← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 18

Sashe 15

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

JUNAID ne ya ce.

" D'an ki ne ya kore mu".

Murmushi ta yi ta ce.

" Tohm ga gurin zama nan, sai ku zauna".

D'akin su Jamil ya wuce bai tsaya tankawa Momma ba.

Farkawa ta yi ta ga ya zura hannunsa cikin rigar ta yana wasa da bobs d'inta, da sauri ta mik'e ta ce.

" A uzubillahi'minashaid'anir rajim".

Shi kam ko a jikinsa sai ma ƙok'arin sake saka hannunsa yake.

Kunyarsa ce ta kama ta, ta kalle shi ta ce.

" Mai ye haka?".

Mik'ewa ya yi shima ya ce.

" Ciwo babu".

Shiru ta d'an yi na wani lokaci kafin ta tuna duk abinda ya faru, murmushi ta yi ta ce.

" Ya dai na ciwo".

Shima murmushi ya yi ya ce.

" Zan sha milk".

" Toh bari na je na kawo maka".

Ganin ta juya zata fita ne yasa ya yi saurin mik'ewa ya rik'ota.

Jin ya rik'e ma ta hannu yasa ta juyo a fusace ta ce.

" Wai yau mai yake damun kanka ne?".

Maimakon ya bata amsa sai kawai ya zura hannun sa cikin rigar ta.

Kasa yin magana ta yi sabida jin wani bak'on yanayi da ke ziyartar ilahirin jikin ta.

Ganin ta saki jikinta hakan ya ba shi damar ci gaba da tura hannu cikin rigar.

Kamar wacce a ka jonawa shoking haka jikinta ke rawa.

Cikin tsoron yanayin da ta shiga Ahyan ya cire hannunsa daga cikin rigarta, ido jajir ya kalleta ya ce.

" Ciwo?".

Kasa ba shi amsa ta yi.

Komawa ya yi ya zauna ya na mayarda numfashi.

Ita kam fita ta yi daga d'akin ta tafi nata d'akin.

FEW DAYS LATER

Alhamdulillahi jikin Jamil da sauk'i sosai,amma har yanzu ya kasa fallasa sirrin zuciyar sa, dan ko JAWAD da JUNAID bai ce musu komai ba, ya dai hana su fad'awa kowa halin da yake ciki.

Amanah tun ranar da Ahyan ya yi ma ta abinda ya yi, ta fita sabgarsa domin tun da ya yi ya ji dad'i shikenan a ko ina sai ya yi yunk'urin sa ma ta hannu a riga.

Affah ko kad'an bai damu da rashin su zulai ba, hasali ma sabgogin gabansa ya ci gaba da yi.

BAWO

zaune ta ke a gaban Boka sai gumi take yi, domin ya fad'a mata nan da wani lokaci Ahyan zai samu lafiya, sannan kuma aikin da take yi wa JUNAID ya fara yin sanyi wato ya fara daina karb'ar jikin sa.

Bakin ta na rawa ta ce.

" Tsafi ya baka nasara, yanzu ba wata hanyar da za a bi domin ganin Ahyan bai dawo daidai ba?".

Dariya Bokan ya yi ya zuba wani abu a cikin wuta ya ce.

" Duk abinda na lissafo miki dole ya faru, sannan ina ganin wani haske ya na baibaye Ahyan, kuma duk wani aiki idan mun tura masa ba ya samun sa".

Kasa yin magana ta yi, dan yau bata ji dad'in zuwa wurin Bokan ba.

Ruwan da ya ke zubawa a cikin wutar dake ci agansa ya watsa ma ta ya ce.

" Na sallame ki".

Sumsum ta bar bukkar zuciyar ta cike da bak'in ciki.

" Wallahi mama na gaji da tafiyar nan".

A zafafe ta kalli Jummai tace.

" Ni ban ce na gaji ba sai ke, ubanwa za a nemawa taimakon in ba ke ba?".

Tura baki ta yi ta ce.

" Ni fa in dai akan JAWAD sannu ne ki daina b'ata lokacin ki, domin shi kiss ɗaya ko runguma sun wanke masa zuciya".

Dogon tsaki Laraba ta ja ba ta ce komai ba.

BOKA

Tun daga nesa ya hango su, hakan yasa shi hade rai ya fara magana.

" Kwanaki kun zo na fad'a muku ba zan iya yin komai akan yarinyar ba, sai dai yaron da kuka ce yana son ta".

Jiki na rawa Laraba ta ce.

" Mun amince ayi mana aiki a kansa".

Momma ce ta kalli Amanah ta ce.

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU♥️)

PAID BOOK 📚 NE KI BIYA 400 DOMIN MALLAKAR NA KI GA ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

MUNA TALLATA HAJA GA WANDA TAKE SON A TALLATA MATA SAI TA YI MAGANA TA NUMBER TA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕 KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE 2️⃣0️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

" Wai khadeeja mai ya had'a ki da Adam ne?".

" Adam kuma, waye Adam?".

Murmushi momma ta yi tace.

" AHYAN fa nake nufi".

D'an sosa kai ta yi ta ce.

" Ba komai fa, mai kika gani?".

Sauke ajiyar zuciya momma ta yi tace.

" No ba abinda na gani".

Haka dai suka dinga hira.

JAMIL

Kallon JUNAID dake waya ya yi, ya ce.

" Wai dan Allah mai kuke ji a jikin matan banza?".

Kashe wayar JUNAID ya, yi ya kalli Jamil ya ce.

" Ba zaka gane ba, kawai dai ka kallemu".

Tsaki Jamil ya ja ya tofar da yawu ya ce.

" Allah ya shirye ku?".

