← Book details Juhud Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 64

Sashe 43

Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya tarkato Sarki. Ana haka Mai Martaba yaga zaman ya fara tsayi Abu ya tafi shekara biyu ya Sanya Kareem ya nema mata admission bayan sun biya mata an zana mats jamb lkcn da sukayi mata mgnr karatun fir qi tayi tace ita bataso daqyar Mom da Kareem sukasha kanta ta yarda ta fara zuwa Alqalam University Katsina bata jima da fara zuwa ba abubuwa suka fara canzawa Dada Hanne da Alh Aminu suna zuga Mai Martaba baiyi furuci ba Amma gabadaya ya janyewa Meenah tallafi babu Wanda yasan dalili Mom ce taci gaba da dawainiya da karatun nata ita da Kareem. A hakadai da dadi babu dadi take gurgura karatun cike da samatsi da qalubalen rayuwa kullum addu'a takeyi Allah ya bayyana mijinta itama ko ta samu hasken zuciya. Yau da gobe ce tasa Kareem bawa Mom shawarar kama mata hostel saboda karatun nata na Law yanajan kudi sosai hakan kuwa akayi suka kama mata hostel ta koma can da zama Sarki junior na gurin Mom yanata girmansa inda a lkcn Ya'isha ta ta haihu Zahran Kareem ma ta haihu taso zuwa daidai lkcn suna exam hakanan ta hqr sai bayan Exam akayi hutu ta shirya domin zuwa tayi barkar ta nufi Daura cike da kewar gudan jininta da sallamarta ta shiga falon Sarki ya taso da gudu ya rungumeta ta dagashi tana juyashi suna dariya tayi kissing nasa tace miss you love inata kewarku" Lakace mata hanci yaran me shekaru hudu yayi yace yaushe zaki dawo?" Narkar dakei tayi tace saura semester guda Son ka matsu na dawo ne?" Turo baki yayi yace Addah Fadila ce tacemin na daina zuwar mata gidanta kada na cinye mata su Jabir Momy wai tace kece kika cinye Dad Ina ya bata....." Gwabe bakinsa Mom tayi tace ba nace maka idan na qarajin mgnr nan a bakinka saina yankaka ba" riqe bakinsa yayi alamun yayi shiru ta daukeshi jikinta a mace ta nemi guri ta zauna suka gaisa da Mom ta miqe tace zanje nagano babyn Ya'isha" miqewa itama tayi tace nima abinda ya kawoni kenan hutunmu na sati daya ne Kuma tun shekaran jiya akayi" dungumawa sukayi suka fita suna fitowa Muntaz na shigowa Mom tace yawwa zo ka kaimu gdan Ya'isha" Babu musu yaja suka tafi suna taba yar hirarsu tace Jiya Hafeez abokin aikin Baffa'am yakaimin ziyara" murmushi Mom tayi tace nan ms yazo gurin Mai Martaba yazo ne da wani shirme wai qa'ida shekara hudu ne idan mijin mace ya bata alqali zai bata damar tayi aure ke anbaki dama ne? Tsaki taja me zafi tace shege sai naci kutumar ubansa ni ce masa akayi mijina bazai dawo bane nifa Mom bantabaji a Raina Baffa'am ya mutu ba Yana raye kawai dai Allah ne be gama ganawa ba" numfashi Mom taja tace nima haka nakeji so naga Mai Martaba ya saduda shiyasa nima na fidda rai da tsammani" shiru ce ta dan gifta suka Isa gdan Kareem ta jinjina haduwar gdan karo ns farko data sanya qafarta a gdan tun aurensa da Zahrah kasancewar Zahra mugum baqin kishi takeyi da ita to itama shiyasa taja jikinta. Da sallama suka shiga aka Amsa musu Dada Hanne na dagowa taga Juhud tayi maza ta dauke jaririn tasa a bayanta suka gaisa tayima Zahrah barka tana amsawa a yatsine ta aje kayan data siyowa bebin tana satar kallonsa a bayan Dada tanason jariri a rayuwarta bata samu arziqin daukan jaririn ba Kareem ya sauko tunda ya fito idonsa na kan Juhud dake wasa da yatsunta yace aa Meenah Ina cewa zanzo na daukoki ashe kina hanya" murmushi tayi masa tace wlh na matsu nazo naga baby's din da muka samu shiyasa na biyo motan haya" shafa kansa yayi yace insha Allahu cikin satinnan motarki zatazo haihuwar nan cema ta dan takemin birki" gdy tayi ta miqe saboda bata cikason zaqewa a lamarinsa ba ganin haksn yasa Mom miqewa sukayi sallama ya biyosu har jikin motarsu yanajan Sarki da wasa suks shiga suka tafi shikuma ya juya suka nufi gdan Ya'isha......... Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/6, 10:48 AM] Oum Hairan: *0029* A gdan Ya'isha suka shantake sunata fira Basu suka baro gdanba sai gefin magrib suna shiga gdan gaban Juhud ya fadi batare da tasan dalili ba suka nufi parlourn da sallamarsu a tsaitsaye suka tarar da Addah Abulle da Fadila Juhud na Shirin mgn taji an shaqeta ta baya batare da sanin waye ba suka rinqa kokawa daqyar Mom da Muntaz suka rabasu Fadila na huci ta nuna Juhud da ta zubanta ido tace muguwa azzaluma Ni dama tunda akace kinje barka nasan ba Alkhairi ne yakaiki ba ace daga zuwanki jaririya ta kama cuta kwana uku da haihuwarta batayi ba sai yanzu da kikaje to wlh ki sakar Mana kurwar yarinya ko mu aikaki lahira shegiya baqar kadara" Cafewa Addah Abulle tayi da cewa to waima meye yakaita barkar waye yace