← Book details Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bawo kuwa duniya ta na gara mata yadda ta ke so, dan ma yanzu ba ta iya cin galaba a kan Ahyan, ta rasa dalilin da yasa hakan, Amanah kam ta yi aiki a kan ta ku san sau bakwai, amma bata samun nasara.

JAMIL

Ciwon soyayyar Amanah ne ya ke ta nuk'urk'usarsa, ya rasa yadda zai yi ta so shi, kullum abinda take cewa shi d'in a matsayin yayanta ta d'auke shi, ba saurayi ko mijin da za ta aura ba, hakan na damunsa sosai.

JAWAD

Tun lokacin da ya kama jummai da junaid bai sake nemanta ba, ya ma manta da ita, soyayyar Amanah kam kamar kullum hura masa wuta a ke a cikin zuciyarsa, a kan son ta, sosai yake son zama mutumin kirki domin ta so shi.

AHYAN

ALHAMDULILLAHI jikinsa da sauk'i sosai dan yanzu ciwon da ya ji duk ya warke, ga shi Amanah ta na kula da shi sosai, har k'iba ya yi.

Affah kam gaba d'aya hankali da tunaninsa suna kan Bawo sai yadda ta ce haka a ke yi, rabon shi da gidan momma kusan wata d'aya kenan, neman su Adnan ma ita ce take ba shi umarnin ya yi.

Ta na kitchen ta na dafa abinci, domin tun da ta zo gidan ita ke yin girki, ruwan zafi ta d'aura a kan Gas ta juya ta kalli Ahyan ta ce.

" Ya Ahyan zo ka ta ya ni please".

Dariya ya yi, wacce idan ka gani kasan ba ta masu badataccen hankali ba ce, ya ce.

" A a, wunya ina ji".

Dariya ta yi tace.

" Wato yau da y'an wasan na ka ka ta shi ko?, wai wunya hhhh yunwa dai ko?".

Shi ma dariyar ya yi ya ce.

" Ehh yunwa na ke ji".

A haka dai suna yin hira harta gama dafa, shinkafa da miya.

Zaune su ke su biyar a kan dining wanda ya ke d'aukar mutum shida.

JAWAD ne ya kalli Amanah ya ce.

" Kad'an za ki zuba min".

Zuba masa ta yi kamar yadda ya buk'ata, ta zubawa kowa, Ahyan ne ya saka hannu a plate d'in gabanta ya ce.

" Tare za mu ci ko?".

Murmushi ta yi ta ce.

" Allah yaya cin ka ya yi yawa, d'atsun ma fa sai da ka ci abinci a kitchen".

Jamil ne ya zuba musu ido, ji yake ina ma a ce shi ne, ko ba komai dai zai samu kulawarta da Murmushin sa kuma duk domin sa.

Momma ce ta ce.

" Jamil ka ci abincin mana, kar ya huce".

Danne komai ya yi ya fara cin abincin.

Sai da suka gama tsaf sannan, Jawad ya ce.

" Gaskiya kin iya girki".

Murmushi ya yi dan ta na son idan ta yi abu a yaba mata, ta ce.

" Na gode".

Har cikin ransa ya ji dad'in godiyar da ta yi masa.

Kallon Jamil ta yi ta ce.

" Yayana, ya na ji ka shiru, ko dai abincin bai yi maka dad'i ba?".

Sauke ajjiyar zuciya ya yi ya ce.

" Ai kin san an ce idan abinci ya yi dad'i tsabar santi mutum ko magana ba ya iya yi".

Dariya ta yi ta ce.

" Tohm kenan kai ma dad'in ne ya hanaka yin magana?".

Shi ma dariyar ya yi ya ce.

" Ehh mana, ai gaskiya girkin ya yi dad'i".

Wannan karon momma ce ta ce.

" Za su cika ki da dad'in baki, kin fasa zuwa gidan ne?".

Murmushi ta yi ta ce.

" Kai momma dan Allah, zan je mana, amma so na ke sai ya Ahyan ya yi bacci kar ya ce zai bi ni".

JAWAD ne ya ce.

" Tom mai zai hana ki shirya sai na kaiku ke da shi d'in, tun da kin san dai ba dole ba ne ya yi bacci, ga shi yamma ta yi".

Ji ta yi ta yarda da shi, dan haka ta ce.

" Toh bari na shirya sai mu je".

JAMIL kam shiru ya yi bai ce komai ba.

LARABA

Kallon jummai ta yi tace.

" Wai mai yasa mijin ki yake koroki ne?".

Cikin kuka ta ce.

" Wallahi ba zan koma gidan shi ba, ni dama Jawad na aura ba shi ba, kawai dan ban kai masa budurci na ba, shi ne fa ya ke ta Wulak'anta ni, kuma ai shi ma ma ne min mata ne, dan har cikin gida yake kawo su".

Tagumi Laraba ta yi ta ce.

" Tun daga yanzu har na fara ganin abinda bai kamata ba".

Lami ce ta rangad'a gud'a ta ce.

" Maraba da AMANAR ALLAH sannu da zuwa".

✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU❤️)
[8/6, 8:00 PM] Nusaiba Muhammad Ibrahim: https://chat.whatsapp.com/Ew9kyz36EaKF83qTycKxNu

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

(🧕KISHIYOYIN UWAH🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM(AMINIYAR JAJIRTATTU♥️)

PAID BOOK 📚 NE KI BIYA 400 DOMIN MALLAKAR NA KI GA ACCOUNT NUMBER 8136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY

MUNA TALLATA HAJA GA WANDA TAKE SON A TALLATA MATA SAI TA YI MAGANA TA NUMBER TA 08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM

(🧕 KISHIYOYIN UWAH 🧕)

(TRUE LIFE STORY)

BY NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM (AMINIYAR JAJIRTATTU ♥️)

BOOK 1️⃣

🆓 PAGE 1️⃣6️⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

Da gudu Laraba ta fito daga d'akin ta dan ganin Amanah.

