← Book details Juhud Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 64

Sashe 18

Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin zabura tayi ta miqe a hargitse tana waige kamar ance ta daga kanta sama ta hango Baffa'am dinta tseye shima ya zubanta ido fuskarsa babu alamun haske ko annuri mamaki ya cikata a tace yaushe ya dawo?" Baita samu amsar abinda take nema ba Kareem yasha gabanta ya tsugunna yace malaminki yana neman taimakonki Aminatu don Allah kada ki wofintar dani nasan har yanzu babu kowa cikin zuciyarki shiyasa nayi gaggawa wajen furta miki abinda Raina ya qunsa" Sake kallon inda Rasheed yake tsaye tayi har yanzu ita yake kallo ta janye hannunta daga riqon da Kareem yayi mata ta nufi step din upstairs din da sauri zuciyarta na bugawa da qarfi kafin ta qarasa taga ya juya ya shige dakinsa ya danno qofar da qarfi daidai lkcn ta qarasa ta shiga qwanqwasa qofar tana cewa yau nafi kowacce ya saa Baffa'am ashe idan mutum Yana mafarki gani yakayi wayyoh dadi baffana ya dawo gareni, please budemin na kwashi tabarraki kasamin albarka My lovely Dad......" Yana tsaye jikin qofar yanajinta qirjinsa na harbawa da qarfin dashi kansa baisan dalilinsa ba so yake ya bude mata ya kasa saboda wani tuquqi da zuciyarsa takeyi masa yayi danasanin fitowa a daidai wannan lkcn duk da baisan meye Kareem ya fada mata ba Amma yanayinsu ya nuna wani sashine me muhimmaci sukeson wanzarwa. Zama yayi saman gadonsa jikinsa Yana wata irin rawa a hankali ya furzar da iska me zafi yace meye yake fada miki Meenah?" Miqewa yayi zunbur ya bude qofar har ta hqr ta juya jikinta a sanyaye abinka da me qoramar hawaye ta fara fitar da qwallah taji ya bude qofar ta juya da sauri ta nufesa a guje ya bude mata hannu me Kuma ta tuna saitayi turus a gabansa idanunsu na sarqe cikin na juna hakanan taji sautin bugun zuciyarta yana nunkuwa ta kama hannunsa ta tsugunna saita rushe da kuka abinda ya qara tashin hankalinsa yasa hannu biyu ya dagota yasa yatsansa Yana share mata hawayen har zuwa lkcn zuciyarsa tafasa takeyi burinsa kawai yaji meye Kareem yake fada mata harta bashi attention haka data kasa jin kiransa ta kasa ganinsa? A kasalce ya hadata da jikinsa qirjinta ya tokare nasa yaja wata ajiyar zuciya me qarfi yanajin wata nutsuwa na saukar masa yace miss ur My Meenah" dagowa tayi hawaye nabin kuncinta tayi murmushi ta sake saqale bayansa tace shine Saida ks batamin farin cikina Baffa'am kasan irin wahalar da nasha kafin na saba da rashinka kuwa meye yasa ka ja zuciyata a qasa harna fara tunanin ko na bataran haskena?" Inda kalamanta suka nufa daban inda yakaisu daban janyeta yayi ya zauna a qasa itama ta zauna yace meye Kareem yake fada miki me dadi haka da har ya dauke miki hankali kusan 30 minutes Ina tsaye akanku Amma baku sani ba?" Rufe fuskarta tayi tana dariya sokuwar tace nifa Baffa'am bansan meye yake nufi ba wai Yana sona kuma son aure hakams Saleem yace da Ya'isha nikam bana kulasu ma cewa nakeyi suje su sami Baffa'am dina namasan bazakayimin aure ba ko........." Wani ihu yayi daya ja hankalin mutanen dake falon qasan gabadaya ya miqe ya shaqeta jikinsa na tsuma ya kasa mgn sai wani turiri da bakinsa yakeyi haqoransa suna haduwa da gudu Mom ta nufo saman ta