB 900 30DAYS

GLO 1 GB 900 30DAYS

SAUKI NA ALLAH RANGWAMI NA MA'AIKI.

GA ARAHA GA LASTING

KU NEME NI A NUMBER TA

08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

NA GODE

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU❤️)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE 4️⃣

Laraba sai dariya ta ke, dan abin ya yi mata dad'i.

wata budurwa ce wacce ba za ta wuce sa'ar Amanah ba ta ce.

" Baba dan Allah ka dai na dukan ta wallahi ba abin da ta yi wa Mama shirri ne kawai".

Cak ya tsaya da dukan da ya ke wa Amanah da mama Lami, yarinyar ya kalla ya ce.

" Ke Zubaidah kin san ba na son k'arya koh?".

Da sauri ta je in da ya ke ta ce.

" Na rantse ba abin da ta yi wa mama, ka tambayi Lami".

Kallon Lami da ke gogewa Amanah hawaye ya yi ya ce.

" Lami mai ya faru?".

B'ata rai ta yi ta ce.

" Kullum idan ka ta shi yanke hukunci ba ka yin bincike, duk abin da ta fad'a maka sai ka hau kai ka zauna".

" Kinga tambayar ki na yi ba cewa na yi ki min zan cen banza ba".

Jan hannun Amanah ta yi su ka bar wajen.

Kallon Baba Laraba ta yi ta ce.

" Lallai ma, wallahi raini ya shiga tsakanina da kai, tun da har zan fad'a ma ka abu ka zauna ka na kokwanto".

Jikin Baba ne ya hau rawa ya ce.

" Ki ya hak'uri dan girman Allah ai dai a gaban ki na daketa ko?".

Tsaki ta ja ta bar wajen, dan ya b'ata mata rai.

Kamar dai Kullum yau ma suna zaune su hud'u, Momma ce ta kalli Ahyan ta ce.

" Adamu wai salon salawaitun iskanci ne ya sa tun da ka zo ba ka yi min magana ba, ko kuma uban naka ne ya hana ka yi min magana?".

Had'e fuska ya yi, bai yi magana ba.

Jamil kam dariya ya hau yi ya ce.

" Maganinki ke nan y'ar tsohuwa, ga shi nan jikan ki ya na yi miki wulak'anci, ko da ya ke ke ki ka jawowa kanki, tun da duk cikin mu kin fi nuna masa kulawa, idan an yi magana ki ce shi abin tausayi ne".

Carbin hannunta ta zabga masa a kafad'arsa, ai kam ba shiri ya ta shi daga kusa da ita, ya koma kusa da jawad.

Jawad kam dariya ya ke sosai, dan shi ya sa ma ba ya nuna k'iyayyar Ahyan a fili, amma gani ya ke duk duniya ba wanda ya tsana kamar Ahyan.

Shi kam bai ma san suna yi ba dan chat su ke da Affah, in da Affah ya ke fad'a masa zai yi aure, shi dai goyon baya ya bawa Affah dan Zulaihat ba matar aure ba ce.

(Ni kam na ce baka San wacece Bawo ba ne shi yasa amma Oum Ahmad za ta baka labarin ta😢😂)

Ita dai momma Allah ya gani ta na mugun son Ahyan domin ko Nonon uwarsa bai sha ba, wannan dalilin ya sa ta ke son sa da tausayinsa.

Bawo

Dad'i ta ke ji Affah ya amince zai aure ta, sai shiri ta ke duk da aure kawai za a d'aura ta tare a d'akinta, amma sai d'oki ta ke.

Zulaihat

Ba k'aramar k'iyayyar ta ke yi wa Bawo ba, domin ta ci amanar ta, ba ta tab'a zaton Bawo za ta yi mata haka ba.

Affah

Ya fita daga sabgar Zulaihat tun daga ranar da ya ji irin k'udurinta a kansa da Ahyan,ita kam duk a tunanin ta asiri Bawo ta yi, ta juyar da hankalinsa kanta.

ONE WEEK LATER

KANO

JA'IN

Laraba

shige da fice ta ke sosai ta rasa yadda za ta yi da Lami domin duk wurin Bokan da ta je, sai dai ya ce mata wani haske ya lullub'e Lami ba ya iya ganin ta, kuma duk aljanin da ya rab'eta k'onewa ya ke.

Lami

Sosai ta dage da karanta addu'ar da ta ji wani malami ya fad'a cewa in dai ka karanta ta sau uku da safe sau uku da yamma toh aljani ko ya rab'e ka sai ya k'one.

( GA ADDU'AR👇👇

AMANTU BILLAHI WAHADA WAKAFARTU BIL'JIBTI WAD'D'AGUT WA AKASAMTU'BIL KURBATUL'WUSD'A LAMFISSA'AH LAHA WALLAHU SAMI'UL ALEEM HASBIYALLAHA WAKAFA WASAMI'ALLAHU LIMAN D'A'AH WALLAISA WARA ALLAHUL MUNTAHA)

Haka ta dage da koya wa Amanah domin ita ma ta ringa yi.

Baba kam ya rasa mai ke masa dad'i, domin tun da ya daki Amanah ya ke jinsa wani iri, gani ya ke kamar bai kyauta ba, amma idan ya tu na Laraba sai ya ji ko mai normal.

Mommah

Tashin hankali ta shiga jin Affah zai k'ara aure, amma da ta tuna dalilin da ya sa zai yi auren sai ta ji dad'i, a wani b'angaren kuma ta na tausayawa rayuwar Ahyan domin ya na ganin jarrabawa.

JAWAD
Chapter 2 · 0% Book details