← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya na fad'in hakan ya shiga mota ya tafi.

Ganin ya k'i yarda da kowa yasa momma ta kira Affah a waya ta ce masa.

" Adamu yaron nan fa ya k'i yarda da kowa, sai kiran Ahmanah ya ke, idan da dama dan Allah a rok'i iyayenta ta zo ta zauna da shi na wani lokaci please".

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)

PAID BOOK NE ZA KI BIYA 400 ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WHATSAPP.

GA MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJARTA TA YI MIN MAGANA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

TALLAH TALLAH TALLAH 💃💃💃💃

MUNA SIYAR DA DATA MAI INGANCI DUK MAI SO YA YI MIN MAGANA DOMIN SIYA

08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU 🧕)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE 1️⃣0️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Shiru Affah ya yi, kafin ya ce.

" Momma ba lallai su yarda ba, kuma ni ban san gidan su ba, sai dai Jamil, zan same shi mu yi maganar".

Tsaki momma ta ja ta ce.

" Wanne irin zan cen banza ne wannan, idan ba ka san gidan su ba, ba zaka iya bincikawa ba, ko a wata k'asar take ai ya ka ma ta ka nemo ta, idan kuma bazaka iya ba ni sai na fita neman ta".

Ta na gama magana ta kashe wayar.

Affah kam shiru ya yi ya na nazarin kalaman momma, kafin daga baya ya sauke wayar ya ci gaba da tunanin mafita.

Jawad

Cikin muryar wanda sha ya yi mak'il ya ke magana.

" Tun da ni na yi nawa aiki ya rage naki, in kin ga dama ki k'arasa shi, in kin ga dama ki bar shi".

Ban ji mai d'ayar ta ce ba, na dai ji ya sake cewa.

" Ba wanda ya san da akwai wani abu a tsakaninmu, dan haka ni yanzu ki turo min da ragowar kud'ad'en nan zan biya scorpion kud'in aikin sa".

Kashe wayar matar ta yi.

Tsaki ya ja ya ce.

" Y'ar wahala".

Kallonsa abokinsa ya yi ya ce.

" Baaba ya dai?".

Tsaki ya sake ja ya ce.

" Wallahi ni da wannan y'ar wahalar ce".

Dariya abokin ya yi ya ce.

" Allah wata rana ya ka mata mu kai mata farmaki".

Wata k'atuwar kwalba Jawad ya d'aga ya kai bakinsa, ya ce.

" Rabu da ita kawai".

Da murnar ta ta shiga gida, ta na zuwa ta wuce d'akin Baba domin ta san Lami ta na can, cikin farin ciki ta d'auko wayar ta yi ta nuna wa mama Lami ta ce.

" Mama kin gani waya ya bani, ya ce idan da matsala a kira a fad'a masa".

Da fa ra'ah a fuskar mama ta ce.

" Masha Allahu, Allah ya san ya alkairi".

Baba ma murmushi ya yi ya ce.

" Mun samu ta kiran gwaggo jummai".

Danne b'acin ran ta ta yi ta ce.

" Ehh wallahi Baba".

Laraba kuwa ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe, domin bak'in ciki da hassada.

Jummai kam shigowa ta yi ta na yauk'i ta kalli baba ta ce.

" Baba ya jikin?, ni zan tafi zan je gidan su k'awata".

Washe baki baba ya yi ya ce.

" Toh toh Allah ya yi miki albarka".

Laraba kam kallon jummai ta yi ta ce.

" Sai kin dawo".

Murmushi jummai ta yi ta ce.

" OK sweetheart".

Haka dai su baba su ka ringa hira kamar ba komai a tsakanin Laraba da Lami.

Jummai

Waya ta d'auko ta kira wani guy, cikin kashe murya ta fara magana.

" Jay where are you now".

Cikin kasala Jay ya amsa da.

" Am at home".

Da murna ta ce..

" I'm on my way".

JAWAD

Murmushi ya yi ya kalli, abokinsa ya ce.

" Bari na je na yi wanka, ga J J, nan".

Zum bur abokin ya mik'e ya ce.

" What?, are you sure?".

Tsaki ya ja ya shiga bathroom.

Momma

Kallon Jamil da ya ke bawa AHYAN abinci ta yi ta ce.

" Jamil dan Allah gidan su khadeejah na ke son ka kai ni".

Da sauri ya d'ago ya kalle ta ya ce.

" Momma is everything okay?".

D'an murmushi ta yi ta ce.

" No ina buk'atar yin magana da iyayenta ne, sabida ina son ta dawo nan da zama".

Tab'e baki ya yi ya ce.

" mai zai hana ki auro min ita, sai ta dawo gaba ki d'aya".

Cikin Mamaki!! Momma ta kalle shi ta ce.

Aure kuma Jamil?, son ta ka ke yi? ".

Murmushi ya yi ganin momma ta d'auki zan cen serious ya ce.

" Ba son ta na ke ba tausayin rayuwar ta na ke".

Ya mutsa fuska ta yi ta ce.

" Tell me something about her story".

Gyara zama ya yi ya fara ba ta labarin Amanah, tun daga farko har k'arshe.

Hawaye ta share ta ce.