riqeshi tana cewa na shiga uku ni Aishatu Abdulrasheed meye Kuma yarinyar nan tayi maka daga dawowarka ko hutawa bakayi ba...." Da ihu yace So Momy sonta fah yace yanayi Kuma har take iya fadamin wai yanasonta Nawa take Mom irin riqon amanar taku kenan har damar soyayya kuka bata injiwa? Waye yabaku wannan damar?" Daqyar suka bambare Juhud daga hannunsa yayi watsi da ita baijira cewar kowa ba ya fada dakinsa ya doko qofar da qarfi hada kansa da bango duk wata qofa ta gashi a jikinsa ta miqe idanunsa ya kada yayi jawur zuciyarsa kuwa kamar ta faso qirjinsa haka yakeji. Mom ce ta dagota idanunta gabadaya sunyo waje saboda ba shaqar cigaba da rayuwa yayi mata ba so yayi ya aikata lahira sauka sukayi Addah Abulle ta karbeta hannun Mom tajata dakinta ta zaunar da ita Ya'isha ta matso tace kay yau Ina ganin masifa towaishi Big Cele meye yake nufi dan ance anasonki ya nemi aikaki barzahu?" Iska Addah Abulle ta furzar tace Lamarin Rasheed wuyar sha'ani garesa ni yaran nan sun fara gwaramin kai wlh yanzun Kareem ya fita harda hawayensa wai in taimakeshi ta yarda tanasonsa kafin ya tafi karatu ayi komai a gama a hada aurensu da Rasheed sai tayi karatunta acan shine nace yaje ya samu Mai Martaba ya fada masa shikuma wannan kurman yazo Yana neman kasheta kawai don ance anasonta ko ubanme yake nufi oho" Shiruce ta ratsa na dan lkc Amrah ta miqe tace Allah ya kyauta saiki tashi kisa uniform dinki mu fita ai" tunda suka shigo tana kwance jikin Addah tana aikin kuka daqyar Addah ta rarrasheta ta miqe tasa uniform din suka fita driver yajasu suka tafi mkrnta duk abinda akeyi akan idon Muntaz yayi qwafa ya fito ya shiga cikin gidan sukayi clear da Kareem suka harari juna kowa ya wucce. Tunda suka fito har sukaje mkrntar kuka takeyi har suka isa kai tsaye office din principal suka nufa suka gaisheta tare da gabatar mata da Aminah Haroona Moddibo a matsayin sabuwar dalibar da aka dade dayi mata bayaninta, tambayoyi tayi mata ta bata Amsa duk da batada nutsuwa Madam Khairat ta Yaba da qwazon yarinyar a mstsayinta na wacce batayi karatu ba. Bayan ta gama mata Interview din tabasu izinin su tafi domin Mai Martaba yace kada a raba masa yaya abarsu tare, hakance ta faru har aka tashi batada walwala, Muntaz ne yazo daukarsu baiga fuska a gurinta ba dole yasha jinin jikinsa maimakon ya tafi dasu gda wani park yakaisu waisu huta tukunna kafin lkcn islamiyya, Ya'isha da Amrah suka tafi harkokinsu itakuma ta nemi guri ta zauna har yanzu idan ta tuna ta batawa Baffa'am dinta rai sai taji hawaye ya zubo mata. Ji tayi an kama hannunta ta dago tana sauke ajiyar zuciya ganin Muntaz da wani fure a hannunsa yasata zubansa ido ya miqo mata yace yau ranar masoya ce ta duniya shiyasa na zabeta matsayin ranar da zan fara fayyace miki sirrin zuciyata, kafin hakan ki karbi wannan furen ki shaqi qamshinsa nasan zaiyi miki dadi" hannu tasa ta karbi furen tayi jifa dashi tace na shiga ukuna ni Aminatuh don Allah Ya Muntaz kar kace kanasona wlh Baffa'am kasheni zaiyi dazun saboda Ya Kareem yace yanasona daqyar aka kwaceni a hannunsa...." Batayi aune ba taji ya banqarata baya ya hade bakinsa da nata numfashinta ya dauke ta rintse idanunta ta hada qarfinta ta tureshi daqyar ta miqe tana rarraba idanu