Jummai ce ta yunk'ura da k'yar ta fito.

Amanah ce ta kalli Lami ta ce.

" Mama tare nake da bak'i a waje".

Murmushi Lami ta yi ta ce.

" Kai masha Allahu kin ga yadda ki ka yi k'iba kuwa, ga wani haske da kika k'ara, kai Allah dai ya baki gidan hutu idan ki ka ta shi yin aure".

Dariya sosai Amanah take ta ce.

" Ameen mama, baba ba ya nan ne?".

Bud'e d'akin baba Lami ta yi ta na fad'in.

" Je ki shigo da baƙin kar su ga an bar su a waje".

Laraba ce ta ce.

" Ke shegiya ba za ki iya zuwa ki gaida ni ba?".

Murmushi Amanah ta yi ta ce.

" Lah ai ban san ki na gidan ba".

Kallon banza Jummai ta watsawa Amanah ba ta ce komai ba.

Tsaki Laraba ta yi ta ce.

" Gidan ubanwa zan je da?, shegiya mara tarbi ya".

Murmushi ta sake yi ta ce.

" Au ai kamar Jummai nake gani, dama talaka na ganin ku?".

Ashar Laraba ta lailayo ta dannawa Amanah ta ce.

" Ke bana son munafunci, faɗi ki sake fad'a, talaka ba ya ganin su".

Ita dai Amanah fita ta yi daga gidan.

Lami kam murmushi ta yi ta ce.

" Idan ka ce tukunyar wani bazata tafasa ba kai taka ko d'umi ba za ta yi ba".

Laraba ta bud'e baki za ta yi magana sai Jummai ta ja hannun ta su ka koma d'aki.

Kuka Jummai ta sa ta ce.

" Mama kalli fa ki ga yadda Amanah ta koma, ni kuwa duk na lalace".

Jamila dake kwance ta na bacci bud'e ido ta yi ta ce.

" Dan Allah da gaske ta zo?".

Tsaki suka yi basu ba ta amsa ba.

Ita kam da gudu ta fita daga d'akin domin zuwa wajen y'ar uwar ta.

Da sallama suka shigo gidan, wacce ta sauka a kunnen Jummai, da sauri ta mik'e tsaye ta ce.

" Mama Jay".

Kallon rashin fahimta Laraba ta yi mata ta ce.

" Mainene kuma haka?".

Kuka ta sa ta ce.

" Mama Jawad ne, wallahi shi ne, ga ƙamshin turaren sa nan".

Ita ma mik'ewar ta yi ta ce.

" Ba dai saurayin ki ba?".

" Shi ne mama".

Safa da marwa Laraba ta hau yi, ta kasa yin magana.

Da farin ciki Lami ta tarbe su, kallon Ahyan da yake ta lik'ewa Amanah ta yi ta ce.

" Ina ku ka baro Jamil?".

Murmushi Jawad ya yi ya ce.

" Yana gida, ya ce a gaishe ku".

D'akin baba suka shiga, Amanah ce ta ce.

" Bari na samo muku ruwa".

Kallonta Jawad ya yi ya ce.

" No ki bar shi, kinga daga gida muke".

Murmushi ta yi ta ce.

" Okay tohm".

Ahyan ta kalla ta ce.

" Tohm ina zuwa, ya Ahyan ka zauna a nan yanzu zan dawo".

Kuka ya fara yi ya ce.

" Ni dai zan bi ki".

Jawad ne ya mik'a masa wayar sa, ya ce.

" K'arb'i ka kalli hotuna".

Kallon Jawad ta yi ta ce.

" Momma fa ta ce a daina ba shi waya".

Murmushi Jawad ya yi ya ce.

" Ba kya son ya dawo hankalin sa kenan?, ai idan a na nuna masa wasu abubuwan zai iya dawowa tunaninsa, amma idan a ka bar shi haka ba lallai ne ya dawo hankalinsa ba".

Sauke ajiyar zuciya ta yi ta ce.

" Haka ne kuma, Allah yasa ya tuna komai".

Daga haka ta fita.

Ta na fita ta ci karo da Jamila dake ta sauri, murmushi ta yi ta ce.

" Hajiya Jamila, ya kike?".

Murmushi Jamila ta yi ta ce.

" Alhamdulillahi anty, kema ya kike, ya mai jikin".

" Da sauk'i ki zo mu je ku gaisa".

Komawa d'akin suka yi ita da Jamila.

Tun da suka shiga gaban Jawad ke fad'uwa, kallon Jamila dake gaida shi ya yi ya amsa da cewa.

" Lafiya alhamdulillah".

Kallon shi ita ma ta yi ta ce.

" Kai Jay".

Kallon zargi Amanah ta yi musu, ta ce.

" Kun san juna ne?".

Shafa kai Jawad ya yi ya ce.

" Maybe ta sanni amma ni ban santa ba".

Dariya Jamila ta yi ta ce.

" A wayar anty Jummai na ga hoton sa".

Cak komai ya tsayawa Jawad ya kalli Amanah da ta dafe k'irji ta ce.

" Wacce Jummai?, ba dai ta gidan nan ba, dama saurayin ta ne?".

Mik'ewa Jawad ya yi ya ce.

" K'anwar ki ce dama?".

Tsaki ta ja ta ce.

" Wai dama duk bad'alar da kake yi da ita kake yi?, inna lillaahi wa inna ilaihir raju un".

Ita kam Jamila fita ta yi daga d'akin, d'akin Laraba ta shiga da sauri ta ce.
Chapter 12 · 0% Book details