Sashe 59
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/22, 8:04 PM] Oum Hairan: Da mugun gudu cikin fitar hayyaci Juhud ta fito daga dakin da take cikin gigita ta cacumi Rasheed dake shigowa idanunsa kamar garwashi ta jijjigashi tace da gaske ko gizo kalamin Ya'isha sukemin Ya Kareem ya mutu....." Zubanta idanunsa yayi so yake yayi mata mgn ya kasa sai kawar dakai da yayi hawaye suna zubo masa yasa hannunsa ya janye nata, ganin yanda yake goge hawaye da tissue yasata zama a gurin dabar ta daura hannunta akanta ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un" Ya Kareem kada ka mutu dom girman Allah ya kasance mafarki shudadde Wanda bazan qarayinsa ba har abada wlh na aminta da kai zan dawo gareka na qara Haifa maka qannen Muneefah nasan shin....shine burinka a duniya....." Dagota Mom tayi tace kiyi hqr Meenah shirya mu tafi" Babu wani shiri ta sunkuci Muneefah da taketa bacci abinta baccin asara abin tausayi mota ta debesu gabadaya harda Alh Garbu suka nufi airport dake abin na manya ne nandanan suka Isa Nigeria kamar a qasar suka kwana goma na safe suka shiga Daura lkcn an gama shirya Kareem da Zahrah zaayi musu sallah mazan suka tsaya wajen jana'izar sukuma suka shige ciki. Addah Abulle tana ganin Juhud ta miqe ta nufeta da sauri ta karbi Muneefah ta rungume ta qara rushewa da kuka tace shikenan ya tafi Meenah yatafi yabar Mana duniyar Babu shi din Babu Zahra wayyoh Kareem dama inada dama Dana dawo dakai duniya nabarka da zabinka da yarka daya mafi soyuwa a ranka kullum kana fadamin bakajin dadin rayuwa baka tare da Muneefah ashe ita kadaice rabonka ita zaka tafi kabarni da ita Kareem wayyoh Ni Zainabu na cuci kaina na cuceka Kareem Allah na gde maka da bakabani saa ba lkcn da malam Mati yabani magani yace nabaki kici a waina da tuni Babu Aishatu da tuni Ni da kaina na kashe bayan dana kaicona Ni Zainabu Allah ya isa Dada Hanne da Hajiya Bilki kune kukayita dorani a keken bera ashe kaini zakuyi ku baro yau na rasa Kareem ban barshi ya rayu da farin ciki ba ya tafi da jin ciwon nice silar rabashi da matarsa mafi soyuwa a duniyarsa...." Surutai taketayi kamar wacce ta zautu hakan yasa wasu mata daga cikin danginta sukazo suka kamata suka tafi da ita daki tana kuka tana kiran Meenah Kareem shikenan Kareem ya tafi yabarmim duniyar Ina nutsuwata da hankalina yayi na kasa gane nauyin qaddararsa?" Kowa ka gani a falon kuka yakeyi mutuwar Kareem tabar tambari ba iya Daura ko Katsina kadai ba hatta arewacin Nigeria baki daya duk Wanda yaji labarin mutuwar ko baisanshi ba sai yaji alhini a jikinsa duniya tayi rashin nagartaccen mutum me hqr da kawaici kunya da kara wannan dabi'ar tasa yake soyuwa a zuciyar duk wanda yayi mu'amala dashi ta kusa kota nesa ranar anyi yinin alhini Juhud kam zazzabi ne ya rufeta sosai bana wasaba hawaye yaqi tsayawa a idanunta tayi danasanin zabar Rasheed akan Kareem ta zabi Rasheed tabar Kareem Rasheed din ya tattarata yayi watsi da ita yaqi saurarenta. Haka suka yini yinin koke da dare kowa ya nemi guri ya kwanta itakam koda ta kwanta kasa rintsawa tayi rayuwarta da Kareem