" Allah sarki, gaskiya ta na ganin rayuwa, amma duk wahalar da ta sha ba ta kai Adamu ba, domin in sha Allahu ta ta wahalar ta zo k'arshe".

Cikin jin dad'i ya ce.

" Yauwa momma, dan Allah

[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)

PAID BOOK NE ZA KI BIYA 400 ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WHATSAPP.

KINA YIN SANA'AH AMMA BA KI DA ABOKAN KASUWNCI. TOH GA DAMA TA SAMU DOMIN DA KUDI KADAN ZAN TALLATA MIKI HAJAR KI KUMA DA YARDAR ALLAH ZA KI SAMU ABOKAN CINIKI. IDAN KINA BUKATA KI YI MIN MAGANA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

TALLAH TALLAH TALLAH 💃💃💃💃

MUNA SIYAR DA DATA MAI INGANCI DUK MAI SO YA YI MIN MAGANA DOMIN SIYA

08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU 🧕)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE 1️⃣1️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Bai tsaya ko ina ba sai gidan su Amanah, sake kiran ta ya yi amma ba amsa, fita ya yi daga cikin motar ya yi sallama a k'ofar gidan, ya dan dade kafin Amanah ta fito, cikin fara'ah ta ce.

" Laah Yayana ka shigo mana".

B'ata rai ya yi ya ce.

" Ina wayar da na baki?".

Murmushi ta yi ta ce.

" Yanzu dai please ka fara shigowa sai mu yi magana".

Fuskarsa ya mayar serious ya ce.

" Answer my question".

Kamar mai jiran umarni ta ce.

" Ta na wurin mama laraba ".

Ai tun kafin ta rufe bakin ta ya nufi hanyar shiga gidan, da sauri ta sha gabansa ta ce.

" Yaya please, kar ka yi mata komai, she's my step mother".

Wani kallo ya yi mata ya ce.

" Out of my side".

Ganin babu alamun wasa a Fuskarsa yasa ta matsa kamar yadda ya bukata.

Da sallama ya shiga gidan, Lami ce kawai ta amsa masa, ita kam laraba d'aki ta shi ge.

" Ah jamilu kai ne, sannu da zuwa".

Kallon Lami ya yi da ta yi magana ya ce.

" Mama barka da gida, ya jikin baba?".

" Alhamdulillahi jiki da sauki sosai wallahi".

" Masha Allahu haka a ke so".

Kiran Amanah ta hau yi akan ta kawo wa jamil ruwa.

Murmushi ya yi ya ce.

" Mama dama wurin baba na zo, dan Allah ko za ki iya yi masa magana".

Ita ma Murmushin ta yi ta ce.

" Toh Bismillah mu je".

Bin bayanta ya yi su ka shiga d'akin baba.

Laraba da ke lek'en su ce ta fito da sauri ta shiga d'akin Lami, wayar da jamil ya bawa Amanah ta ajjiiye a cikin kayan Lami ta fita da sauri.

Gaisawa su ka yi da baba, in da ya ke gabatar musu da maganar da su ka yi da momma, akan suna son a basu aron Amanah domin kula da Ahyan wanda ya ke kiran sunan ta a koda yaushe.

Shiru baba ya yi ya na nazari, ya san k'ila jamil ya yi hakan ne dan ta daina yi wa laraba tallah, amma in yasan wata bai san wata ba,murza zoben azurfar hannun sa baba ya yi ya ce.

" Ni malam Musa na yarda".

Sauke ajjiyar zuciya jamil ya yi ya ce.

" Alhamdulillahi, mama ke ma kin a mince?".

Murmusawa Lami ta yi ta ce.

" Tun da malam ya amince ai nima na amince, amma ka Sani yarinyar nan Amana ce a wurin ka, duk abinda ya sameta kai ne sila, ka rik'e ta kamar k'anwarka wacce ku ke uwa d'aya uba d'aya".

Gabansa ne ya fad'i amma ya danne ya ce.

" In sha Allahu zan yi iya yi na dan ganin na rik'e wannan amanar da kika bani".

Baba ne ya ce.

" Tun kafin na gama yanke hukunci har kun fara magana, toh yardar laraba ita ce tawa in dai ta yarda nima na yarda".

Tashin hankali ne ya bayyana a fuskar Lami da jamil, shi Tashin hankalin yadda ya ga samu, amma kuma ya na k'ok'arin ganin rashin, ita kuma tasan laraba da bak'in ciki da hassada ba lallai ta bar Amanah ta ta fi gidan masu kud'i ba, dan tasan idan ta tafi za ta huta.

Murmushin k'arfin hali jamil ya yi ya ce.

" Baba dama ina son dan Allah ka cewa laraba ta bawa Amanah wayarta, please".

Kallon Lami ya yi ya ce.

" Je ki ki kira min ita".

Ba tace komai ba ta ta shi ta fita.

Bakin k'ofar d'akin laraba ta je ta ce.

" Malam ya na kiran ki".

Daga haka ta koma wurin baba.

Ko second 30 lami ba ta yi da zama ba laraba ta shiga d'akin sai shan k'amshi ta ke.
Chapter 8 · 0% Book details