← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" anty zo ki ga Jay, tare suka zo da anty Amanah".
Bin bayan ta Jummai ta yi, suka shiga d'akin ko sallama babu.

Ahyan ne ya kalli Amanah ya ce.

" Mu tafi gida".

Kafin Amanah ta yi magana Jummai ta ce.

" Allah ya toni asirinka munafuki, dama ashe gurinta ka koma shi ne ni ka watsar da ni".

Dafe kansa ya yi ya ce.

" Tun farkon had'uwata dake, ke kika fara lalata min rayuwa domin ke ki ka nuna min hanyar banza, kuma kin san ba na iya bin mata sai dai ke, amma ita Deejah ba irin ki ba ce, ita tsaftattaciyar gona ce, wacce babu mai shigar ta sai mai ita, ke kuma fa?".

Kuka sosai take yi ta ce.

" Ko ma mai za ka ce ka fad'a, amma wallahi kai nawa ne ni kad'ai, kuma in dai ina da rai da lafiya ba zan bari ka auri Amanah ba".

Tana gama magana ta fita.

Waya ta d'auka ta kira numbern JUNAID, bugu biyu ya d'auka ya ce.

" Hello".

Tsaki ta yi ta ce.

" Wai kai wanne irin shashasha ne, bana ce ka turo min number scopion amma ka k'i ko?".

Tsaki ya yi ya ce.

" Who are you".

" Kutumar ubanka ni za ka zaga da yaren nasara".

Dariya ya yi ya ce.

" ahhh yanzu dai ina kan wata y'ar shila ne, amma idan na sauka zan kira ki".

Zagin sa ta ringa yi ta kashe wayar.

Jamil ne zaune a gaban DR ya na rubuta masa magani, kallo jamil DR ya yi ya ce.

" Wai mai ka saka a ranka haka ne?".

Murmushi ya yi ya ce.

" Fad'a min mai ke damuna".

Sake duba file din gabansa ya yi ya ce.

" Zuciyar ka ta kusa kamuwa da ciwo, ko dai ka yi k'ok'arin ba ta abinda take so, ko kuma ka cire damuwa daga ranka".

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU♥️)

PAID BOOK 📚 NE KI BIYA 400 DOMIN MALLAKAR NA KI GA ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

MUNA TALLATA HAJA GA WANDA TAKE SON A TALLATA MATA SAI TA YI MAGANA TA NUMBER TA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕 KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

BOOK 1️⃣

🆓 PAGE 1️⃣7️⃣

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Murmushi ya yi ya ce.

" Allah sarki rayuwa ta, k'ilan ita ce sanadin rayuwa ta, domin ba na gabanta".

Da mamaki!!, a fuskar Dr ya ce.

" Kar ka cuci kan ka, idan har ba ka gwada sa'ar ka ba, ba zaka samu abinda zuciyar take so ba".

Dafe zuciyar ta shi ya yi ya ce.

" Gaskiya bana tunanin zuciyar nan za ta samu abinda take so, domin ita wacce nake so ba ta so na, sabida ta ce ba za ta yi aure ba, amma zan jure ciwo da rad'ad'in da zuciya ta take yi min, a kanta".

Jikin Dr ne ya yi sanyi ya bud'e baki ya ce.

" A gaskiya na tausaya maka, kuma ina baka shawara a matsayina na Doctor ka nisanta kanka da ga wurin yarinyar, sannan ka dai na saka damuwa a zuciyar ka".

Godiya sosai ya yi wa Dr ya tafi gida.

Amanah runtse idon ta ta yi ta ce.

" Please Jawad ya isa haka, dama duk zinar da kake yi da ƙanwata kake yi?".

Cikin lallashi ya ce.

" Mu tafi gida zan yi miki baya nin komai".

" Ba zan bika wallahi, haka kawai a hanya nima ka yi iskanci da ni".

A zafafe ya matsa kusa da ita, bai jira komai ba ya rungume ta, hakan bai wadatar da shi ba sai da ya had'e bakinsu wuri d'aya, kusan minti biyu sannan ya cire bakinsa ya ce.

" Deejah ki sani ba da iskanci na ke son ki ba, da aure na ke son ki, in da a ce iskanci zan yi da ke wallahi da tuni na yi, amma kin kasa fahimta, kuma ba wai sai a hanya zan yi miki wani abun ba, ko a ina zan iya yi".

Ita kam tunda ta ji ya rungume ta ta daskare a wurin, sanda ya had'e bakin su kam suman tsaye ta yi, domin tun da take a duniya makamancin hakan bai tab'a faruwa da ita ba.

Kallon bakinsa kawai take ba tare da ta na jin sautin muryar sa ba, amma duk abinda ya ke fad'a ta gane, danne zuciyar ta ta yi ta kalli Ahyan da bai san wainar da suke toyawa ba ta ce.

" Ya Ahyan ta shi mu tafi gida".

Ajjiiye wayar ya yi ya mik'e.

Wayar ta d'auka domin ta Ahyan ce.

Hannun ta Ahyan ya rik'e su ka fita.

Suna fita suka ci karo da Laraba, wacce ta fito yi wa Amanah rashin mutunci.