zamantakewarsu da yanayin salon qaunarsa me tsayawa a rai shudaddiya wacce bazata dawo ba tanayi mata yawo a kwanya saidai kawai lkc zuwa lkc ta dauke hawaye, wajen 10:30 taji ana taba qofar dakin data shiga ta kulle kanta ta miqe a wahalce ta bude ta dan ja da baya a tsorace ganin Rasheed ne jajayen idanunsa akanta ya miqa mata Muneefah da tayi bacci tasa hannu ta karbeta ta juya ta nufi cikin dakin taji muryarsa data shaqe da alamun yaci isasshen kuka yace Duk da bansan irin radadin da kikeji a zuciyarki ba na rashin masoyinki uban yarki nasan kinajin fiye da abinda nakeji tabbas akwai daci daci mafi dacin daci rabuwa da abinda kakeso a lkcn da kake tsananin buqatarsa yaune kika farajin kwatankwacin abinda naji lkcn dana rasa hanyar dawowa gareki kwanyata ta daina fadamin daidai aka rinqa nunamin ke cikin wani yanayi dana kasa ganewa har yanzu and end aka nunamin ke wani mutum ya hankadaki cikin wani dogon rami Wanda na yanke shawarar binki mu mutu tare Meenah bayan na biki bansake sanin komai da hankali zai tuna ba sai bayan shekara bakwai dinnan Amma ko a cikin yanayin zautuwar qwaqwalwata ban mantaki ba duk wani furucina kece bansan ya ake tunani ba Amma idan na zauna kece kikemin gizo da siffofi mabambata" Numfashi ya sauke ya juyo idanunsa na zubar hawaye yace meye kike tunani ranar da Allah ya Amsa addu'ar masoyana ya dawo dani hayyaci na laluba naga bakinan na tambayi kina Ina akacemin kina matsayin matar wani waninma qanina Meenah taya zan iya yafewa kaina bata lkcn da nayi na nakasa rayuwata saboda ke? Nakasa yafewa kaina kema na kasa yafe miki girman cin amanar da nakeji a Raina kinyimin domin bana mantawa kintaba yimin alqawarin zamu rayu tare zamu mutu tare ya akayi tun Ina raye kika zabi rayuwa da wani bani ba?" Duk da kalamansa sun kashe mata jiki Amma yanayin da take ciki yasata juyowa a fusace tace qaddara Abdulrasheed dukkanmu akanta muke rayuwa Babu Wanda ya isa ya tayani dakon tawa kamar yanda Babu Wanda ya tayaka Babu Wanda ya taya Ya Kareem Allah madaukakin Sarki ya sardanta ku biyun daka kuna cikin qaddarata kaine kakeja da lamarin ubangiji ni bana jayayya Ya Kareem ma baitaba jayayya ba kullum nunamin yakeyi bayin kansa bane girman rabone da hukuncin Allah saiya Sanya Muneefah tsakaninmu Kuma na dade da sanin tun baya ma shine akan daidai kai kana rayuwa ne a doron son zuciya saboda haka Baffa'am tun da sauran mutuncinka a idanuna ka fice cikin rayuwata kafin na keta alfarmarka na shiga nayi fata da qimarka Meenah daka sani a baya ba ita bace yanzu yanzun Aminatuh ce a gabanka me taqama da asali kyawun nasaba arziqi da ilimi kada ka manta bayan tafiyarka na samu shahadar zama Barrister Aminah Haroon Moddibo so nasan yancina banason kowa cikin rayuwata ta yanzu" Shigewa tayi daki ta banko qofar ta murda mata key ta haye gado ta zubawa yarta ido tana mata tunanin rayuwarta ta gaba babu bangonta na farko kwanciya tayi bacci ya qauracewa idanunta kamar yanda ya qauracewa idanun Rasheed sosai yake jujjuya kalamanta ya rasa a ma'aunin dazai sanyasu ta fada masa kalamai masu wahalar gogewa a