← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 18

Sashe 6

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ummana da kin bar ni ma da na fad'a domin wad'annan kalaman na ki na dad'e da yin haddar su a kaina".

Ita ma dariya ta yi ta ce.

" Da Allah ya na barin wani dan wani ya ji dad'i da na ce Allah ya barni domin ki".

Murmushi na yi na ce.

" Dan Allah ummana mu dai na wannan zance, yanzu dai kin ga saura shekara hud'u mu yi sauka, toh idan na yi sauka sai kin Kai ni wurin ummanki, da gwaggo jummai".

Murmushi ta yi ta ce.

" Ni kam ina jin dadin hirar nan ta mu, dan Allah ki bar maganar sauka ma yi daga baya, amma yanzu mu yi fira".

Kuka na saka na ce.

" Shi ke nan ummana tun da ba za ki yi min murnar sauka ta ba".

Wannan Karon da k'yar ta yi magana ta ce.

" Allah ya yiwa karatu da rayuwar ki albarka ubangiji ya ba ki miji na gari wanda zai kula da rayuwar ki".

Tsalle na yi na dire na ce.

" A, ah ummana ba na son na yi aure na barking, gara mu yi ta zama ta re".

Tari ta hau yi, ta na son yi magana amma ta kasa yi.

Da gudu na fita domin kiran Baba don na ga jikin na ta ya tsananta, ko da na je kiran sa ya na d'akin mama Laraba, da sallama na shiga d'akin na ce.

"Baba ummana, ka zo za ta mutu".

Jinkin sa na rawa ya Mike zai biyo ni, amma mama Laraba ta ce.

" Musa koma ka zauna, ban baka umarnin fitowa ba, idan kuma ka fito ranka zai ba I".

Kallon banza ta watsa min ta ce.

" Ke Amanah kike ko azabah, to ko ma dai ya ya ne wuce muje na gani, ko lokaci ne ya yi".

Kallon Baba na ke Wanda ya koma ya zauna, ya na matsar k'walla,jin ta ja hannuna ya sa na bi bayan ta.

Ko da muka je har rai ya yi hakinsa".

Da iya ka cin gaskiyar ta ta ke yin kuka domin ko mai dawo mata ya yi kamar video.

Ruwa Jamil ya mik'a mata ya ce.

" Is OK, bar shi haka".

Bata karbi ruwan ba ta kalli fuskarsa da ta yi ja sabida kukan da ya ke dannewa ta ce.

" Bayan mutuwar ummana ne na dawo kamar jaka domin, duk wani aikin gidan ni na ke yin sa, dama Baba ba ya iya yi mata musu, ta bangare daya ne ba ta samu galaba a kansa ba, shi ne kara aure, domin ko shekara uku ummana ba ta yi da mutuwa ba ya auro mama Lani, mama Lami mutuniyar kirki ce, sosai dan ba halin su daya da laraba ba,haka dai rayuwa ta ci gaba da tafiya, ina shan wahala, sanda na gama secondary school Baba ya so na dora amma Laraba tahana, yaran ta kuma sun ci gaba da karatu, ni kuma sai ta fara yi min awara da dan kalin Hausa ina siyar wa a bakin titin layin mu".

Kuka ta hau yi sosai.

Ba kad'an ba Jamil ya ji tausayin ta, bai san lokacin da ya Mike ba ya je in da ta ke ya rungumeta.

Akwai book din da na rubuta mai suna SAJJAD duk mai bukata ta yi min magana domin siya naira 400 ne ba tsada

Accou number 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WhatsApp

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ❤️)

PAID BOOK NE ZA KI BIYA 400 ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

SHAIDAR BIYA TA 08133163639
WHATSAPP.

KINA YIN SANA'AH AMMA BA KI DA ABOKAN KASUWNCI. TOH GA DAMA TA SAMU DOMIN DA KUDI KADAN ZAN TALLATA MIKI HAJAR KI KUMA DA YARDAR ALLAH ZA KI SAMU ABOKAN CINIKI. IDAN KINA BUKATA KI YI MIN MAGANA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU

TALLAH TALLAH TALLAH 💃💃💃💃

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DAoXdILRZKjC042FBN7HEK?mode=r_c Kina neman inda zaki samu kaya masu sauqi da quality taho nan mamana kayanmu sunada kyau ga sauki farashin sarine muna aika kayan mu ko ina in sha Allah

Ga wacce bata bukatar shiga group din za ta iya yi mata magana ta number t👇👇

Oum Ra'is 913 824 3082

Kar ku manta kayanta suna da kyau sosai muna maraba da masu siyan d'aid'ai ko sari

MUNA godiya 🤝😊

TALLAH TALLAH TALLAH 💃💃💃💃

MUNA SIYAR DA DATA MAI INGANCI DUK MAI SO YA YI MIN MAGANA DOMIN SIYA

08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU 🧕)

BOOK 1️⃣

🆓PAGE 8️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Kamar daga sama ta ji ya rungume ta, ba ta san ta na da k'arfi ba sai da ta ga Jamil a k'asa, da sauri ta fa ra magana ta ce.

" Idan ba ka manta ba a cikin labari na na fad'a maka mahaifiya ta ta ce, na rik'e mutunci na, toh ina ganin bai kamata ka rungume ni ba".

Ta shi ya yi ya karka d'e jikinsa ya ce.