Tsaki Laraba ta yi ta ce.

" Ke makira, tsaya a nan".

Ko in da take Amanah ba ta kalla ba ta nufi d'akin Lami, janyo Ahyan Laraba ta yi ta ce.

" Kai mahaukaci kai tsaya, tun da ita karuwar taka ta k'i tsayawa".

Cike da k'osawa da rashin mutuncin da a ke yi mata ta juyo ta ce.

" Laraba, ki fita daga ido na, duk rashin mutunci da Wulak'anci da kike min ya i she ni haka, ko dan kinga ina yi miki shiru ne?, kuma wallahi ni ba karuwa ba ce, uwata ba ta haifi karuwa ba, ke ki ka haifi karuwa, karuwar ma mara Class".

Jawad Laraba Jummai Lami Jamila duk shiru su ka yi suna kallon Amanah wacce take ta faman huci, Lami ce ta ce.

" Wannan shi ne daidai, tun yarinyar nan ta na jin tsoron ki ga shi har ta daina, sai ki yi hankali ki gyara halinku".

Kamar daga sama haka Laraba ta fashe da kuka ta na cewa.

" Yau ni Laraba za ki daka, toh wallahi bari malam ya dawo yau sai na bar gidan nan, haba dan Allah a gaban yara na".

Kallo ne ya koma kan Laraba, ita kam Baba ta gani shi yasa ta saka kukan k'arya.

Jawad kam kallon Laraba ya sake yi ya ce.

" Gaskiya Deejah ba karuwa ba ce, domin ta na tsare mutuncin ta, ba kamar J J ba".

ya fad'a ya na nuna Jummai da ta yi zukud'i ta na kallon shi.

" J J kuma, wacce J J?".

Lami ta tambaya.

Murmushi Amanah ta yi ta ce.

" Mama sunan Jummai ne, wanda karuwai y'an uwanta suke kiran ta da shi".

" Allah ya kyauta".

Cewar Lami.

Baba kam ja ya yi da baya ya koma waje, dan kunnuwansa ba za su iya jin wannan mummunan zancen ba.

Sallama Amanah ta yi wa Lami a kan zasu tafi.

Shiga d'aki Lami ta yi ta d'auko wayar da Jamil ya bawa Amanah ta ba ta ta ce.

" So a ka yi a had'a ni da malam, a kan wayar nan, sai kuma Allah ya tura mata aniyarta".

Murmushi Amanah ta yi ta karb'i wayar ta ce.

" Ikon Allah, ai Allah ya fi su".

Fita Amanah ta yi ta dawo hannun ta rik'e da manyan ledoji guda biyu.

Lami ta mik'awa ta ce.

" Ga shi momma ce ta ce a kawo miki, wannan kuma na Baba ne".

Godiya Lami ta ringa yi harda gud'a.

Laraba kam barin wajen ta yi ta shige d'akin ta.

A haka dai suka koma gida ba tare da sun ga Baba ba.

Ko da suka koma gida Amanah ba ta nunawa momma komai game da Jawad ba, haka su ka ci gaba da harkokinsu.

JAMEEL

Kallon momma ya yi ya ce.

Dan Allah saka khadeeja ta kawo min tea, ina d'aki na".

" Toh". ta ce ta hau kiran Amanah.

Shi kam d'aki ya tafi domin ji yake zuciyar sa na masa zafi,amma yau in sha Allahu zai tunkareta da maganar.

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: Uhttps://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU♥️)

PAID BOOK 📚 NE KI BIYA 400 DOMIN MALLAKAR NA KI GA ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

MUNA TALLATA HAJA GA WANDA TAKE SON A TALLATA MATA SAI TA YI MAGANA TA NUMBER TA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕 KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE1️⃣8️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Ba tare da tunanin komai ba ta had'a masa tea d'in da momma ta sa ta, bayan ta gama had'awa ne ta d'auki tray d'in da ta zuba komai a kai ta nufi hanyar d'akinsa.

Sai da ta wuce d'akin Ahyan sannan ta ƙarasa nasa, bubbuga ƙofar ta yi.

Can ciki ya ce.

" Come in".

Da sallama ta shiga d'akin ta ce.

" Yayana barka da gida".

Murmushi ya yi ya ce.

" Yauwa zauna magana za mu yi da ke please".

Ba ta yi tunanin wani abun ba ta zauna a kan kujera, ta kalle shi ta ce.

" Ina jin ka yayana".

Shima zaman ya yi ya ce.

" Khadeejah, ki bani aron hankali da tunanin ki please".

Murmushi ta yi ta ce.

" Tohm na baka".

Gyara zama ya yi ya ce.

" Wani aboki na ne ya tambaye ni, na ba shi shawara, kuma na yi tunani na kasa ba shi amsa amma ke zan baki labarin sa sai ki ba ni shawara ni kuma na fad'a masa".

Dariya ta yi ta kalli fuskarsa ta ce.

" Yaya why not ka tambayi momma ko Jawad?".

Dafe kansa ya yi ya ce.

" Come on, ke nake son tambaya, sabida ina son ganin shawarar da za ki bani".

" Tom shikenan yaya ina jin ka".
Chapter 13 · 0% Book details