← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ni nasan abinda ya ke so, wata yarinya ce, kuma Jawad ma ita yake so".

Da sauri momma tace.

" Khadeeja ce ko?".

A tak'aice ya bata labarin duk cutar da Jamil yake yi akan Amanah.

Sosai momma ta jijjiga da jin zancen, domin ita Ahyan take wa sha'awar auren khadeejah ba Jamil ba, amma tun da abin ya zo a haka dole ne ta hak'ura Jamil ya aure ta, shi kuma JAWAD Allah ya ba shi wata mafi alheri.

FEW DAY LETER

Cikin masifa da bala'i JUMMAI ta kalli mijin ta ta ce.

" Na rantse da Allah yau sai ka sake ni, na gaji da zama da mazinaci, tsabar rashin tsoron Allah irin naka har cikin gidan auren ka zaka ringa kawo matan banza".

Dariya ya yi ya ce.

" JUMMAI kenan, tun da kike kin tab'a ganin karuwa ta auri malami, ko mutumin kirki?, ai auren y'ar iska irin ki sai ni d'an iska, idan ma za ki cire zan cen saki ki cire dan wallahi ba abinda zai sa na sake ki".

Kuka tasa tace.

" Shikenan tun da ka ce haka amma wallahi ka sani ni ma neman mazan zan fita, kai in ta kama har gidan nan zan ringa kawo su, tun da abin iskanci ne".

Tsaki ya yi ya bar wajen dan ko a jikin sa.

NA KUSA GAMA FREE PAGE'S DUK MAI BUKATAR KARANTAWA YA BIYA 400 IDAN BA HAKA BA IN NA GAMA RUBUTAWA ZAI KOMA 500

GA ACCOUNT 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU♥️)

PAID BOOK 📚 NE KI BIYA 400 DOMIN MALLAKAR NA KI GA ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

MUNA TALLATA HAJA GA WANDA TAKE SON A TALLATA MATA SAI TA YI MAGANA TA NUMBER TA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕 KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)

BOOK 1️⃣

🆓 PAGE 2️⃣1️⃣

NA KUSA GAMA FREE PAGE'S DUK MAI SON KARANTAWA TA BIYA 400 IDAN YA ZAMA COMPLETE ZAN MAYAR DA SHI 500

GA ACCOUNT 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Suran matan ne suka kalleta suka shek'e da dariya, uwar gidan ce ta yi magana.

" Idan ma za ki cirewa kanki damuwa ki cire, domin in dai alhaji ne ba kunyar jibgar ki zai ji ba, kuma wallahi fitar nan da ya yi in ba Allah ne ya kiyaye ba karuwai zai d'ebo su yi miki mugun duka".

D'ayar ce ta ce.

" Hmm rabu da ita yaya, ai zai koya ma ta hankali, yarinya ki saki jiki ki ci arziki, dan Alhaji ba shi da d'an hannu ko mai kike buk'ata zai yi miki, amma ki ajjiiye fitsara da rashin kunya a gefe".

Tsaki ta ja ta bar wajen.

Su kam ko a jikin su, dan sun saba zama da irin ta, kasancewar mijin su auri saki ne da shi, wai neman haihuwa ya ke a hakan.

BABA

" Laraba kina ina ne?".

Shiru ba amsa, jin ba ta amsa ba ya sa shi kiran Lami.

Tun bai rufe baki ba Lami ta k'arasa in da ya ke, cikin girmamawa ta ce.

" Malam gani".

Kallon ta ya yi rai a b'ace ya ce.

" Ina Laraba?".

Murmushi ta yi tace.

" Ta fita".

Kallon ta ya yi ya ga tana murmushi, ai kam ya hau ta da fad'a.

" Wato ga mahaukaci yana magana ko, shine za ki hau yi min dariya, dan kin raina ni".

Sunkuyar da kanta ta yi ta ce.

" Ban yi dan na b'ata maka ba, amma ka yi hak'uri hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allahu".

Tsaki ya yi ya bar wajen.

Da mamaki ta bi shi da kallo, dan bai tab'a yi ma ta irin haka ba.

Fitsarin ta d'aga ta shanye tass ta kalli Boka ta ce.

" Na gama da wannan babin, yanzu a ina zan samu k'ok'on kan Jaki?".

Dariya Bokan yasa yace.

" Hak'ik'a na dad'e rabon da naga mace mara imani irin ki, amma rashin imanin ki yasa Aljani Mugau zai samo miki k'ok'on kan Jaki, kuma muddum muka yi amfani da shi toh ina mai tabbatar miki da aikin ki ya kammala, amma da sharadi"

Tun kafin ya yi shiru tace.

" Dan Allah Kar ka fad'amin sharad'in".

Tsawa ya daka ma ta yace.

" Ke sau nawa zan fad'a miki ba a kiran Allah a nan, na kula har yanzu akwai sauran imani a tare da ke, sabida haka ki je idan imani ya yi k'aranci a cikin zuciyar ki toh ki zo a yi miki aiki".

Hawaye ta hau yi tana yi masa magiya, amma sai ya d'auki wani tsumma ya rufe jikin sa da shi, kafin ka ce tak ya b'ace.

MOMMA

Kallon Ahyan ta yi tace.