yayi murmushi Yana shafa sumarsa yace nop Ni ba irin baqauyiyar soyayyar nan zamuyi ba sai kinso kosu Ya'isha zasusan halin da muke ciki kawai zan baki damane mu rinqa ware guri muna haduwa har zuwa lkcn da Mai Martaba zaibamu damar yin aure Kinga saimu bayyana kanmu matsayin masoya lkcn babu abinda Big Cele ya isa yayi, to waima da kike wani tsoronsa shidin ubanki ne naga shima aure yake Shirin yi kekuma saiya hanaki jin dadinki akan me?" Wani mugun kallo da takeyi masa yasashi cewa kinga nifa ba dole zanyi miki ba Amma dai yakamata kisan yancinki a matsayinki na macen da kowa zaiyi burin mallaka....." Tsaki taja ta nufi wajen park din tana fita ta samu napep ta hau ta fada masa inda zai kaita yaja suka tafi sun rigata zuwa gdan suna kallo harda Rasheed ta shigo da sallamarta su Mom ne kawai da Mai Martaba suka Amsa mata shikam Rasheed wani kallo yakeyi mata na tuhuma inda Kareem yakeyi mata kallon tausayi Muntaz kuwa da shine ya shirya komai miqewa yayi zaibar gurin ya iso gabanta yayi mata murmushi ya fice daga falon Ya'isha da Amrah ma miqewa sukayi Amrah ta riqe hannunta suka juya zasu tafi Rasheed da taka musu wata uwar tsawa da saida fitsari ya kusa qwacewa Juhud ya taso a haukace ya zare belt dinsa batare dasun lura ba ya rufesu da duka bai damu da kowa bama kamar Juhud tafi kowa dakuwa tana ihu tana tambayar meye tayi masa Yana cewa tayi masa shiru Kareem ne ya miqe a guje ganin Yana neman illatata ya angajeshi ya dagata ya nunashi da yatsa yace kar Kuma ka qara dukanta wlh rama mata zanyi wannan ai zalumci ne duk abinma da Aminah zatayi su waye suka koya mata bagasu ba zaka wani zage qwanjinka akanta ita kadai saboda taqamar kanada iko da ita halittarta kayi?" Tana kuka ta qwace a hannun Kareem ta rarrafa ta riqe qafafun Rasheed tace indai dukan nawa zaisa zuciyarka tayi sanyi Baffa'am ka kasheni don Allah......" Daqyar takai qarshen zancen numfashinta ya kama rirriqewa gabadaya falon sukayo kanta kafin su iso gareta ma tuni ta suma, Kareem ya sunkuceta a guje sukayi waje asibitin dake cikin gdan ya nufa da ita suka karbeta suka shigar da ita wani daki gabadaya jikinta ya farfashe da dukan da yayi mata ruwa suka fara daura mata da Allurai. Mai Martaba ya iso ya tarar da Kareem zaune ya rafsa uban tagumi ya Kira sunansa ya dago idanunsa sun kada sunyi ja Mai Martaba yace ya jikin nata?" Bai bashi Amsa ba yace waini meye laifina don nace inason Aminatuh ko Kuma ita meye laifinta da wannan azzalumin zai nemi illatata shiga fah kaga yanda ya farfasa mata jiki Mai Martaba shikenan Kuma don ya kasance uba a gareta saiya takura rayuwarta ya hanata rayuwa da farin ciki ko kuwa laifinta ne qin dawowa da wurin daga mkrnta ita Ina ta sani a garin nan balle ace ita tajasu yawo"........ Jinjina kai Mai Martaba yayi yace babu komai qarami Yayanku Ni yakejin haushi saboda nace sai yayi aure Kuma na kawo masa Zulaihat nace ita zai aura bazai iya dukana ba shiyasa yake hucce haushinsa akan Aminah zaici qaniyarsa su gama karatun badai cikin satin nan zasu fara jarabawar ba dukkansu inada yanda zanyi dasu kaikuma kaje ka fara shirye nka na tafiya Saudi na gama maka komai" Gumi ne ya keto masa ya dago duk jarumtarsa Saida hawaye ya
Chapter 18 · 0% Book details