zuciya tabbas shima saida ne daga yanda ta watsar dashi da lamuransa na rayuwa yasan tabbas da gaske ba Meenan daya sani a baya bace, to Amma meye yasa ita ta kasa gane tayi masa laifi me girman daya dace duk hukunci ya dauka akanta? Busar da iska yayi ya gyara kwanciyarsa tare da dauko takardar da Mai Martaba yabashi dazu dazai shigo bayan ya fito daga dakin Meenah yace Kareem ne yabashi yace abashi kafin ya rasu. Tashi yayi ya kunna haske zuciyarsa na bugawa ganin yanda takardar ta bushe da jini ya warwareta ya fara karantawa da larabci yayi rubutun fassararsa kamar haka. Assalamu Alaika ya dan'uwa mai albarka na rubuta maka wannan takarda ne a lkcn da Raina yake tafiya ga ubangijin daya halicceshi, badon komai ba saidon inason na qara baka hqr akan laifin da kake tunanin nayi maka na auren matarka Allah yasani ban aureta don cin mutumci ko tozarci a gareka ba, Ni Abdulkareem Mahfuz na zabeka na mallaka maka amanar yata qwaya daya tilo ta zama taka dama nasan takan ce don Allah Abdulrasheed kada kabari Meenah da Muneefah suyi kukan rashina musamman Muneefah ita kadai gareni Kuma na mallaka maka ita halak malak"_ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/23, 7:30 PM] Oum Hairan: Matse takardar yayi a tafin hannunsa jikinsa Yana tsuma zuciyarsa nayi masa wani zugi ya miqe a gadon ya rinqa zagaye dakin nasa a tsarinsa na gaskiya ji yakeyi kamar bazai iya sake zama da Meenah ba yanajin ciwon abubuwan da suka faru a baya so yanzu ya zaiyi da wannan nauyin da Kareem ya dora masa a halin yana gargarar mutuwa? Tambaya ce da yakasa amsawa kansa ita dole akwai sarqaqiya cikin wannan al'amari komawa yayi ya kwanta ya kasa bama kansa mafita sai zafi da zuciyarsa takeyi kawai. Abu daya da yasan ya zame masa dole shine daukar amanar Muneefah da Kareem ya damqa masa to Amma ta yaya zai karbeta a gurin mahaifiyarta bayan yasani yanajin yanda shaquwa take tsakaninsu ko giyar wake Meenah tasha bazata bashi yarta ba, da wannan tunanin ya samu bacci ya dan daukesa da safe yana fita falo ya ishe kowa suka gaisa yanata raba idanun ganin Meenah Babu alamarta hakan ya tabbatar masa tana dakin daya isheta jiya yaja fasali ya dubi Amrah yace shiga ki daukomin Muneefah" miqewa tayi ta nufi cikin dakin ta tarar Meenah tayima yarta wanka tanayi mata kwalliya ta zauna suka gaisa tace Big Cele yace akawo masa Muneefah" Bataso ba saidai batada ikon hanawa ta gama shiryata Amrah ta riqema yarinyar hanu suka fito ya dauketa suka fice daga falon Mom tana kallonsa batace masa komai ba, kwanaki bakwai din da Meenah sukayi suna karbar gaisuwa ta fahimci abubuwa da yawa sosai Addah Abulle tayi laushi batada aiki sai kuka tunda ta haifi Muneefah bazata iya cewa ga ranar da Addah ta dauki yarinyar ba sai cikin kwanakin nan da taketa nan nan da ita danma Rasheed ya hanata sakat akan yarinyar duk wani motsin da Muneefah zatayi tana gareshi. Kwanaki goma da rasuwar su Kareem bayan komai ya fara nutsawa Meenah da Kumbo Hami suka fara Shirin tafiya Rasheed baisan me akeyi ba sai a daren da zasu tashi Mom ta kirasa lkcn bai dawo daga yawonsa ba