" Allah dai ya baka lafiya Adamu, ga shi mahaifinka ya guje mu, ohh gaba d'aya bai yi dacen matan aure ba, tun da mahaifiyarka ta mutu ya zama abin tausayi".

Kuka ne kufce ma ta ai kam ta hau yi.

Kamar daga sama ta ji ya rungume ta ya ce.

" AFFAH".

Kukan ta ne ya tsaya cak ta ce.

" Adamu kai ne?".

Hawayen fuskantar ta ya goge ma ta, har zai yi magana sai ya tuna a roll d'in da suke sai kawai ya ce.

" Affah zan je".

Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce.

" Allah sarki ai ya sauya uwa tun da ya auri Bawo ya watsar da mu".

Kallon ta kawai yake shima abin yana damunsa sosai, amma ba yadda zai yi.

JAMIL

Fitowa parlon ya yi ya zauna a kusa da Ahyan ya ce.

" Brother how are you doing today?".

Kasa cewa komai ya yi dan bai san yadda ya ke amsa masa ba, lokacin da ba shi da lafiya.

Momma ce ta ce.

" Ya jikin naka?, na fad'a maka ka samu khadeeja ka sanar da ita kana son ta, idan ta amince sai a nema maka auren ta".

Gaban Ahyan ne ya fad'i jin wai Jamil ne zai auri Amanah, haka kawai ya ji ba dad'i a ransa, duk da ba son ta yake ba.

Jamil kam murmushi ya yi ya ce.

" Jiki alhamdulillah, in sha Allahu zan same ta sai muyi magana da ita".

" Yauwa to Allah yasa ta amince".

" Ameen momma, tana ina ne?".

Murmushi ta yi tace.

" Tana d'akin Adamu tana gyarawa".

Ahyan ne ya mik'e da sauri ya nufi hanyar d'akinsa.

Momma da Jamil binsa suka yi da kallo dan abin ya zo musu a bazata.

Kafin ya k'arasa d'akin nasa ne ya ci karo da Zulai ta fito daga d'akin Jamil, kallonta ya yi sai ya ga duk ta rame.

Ita kam sai da ta zo daf da shi sannan ta ce.

" Na san duk abinda zan fad'a ba lallai ne ka yarda da ni ba, amma wallahi na tuba na yarda dukkan makaman yak'i na, duk da na san ba zaka fahimci abin da nake nufi ba tun da har yanzu ba ka dawo daidai ba, amma da yardar Allah ka kusa samun sauk'i, ko dan ka ceto Adnan da gawar ummie".

sai ta fashe da kuka.

Da sauri ya d'aga kai ya kalle ta, toh mai ya samu su Adnan kenan?, ita ce tambayar da ya yi wa zuciyar sa.

" Na san wannan ciwon naka da sa hannun Bawo a kai, amma Allah ya fita".

Tafiya ya yi ya nuna kamar bai san abinda take nufi ba.

Sai da ya tabbatar da ta tafi sannan ya k'wank'wasa k'ofar d'akinsa.

AMANAH

Tun da ta gama gyaran d'akin ta nemi wuri ta kwanta, wani wahalallen bacci ne ya yi awon gaba da ita.

Jin shiru yasa shi tsayawa, kusan mintuna 10 yana tsaye, jin babu alamun zata ba shi izinin shiga kawai ya kutsa kansa ciki.

Da sauri ya juya zai fita sakamakon abinda ya gani.

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU♥️)

PAID BOOK 📚 NE KI BIYA 400 DOMIN MALLAKAR NA KI GA ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

MUNA TALLATA HAJA GA WANDA TAKE SON A TALLATA MATA SAI TA YI MAGANA TA NUMBER TA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕 KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)

BOOK 1️⃣

🆓 PAGE 2️⃣2️⃣

NA KUSA GAMA FREE PAGE'S MAI SON KARANTAWA TA BIYA 400 IDAN YA ZAMA COMPLETE ZAN MAYAR DA SHI 500

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Salati ta saki, ganin abin ya fi k'arfinta yasa ta fita daga d'akin.

Sosai take yi masa magiya akan ya taimaka ya yi ma ta aikin da ya kawo ta, amma shiru duk da tasan ya b'ace amma tasan ba nisa ya yi da wurin ba, kuma yana jin ta, haka dai ta bar cikin bukkar zuciyar ta cike da k'una.

Kuka kawai take son yi, amma zuciyar ta tak'i bata had'in kai, blanket ta janyo ta rufe jikin ta ta kalle shi ta ce.

" Mainene haka dan Allah?, tun yaushe kake a nan?".

Gyaran murya ya yi ya ce.

" Ba abinda kike tunani bane, wallahi ban dad'e a nan ba, na zo ne fad'a miki wani abu".

Hijab ta saka, duk da akwai doguwar riga a jikin ta, kallon shi ta sake yi tace.

" Ina jin ka".

Zama ya yi a gefen gadon ya ce.

" ki taimaka ki samu kusanci da Mommy domin ki ji in da su Adnan suke, d'atsu take fad'amin, and please kar ki yarda da auren Jamil".

Cike da mamaki take kallon shi ta ce.
Chapter 16 · 0% Book details