Sashe 18
Kishiyoyin Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Sauke ajiyar zuciya Jamil ya yi ganin Ahyan ya koma sak wanda baya cikin tunanin sa, dan yasan da da tunani ba zai had'a jiki da ita ba.
Ita kam bata san Jamil yana wurin ba dan bacci ne ya kwashe ta, cikin baccin kuma ta ji Ahyan ya fad'a kanta, cikin masifa da gajiya da abinda yake ma ta ta tattaro k'arfinta ta ture shi ta ce.
" Wannan wane irin hauka ne, sai ka ringa yin abu kamar mara ilimi, na fad'a maka ni ba y'ar isa bace, mai yasa ka ke son nanik'ata ne, toh wallahi barin gidan zan yi ai ka ji sau.....".
Kafin ta k'arasa ta ji saukar mari, cikin rad'ad'i ta bud'e idon ta wanda da a rufe suke, bata sauke idon ta a ko ina ba sai a kan fuskar JAMIL wanda ya had'e rai kamar bai tab'a dariya ba.
Tsoro ne ya mamaye ma ta zuciya ta ce.
" Yayana".
Hawaye ne ke zuba a idon Jamil ya kalle ta ya ce.
" Kin cuce khadeejah, ban yi zaton haka daga gare ki ba, ya kike son nayi da zuciya ta?".
Ya fad'a had'i da dafe saitin zuciyar sa, dake barazanar fitowa.
Kuka tasa ta ce.
" Na shiga uku, yaya dan girman Allah ka daina kuka a kaina, wallahi ban yi komai sabida na b'ata maka rai ba, ka yi hak'uri dan Allah ".
Tari ya fara ya ce.
" Khadeejah I LOVE You, wallahi da soyayyar ki zan mutu, dan girman Allah da annabi ki so ni, ki yarda na aure ki, tun da sauran numfashi a jiki na please ".
Durk'usawa ya yi har k'asa yana kuka da rok'onta.
Ita kam sandarewa ta yi a wurin ta kasa koda motsin kirki.
" Ki taimaka min please kha dee jah".
Fashewa ta yi da kuka ganin jini na fitowa ta bakin sa.
Ahyan kam kamar hoto haka ya zama domin abin ya bashi mamaki, ganin yadda Jamil ya mari Amanah.
Tab'a fuskarsa ta hau yi tana kuka da magana.
" dan Allah yaya ka tashi, dan Allah".
Bata bi ta kan Ahyan da yak'i taimakawa Jamil ba ta yi waje da gudu.
Dube-dube ta hau yi, a cikin mak'abarta, ganin babu mai kallon ta yasa ta hak'a wani sabon kabari ta saka hannun ta a ciki, can ta ciro hannun tare da wani abu a cikin kaskon k'asa.
Kuka Laraba ke yi jin wai Lami nada ciki.
Jamila ce ta kalli mahaifiyar ta ta ta ce.
" Yanzu dan Allah mama mai yayi zafi da za ki zauna ki ta kuka haka?, ai abun murna ne ma a ce zata haihu kin ga bata tab'a haihuwa ba"
Wata ashariya mai maik'o Laraba ta dannawa Jamila ta ce.
" Na kula dama ke ba kishin kanki kike ba bare ki yi nawa, shashasha kawai mara lissafi".
Tashi Jamila ta yi ta fita daga d'akin dan tasan in dai mama ce bata ji bata gani akan sharrin da take yi wa Lami.
AFTER FEW DAY
Tun da suka dawo daga hospital take son cewa zata tafi gida, domin bazata iya zama a gidan da mutum biyu suke son ta ba, ga shi Jamil har ya kamu da cutar da ke ba razana da rayuwar shi.
Momma kam shiryawa ta yi domin zuwa gidan Affah ta ci masa mutunci.
AFFAH
Goya Bawo ya yi, ya na ta zagaye gidan da ita a baya.
Ji suka yi kamar an dirgo gidan, da sauri JAWAD ya kalli JUNAID ya ce.
" Wacce k'wailar ka kira?, kar fa garin neman matan da kake ka d'auko mana aljana".
Dariya ya yi ya furzar da hayaƙin sigarin bakin sa ya ce.
" Hmmm Ai ni na fi k'arfinta wallahi, sai dai ta nemi wani, wai ka san ma mai ya faru kuwa?".
Kafin ya bashi amsa ya ji an shak'a masa abu a hanci, to second 10 bai yi ba ya sume.
END OF BOOK 1
KARKU MANTA DAMA GAJEREN LABARI NE
MAI BUKATAR JIN YADDA ZA TA KAYA YA BIYA 400 IDAN YA ZAMA COMPLETE ZAN MAYAR DA SHI 500
08136243611 NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM OPAY
✍️NUSAIBA MUHAMMAD IBRAHEEM AMINIYAR JAJIRTATTU