Murmushi JUNAID ya yi ya ce.

" Ai JAWAD ya shiryu dan yanzu ko wise ba sha yake ba, bare kuma bin mata, gaskiya girl d'in nan ta samu lada".

Kallon yi min k'arin bayani ya yi wa JUNAID.

Kamar JUNAID ya san mai yake nufi yace.

" I mean Deejah, sabida ita ya dai na yin komai wai sonta yake".

Cikin ihu wanda ya karad'e ko ina na gidan, Jamil yace.

" NOOOOOOOOO NI NA KE SON TA".

Da mamaki sosai momma ta k'wallawa Amanah kira tace.

" Je ki ki duba min Adamu dan Allah, kamar ihunsa nake ji".

Da sauri Amanah ta yi hanyar d'akin mazan gidan.

Daidai ƙofar d'akin Jamil ta ji ana cewa.

" Wallahi JUNAID na fi shi sonta, Allah ne shedata ina yi ma ta mugun son da ban tab'a yiwa kowa shi ba, please ka taimaka min ta so ni, duk wata damuwar da nake ciki ita ce sila please Ju. Ju. JUNAI.................".

Shiru ya yi sakamakon sark'ewa da numfashin sa ya yi.

Da sauri JUNAID ya tallafo shi ya ce.

" Mu tafi hospital".

Sun kutar shi ya yi ya aza bisa kafad'arsa, jin za a fito yasa Amanah ta yi saurin shigewa d'akin Ahyan.

Hankali tashe momma ta ke kallon JUNAID ta ce.

" Lafiya kuwa? Mai ya same shi?".

Shi dai JUNAID ya kasa yin magana, domin burin sa kawai ya kai shi hospital.

HIJAB momma ta saka ta bi bayan JUNAID.

Tun da ta shiga ta manna bayan ta jikin k'ofa bata d'aga kanta ba, hannu tasa ta dafe ƙirjinta dake barazanar tsagewa, tsabar fad'uwar da yake.

Kamar daga sama ta ji an ce.

" What are you doing in my room?".

Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi, farar jallabiyya ce a jikin sa, ya taje sumar kansa sai ƙyalli take, ga wata fitinanniyar hula da yasa, ya yi masifar kyau, kamar ka sace shi ka gudu.

Murza idonta ta yi, ta sake kallon sa da kyau ta ce.

" Tace yaya Ahyan, kai ne?, da gaske ka warke?".

Kallon who are you, ya yi ma ta, ganin ta na matsowa inda yake ya yi saurin cewa.

" Please out of my room".

Maimakon ta fita kamar yadda ya buk'ata sai ma sake matsawa take.

Ita kam ta kasa yarda shine ya dawo normal, sauri ta k'ara domin tabbatarwa, tana zuwa daff da shi ta saka hannunta, tab'a fuskarsa ta hau yi, jin da gaske shine ya sa ta sakin ihu ta rungume shi.

AHYAN

Daskarewa ya yi a wurin, domin tun da yake bai tab'a rungumar mace kamar haka ba.

AMANAH

Jikinta ne ya hau rawa, jin fatar Jikinta ta mannu da ta shi.

Shi kam hanyoyin sadarwar jikin sa ne suka fara sadar da rungumar da ta yi masa.

Tunawa da ba yayanta ba ne kuma ba muharraminta bane, hakan yasa ta yi saurin sakin shi, ta je gefen gadon shi ta zauna.

Kallon ta ya yi up and dawn yace.

" Please who are you?, and What are you doing here".

Murmushi ta yi ta ce.

" Ni dai sunana khadeeja".

Nan dai ta bashi labarin rayuwar ta, da dalilin zuwan ta gidan, har da abinda ya faru yanzu, da dalilin shigowarta d'akinsa.

Cikin mamaki ya ke kallonta ya ce.

" Nima abinda zan iya tunawa shine, nasan na yi k'ara, da aka jima sai na ganni a k'asan toilet, na fad'i,kaina yana juyawa bayan wani lokaci kuma na dawo normal, shine na yi wanka".

Murmushi ta yi tace.

" Yanzu ba inda yake maka ciwo?".

Kai ya d'aga ma ta.

Murmushi ta sake yi tace.

" Alhamdulillahi, bari na je na fad'awa momma nasan za ta yi farin ciki".

Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar d'aga ma ta hannu ya ce.

" Bana son domuwar magana, please kar ki bari kowa ya san na dawo daidai, ciki harda momma, and ina Affah?".

" Gaskiya ya dad'e rabon da ya zo nan, amma Mommyn ku tana nan gidan wai ya korosu, ita da yaya JUNAID".

Murmushi ya yi bai ce komai ba.

HOSPITAL

Bayan kusan awa d'aya da likitoci suka d'auka akan JAMIL, can wani Dr ya fito ya ce.

" Ku biyo ni office".

Bin bayansa momma da JUNAID suka yi.

Bayan sun zauna ne ya kalli momma yace.

" Hajiya am sorry to say Jamil ya kamu da ciwon damuwa, a yanzu haka k'wk'walwarsa ta na neman kamuwa da ciwon, and dama zuciyar sa ta kamu da ciwo, zuwan da ya yi na k'arshe na sanar da shi ya cire damuwa daga zuciyar sa, sabida gudun hakan amma bai kiyaye ba, yanzu ga shi abin har ya fara tab'a masa Brain nasa, kuma dan girman Allah idan kun san abin da ya ke so please ku gaggauta ba shi, domin tsira da lafiyar sa".

Salati kawai momma ke yi, da sallallami.

JUNAID ne ya yi k'arfin halin yin magana ya ce.
Chapter 15 · 0% Book details