" Am sorry ban yi dan wani abu ba, na yi ne sabida ki samu nutsuwa".

Share hawayen fuskar ta ta yi, ta ce.

" Zan ta fi gida amma zan dawo, Babana ba shi da lafiya, magani na fito siya masa".

Kallon ta ya yi ya ce.

" Idan ba damuwa mu je na kai ki gida, sai na yi musu bayani kin ga kin dad'e".

Ba ta yi magana ba ta dafa gadon a hankali ta mik'e, dama hijab d'in ta ya na jikin ta, dan haka takalmin ta kawai ta saka, ta nufi k'ofar fita.

Shima bin bayan ta ya yi, ta riga shi fita domin shi sai da ya je ya yi wa Dr bayanin zai dawo, kafin ya fita in da ya yi parking d'in motarsa.

GIDAN MALAM MUSA.

Tun da mama Lami ta dawo daga neman Amanah ta kasa yin wani kwakwkwaran motsi, domin abin ya dame ta sosai, a ce mutum ya fita tun safe amma ga shi magriba ta kawo kai ba ta dawo ba.

Tana cikin zullumin ne ta ji ana sallama a k'ofar gida, da sauri ta ta shi ta fita domin ganin ko lafiya.

Gyara tsayuwarsa ya yi ya sa ke yin sallama ya ce.

" Assalamu'alaikum".

Daga ciki mama Lami ta amsa da.

" Wa'alaikassalam".

Sauke ajjiyar zuciya ya yi dan yasan ba Laraba ba ce, tun da aka amsa masa cikin kwanciyar hankali.

Fitowar mama Lami ya yi daidai da fitowar Laraba, wacce jikinta ke rawa ta zo ta ga Wanda ya ke kwad'a musu sallama.

Har k'asa ya tsugunna ya ce.

" Mama barka da yamma".

Da "Yauwa" ta amsa Domin ba ta cikin ya na yi mai dad'i.

Magana ya sa ke yi cikin ladabi da biyayya, ya ce.

" Mama ni dai suna na Jamil, a tare da ni kuma akwai Khadeejah wato Amanah, ta taimaki d'an uwa na ne, ta kai shi hospital sa ka makon ciwon da ya ji
".

Nan dai ya bata labarin komai.

Tun kafin ya yi shiru Laraba ta hau salati ta na fad'in.

" Ka ji shegen yaro mak'aryaci, ubanwa zaku rainawa hankali, kawai ka fito fili ka ce ta siyar maka da mutunci ta, ba wai ka ringa kame_kame ba".

Duk abin da ke faruwa Amanah ta na jin komai, fitowa ta yi ta ce.

" Wallahi mama ba abinda kike tunani ba ne".

Mari Laraba ta sauke mata a kunci biyu, ta ce.

" ke y'ar iskar yarinya, duk iskancin da kike yi ina da labarin sa, kar ki ga na zuba miki ido, kawai bari na yi lalacewar ta ki ta fito fili kowa ya gani, toh alhamdulillahi ga shi har mazan banza sun fara sauke ki a babbar Mota".

Lami ce ta k'arb'e da fad'in.

" K'arya kike Laraba, wallahi ni nasan Amanah ba zata taba aikata abinda kike jifanta da shi ba".

Dariya ta yi ta nuna Jamil ta ce.

" Kina nufin kin yarda da abinda wannan fasik'in ya fad'a kenan?".

Kafin Lami ta ba ta amsa Jamil ya kai mata naushi a baki, kafin ka ce tak ya zubar mata da hak'ora biyu, cikin bacin rai ya ce.

" Mu ba fasik'ai ba ne, sai dai idan ke kika haifi fasik'ai, kuma wallahi daga yau idan bakin ki ya sake furta min wannan kalmar sai na yi ajalin ki, jahilar banza da wofi".

Amanah kam banda kuka ba abinda ta ke yi.

Mirmushi Lami ta yi ta ce.

" Ka yi min daidai Jamilu, gara da ka yi Maganin wannan shed'aniyar".

Kallon Amanah ya yi ya ce.

" Khadeejah shiga ciki ki cewa Baba ya na da bak'o a waje".

Juyawa cikin gidan Laraba ta yi ta ce.

" Ba tsinanne da zai shigar min d'aki".

Tana fad'in hakan ta ruga da gudu, dan Jamil ya dasa mata tsoronsa a zuciyarta.

Lami kam dariya ta yi ta ce.

" Shigo mu je Jamilu ai ni yau ka yi min komai wallahi".

Momma

Ta kalli status d'in Jawad ya fi sau shurin masak'i, sai cizon yatsa ta ke, jira ta ke kawai ya dawo gidan dan sai ya fad'awa aya zak'inta.

Zulai

Kayan ta ta had'a tana kuka, dan dai bata san da b'atan Ahyan ba, amma ta na ji tana gani ya koreta.

Bawo

Bud'e drower ta yi ta d'auko wani k'ullin magani, runtse idon ta ta yi ta juye maganin a bakin ta, ta d'auki minti biyar da maganin a bakin ta kafin ta fito da shi, ko da ta fito da shi ya zama kamar daddawa tsabar bak'in da ya yi, jin motsin za a Shigo yasa ta yi saurin saka abin a cikin drower ta rufe.

Affah

Shiga d'akin ya yi da sallama a bakinsa ya ce.

" An samo in da ya ke".

Da sauri ta ce.
Chapter 6 · 0% Book details