Sashe 35
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata jiki ko Kuma hakanan ya dauki fushi da ita ya yini baiyi mata mgn idan ma zata biye masa sai su kwana babu me cewa wani Amma hakan baya hanashi tumurmusata. Yau ta kama daren lahadi ne gobe litinin take shirye n komawa aiki tun safe taketa aiki a kitchen soya wannan kwashe soya wannan duk dominsa tana aikin ne da qarfin hali kasancewar tafi wata sati guda tanajin wani baqon yanayi a jikinta ta gama soya masa nama kenan wani zazzabi me zafi ya rufeta dole ta hqr da aikace aikacen ta gyara kitchen din ta nufi dakinsu ta shiga bathroom tayi wanka ta dawo ta shafa mai tasa kayan bacci ta duba agogo goma harda rabi taja numfashi yanzu sabuwar dabi'arsa kenan idan ya fita sai yakai 12 bai dawo ba daya shigo zai fara ciccin magani Yana fuffuskewa don kada ta tambayeshi. Hayewa gado tayi bayan ta watsa paracetamol ta kwanta ba baccine ya dauketa ba sai wajen 11:30pm lkcn daya dawo zazzabin ya sauka sai rashin kuzari hakanan ta daure ta tashi ta nufo falon ta tsaya jikin makarin benen ya juyo suka hada ido gabanta ya fadi lkcn da idanunta ya sauka a kuncinsa hoton bakin mace ne radau yasha jambaki, ganin kallon da takeyi masa ne yasashi shan jinin jikinsa ya fara caje kansa ta juya zata haura saman ya cafko hannunta yace Meenah meye Kuma hakan?" Dagowa tayi idanunta ya ciko da hawaye tace babu komi Baffa'am ka sakeni...." Saurin sunkuyar da kansa yayi zai dora bakinsa a nata ta fizge da qarfin da batasan tanadashi ba ta kwasa da gudu ya kuwa tsaya sake da baki yanabinta da kallo, tabe baki yayi ya nufi saman ya shiga dakin ya hangeta ta qudundune a gado sai rawar sanyi take tanata gursheqen kuka ya nufota da sauri ya hauro gadon yace Oh God Meenah meye Kuma nayi miki ne din Allah yini nayi fa bananan bare kice na takura miki ko baki da lfy ne naji jikinki da zafi" dagowa tayi ta sake kallon fuskarsa sai ta Kuma fashewa da kuka tace kaje Baffa'am kaje banson ganin fuskarka don Allah meye ne na gaza maka nikam bansan wanne irin miji Allah yabani kai ba baka ganin qoqarina baka yabamin duk da rashin sabona Baffa'am ban isheka ba saika nemi matan banza Allah na dade Ina qyamar zina meyesa ka jarabceni da miji Mazina....." Damqar wuyanta yayi a nufinsa na kare kansa yace ke banzar inace da zaki kalli idona kicemin mazinaci ni kike cewa mazinaci Aminah kawai don kinga Ina qyaleki?" Cikin kuka tace qarya nayi Baffa'am am sau nawa Ina ganin condom cikin kayanka sau nawa ina ganin jambaki jikin kayanka idan nayi maka mgn kacemin nacika zargi idan baka bani qofa ba meye yasa zanyi zarginka bayan nasan banida duniyar data fika a wannan duniyar meye yasa zaka ke munafurtata kake zagayeni kana tafiya gurin wasu....... Baqar zafin zuciyarsa yasata dauketa da wani mari daya sata fadawa daga gadon ta kifa akan hannunta ta rintse idonta ta saki wata qara me sauti ya miqe a fusace yace an nemi matan kudinki ko nawa burarki ko tawa banza dake wawuya da batasan yanda zata tafiyar d rayuwarta ba......" Mgnr ce ta maqale lkcn daya dora idanunsa a madubi yaga shatin bakin Fannah radau akan kuncinsa nandanan Kuma