Yana buqatar barkarta gsky nikam wannan lamarin na gdannan ya isheni Abu ya wucce kan wadanda suka jajuboki ya dawo kanmu shekara uku dayin auren nan baa haihu ba shine daga kinji an haihu zaki lashe musu ya tab wlh bazai yuwu ba dole ma Mai Martaba ya zaba a gdannan ko mu da muke dolensa ko Kuma ita da suka liqawa mutane" tunda suka fara mgn ta fahimci inda suka dosa jikinta yake rawa hawaye ya kasa tsayawa a idanunta mgn takeson yi Amma bakinta ya sarqe zuciyarta wani zafi takeyi hakanan takejin a ranta yau ko zata fita a kasheta sai tabar gidan lamarin ya fara wucce yanda zuciyarta zata dauka. Juyawa tayi ta shiga dakin da take taja akwatu ta fara hade takardunta tana wani irin kuka me ciwo itakam tagaji da wannan quntattaciyar rayuwar shekaru ashirin da biyar na rayuwarta ta qaresu a qunci shekaru tara Mom na hadiyar baqin ciki akanta meye yasa bazata gushe ba kota samu salama da sanyin ruhi suma masoyanta su samu? Tanayi tana jan zuciya tana tunano yanzu hakanan zata fice tabar gudan jininta daya tal a duniya meye makomar rayuwar Sarki idan ta tafi ta barsa? Dagowa tayi bayan ta gama hada kayan ta zuge ZIP din trolley din ta miqe ta dauki hijjab dinta ta zura taja akwatin takai hannunta zata bude qofar Mom ta bude ta shigo idanunta na tsiyayar da hawaye tace duk wani abu daya kamata nayi miki Meenah nayi miki domin Allah meye yasa qaramin Abu yakesaki jin tafiya kibarni shine mafita? Me kikeso nacewa Rasheed idan Allah ya bayyanashi yaji abinda kika aikata? Haba Meenah nidai Ina ganin indai kika yanke barina to tabbas baki biyani haqqina ba Kuma kin basu damar yimin dariya ne......." Wani kuka ta saki me ciwo tare da durqushewa ta kifa kanta jikin akwatin tanayinsa babu furuci kalma batada ita a bakinta da zata iya furtawa zama Mom tayi tana bata baki tana rarrashinta Amma kamar tana zugata, aka bude qofar aka shigo Mai Martaba ne ya shigo fuskarsa Babu alamun wasa yace ke Aisha tashi ki bani guri inason mgn da ita" miqewa Mom tayi ta fita tana kallon Meenah data dunqule tanata aikin kuka ta girgiza kai ta fice daga dakin ya nemi guri ya zauna Yana nazarin yarinyar da yanda duk jikinta ke rawa jikinsa yayi sanyi shi kansa yanajin kunyar kansa irin biyayyar da yarinyar takeyi masa bata cancanci haka daga gareshi ba ta daukeshi kamar mahaifi tanayi masa biyayya fiye da yanda yayan daya Haifa sukeyi masa to waima meye yasa yake yarda da jita jita akanta ne?" Gyaran murya yayi yace ina kike Shirin tafiya yanzu?" Cikin kuka tace inda ubangiji ya kaini don girman Allah karka hanani Mai Martaba na gaji wlh na gaji da qaddarorin nan masu wahalar dauka inaji a jikina banida wani rabo na farin ciki a rayuwata Mai Martaba idan ka hanani zan rasa kaina zuciyata zata buga....." Jinjina kai yayi cike da tausayawa yace meye yasa kika yanke wannan hukuncin?" Dagowa tayi idanunta akansa bakinta ba rawa tace Baffa'am shine mutum na farko dayayimin gata ya zabi farin cikina akan komansa Mom ta dora sunci baqin ciki akaina sunama kan ci wlh koda bana tare da mijina inaji a jikina duk inda yake hankalinsa yana gareni Mai Martaba bazan zama silar bacewar da na zama silar macewar uwa ba idan naci gaba da zama da Mom baqin cikin abinda ke faruwa Dani zai iya taba tata rayuwar nikam na riga na zaba na yankewa kauna da samun wani jin dadin rayuwa kubarni naje na rayuwa ni kadai abinda kukayi a baya na gde....." Daganta hannu yayi yaja zuciya yace naji Meenah ki cire wannan tunanin a ranki Babu inda zakije kinanan" miqewa yayi ya fita daga dakin yana fita ta koma ta kwantar da kanta jikin gado tana wani kuka me ciwo, tana jiyo hayaniya da fadan Mai Martaba a falo saidai bata fahimtar meye yake cewa sama sama taji yana cewa ni na haifi Rasheed na haifi Kareem dukkansu ikona ne duk da qaddara tasa Meenah bata zama mallakin Kareem a farko ba hakan bazai zama hujja ta cin mutumcinta ba wlh tallahi Zainab duk ranar da wani abu makamancin wannan ya Kuma faruwa zakisha mamaki na Kuma babu wanda ya isa hanani zartar da abinda nayi niyyah a gobe juma'a zan yanke abinda nayi niyyah kai nama fasa yau dinnan idan da Wanda ya isa ya Hana" Bata fahimci komai ba Amma sosai taji wata faduwar gaba ta darsar mata ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta damuwa tasa zazzabinta na qa'ida ya dirar mata wanda likitoci sukayi ittifaqin zai iya haifar mata da ciwon zuciya saboda Yana yawan kumbura zuciyar tata. Bacci ne ya dan dauketa sama sama kasantuwar ba sallah zatayi ba tanaji ana Kiran sallar Isha a masallacin Fada ta sake gyara kwanciyarta bacci me nauyi ya dauketa batasan meye yake faruwa ba sai ji
Chapter 43 · 0% Book details