jikinsa yayi mugum sanyi ya nufota da sauri kafin ya iso ta miqe tana layi waje riqe da hannunta ya biyota da sauri Yana kiranta Fadi yake Kinga Aminatuh tsaya kiji bafa abinda kike tunani bane....." Ai kamar wacce take tafiya da iska yaga ta kama katangar quarters din ta haura Yana Isa tana dirawa ya dafe da sauri Yana kiranta ya dira qasan tuni ta miqe ta zuba a guje tana kuka daqyar da taimakon wani sojansu daya fito shima yawon ta zubar dinsa ya samu suka cimmata ta zube a gurin tana wani irin kuka me cin zuciya da Sanya nadama. Yana isowa ya tsugunna gabanta yakai hannu ya riqe hannunta ta saki qara ya saki da sauri yace me kikeson aikatawa ne a wannan tsohon daren Meenah Ina zakije a garin nan waye kika sani" cikin kuka da shaqewar murya tace najema na mutu mota trailer tabi takaina Mana Ina ruwanka meye asararka banida wani Wanda yayi asara don na mutu kaima bakada ita tunda kanada karuwanka wlh tallahi Bazan iya zaman aure da qazamin mutum irinka ba iyakar wuya zan jure Amma banajin qasqancina yakai na zauna da mazinac....." _Assalamu alaikum_ _Masoya na masu son littafaina nice dai Oum Hairan nazo domin sanar daku abinda ke faruwa. Am akwai wasu mutane Dana samu suna tura maku book dina da nakeyi yanzun wato _Juhud suna cewa daku ku biya 100 su rinqa turo muku har sunace maku sudin agent dinane wasunku Kuma saboda son bulus suna tura musu kudi a qarshe suyi block naku batare da sun baku littafin ba._ _Nidai nasani Kuma kusan duk Wanda yake bibiyata yasani tun shekara uku baya number na daya ne a WhatsApp wato wannan._ _09013718241_ _Indai kika tura kudi a akasinta to ke kikaso su damfareki sannan littafin Juhud ba 100 bane 300 ne VIP 600 idan kinada ra'ayin biya ki tura ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin waya MTN ta number dake sama vtu Kuma ta wannan 09031307566 saiki tura screenshot na biyanki a wannan number_ _09013718241_ _Na gde_ _Taku_ *_Oum Hairan_* [7/31, 8:47 PM] Oum Hairan: *JH0023* Dafe kansa yayi a fili yace oh God ciwon kai Meenah naji tashi muje kiji fah ni bama abinda kike tunani bane" daqyar ya samu ya lallabata suka shiga ciki ta qofar baya suka shiga quarters din Yana riqe da hannunta suka shiga ciki ya rufe qofar ya saki hannunta ta fada kujera ta kwanta yayi murmushi yace Meenah kishinki yayi yawa bansan meye kike kishin ba kullum cikin tuhumata kike meye yasa kike zargina ne?" Lumshe idonta tayi taba banza ajiyarsa yasan tunda tayi haka bazai samu arziqin mgn ba dole ya haye sama ya cire kayansa ya watsa ruwa ya dawo ya dauketa cak suka haura saman har yanzu a sama take dashi bata bashi fuska ba Ganin hakan yasashi shima ya qyaleta da asuba kuwa Yana shafawa yaji Babu ita ya bude idonsa yaganta saman sallaya ya miqe yayi miqa yayo alwala yazo ya tada sallah. Kitchen ta shiga ta dora tea yanzun bata jure yunwa jikinta har rawa yakeyi ta dafa Indomie ta fito. Jerawa tayi a dinning ta zauna tanacin Indomien ya sauko sanye da doguwar riga bata dagoba balle yasaran zata kallesa yaji babu dadi sosai hakanan ya zauna ya zubanta ido sun hada ido yakai sau biyar sannan tace masa morning" zuciya yaja yace kin tashi lfy" bata bashi Amsa ba ta hada tea dinta ta fara Sha ta miqe zatabar gurin ya riqota ta juyo ta zuba masa manyan idanunta baisan sanda ya saketa ba tabar gurin. Duk jikinsa yayi sanyi baison ganinta cikin damuwa miqewa yayi yabi bayanta tana tsaye a tsakiyar dakin sai kaiwa da kawowa takeyi ya jingina jikin qofar ya kira sunanta ta tsaya Amma bata juyo ba takowa yayi ya tsaya a bayanta suna kallon juna ta madubi ya shafa gemunsa ya nemi guri ya zauna yace bawai fushinki ne yake damuna ba not akan abinda kike fushin shine yake damuna nifa ba abin da kike tunani ne yasa....." Dagansa hannu tayi tace na tsani qarya a rayuwata wlh bazan iya hanaka ba domin bani na dora maka ba kaine ka dorawa kanka kawai abinda nakeso ka fitarni a lissafinka ka qyaleni nayi rayuwata kayi taka. Da sauri ya dubeta kamar zaiyi mgn sai Kuma ya miqe yace ok" daga haka wata kalma bata kuma shiga tsakaninsu ba har ya gama shirinsa ta hada masa kayansa ya dauki jakarsa yace zan tafi" batare da wani basa muhimmaci ba tace Allah ya tsare ya taimaka" kudi ya zaro ya aje mata ya juya Yana tafe Yana cewa banida isassun kudi a hannuna ki riqe wadannan ba dadewa zanyi ba kafin bikin su Ya'isha zan dawo" Yana fadin haka ya fice da sauri saboda karyar masa da zuciya take neman yi itama jikinta yayi sanyi sosai tabisa da kallo tana hangensa har ya fice daga quarters din ta zauna tana saqawa da warwarewa can dai taga bazai kaita ba ta shiga daki ta kwanta. Kasancewar ita kadai ce bata tashi a bacci ba sai yamma tayi wanka ta tafasa taliyarta da bushasshen kifi taci ta kora da lemo ta miqe ta lalubo wayarta zaro ido tayi 7 missed nasa tana Shirin kiransa ya sake Kira ta Kara a kunnenta yace kina bacci ko?" Murmushi tayi tace eh na tashi naga missed naka Ina fatan ka sauka lfy" Amsa mata yayi sukayi shiru na dogon lkc can yace fushinki gareni Yana azabtar dani Meenah kiyi hqr don Allah" a kasalance tace yafa wucce Baffa'am kawai dai Raina baya dadi ne idan na tuna kana raba Mana Abu mafi daraja da wasu wadanda basu cancanta ba. Yaji dadi sosai sukaci gaba da hirarsu har zuwa wani lkc sannan sukayi sallama cike da kewar juna tana kashe wayar wayar Amrah ta shigo ta daga shigo ta dauka daga yanayin yanda suke gaisawar tasan da wani saqo a zuciyarta Amma ta maze taja numfashi tace burinki ya cika hankalinki ya kwanta kin yaudareshi kin Sanya masa ciwon zuciya kawai saboda wani quduri naki Meenah Ya Kareem bai cancanci wannan sakayyar daga gareki ba yasoki lkcn da bakisan komai ba shine yanzu dan kin zama komai kika gujeshi......" Dakatar da ita tayi da cewa kina mgn da yaen da bana ganewa Amrah meye ma laifina ne cikin zarginki nima kamar yanda kowa yaji sama taka hakanan naji bansan wani abu bayan abinda kuka sani ba nidai na wayi gari naganni matsayin matar Baffa'am dina Kuma na yarda da abinda Allah ya tsara na karbeshi to meyece tawa a ciki?" Wata dariya Amrah tayi tace bawai inayi miki mgn don kaina bane domin ni da eh dinki da aarki babu abinda zata qaramin Amma dai ki sani baki auri mijin daya dace dake ba domin kuwa ya rainanki hankali ne kawai saboda sha'awa ya aureki Kuma