Sashe 23
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
nata ya fara duba juriyarta. ************* Satinsu biyu da Candy samarin Ya'isha da Amrah suka aiko neman aurensu da farko Mai Martaba yaqi amsar batun a cewarsa karatu zasuyi Alh Ibrahim wani amininsa shine ya sameshi ya bashi shawarar tunda sun nuna auren sukeso yayi musu ba lallai sai mace a gdan iyaye zatayi karatu ba a gdan mijinta ma zata iya karatunta da farko bai dauki mgnr ba saida Addah Abulle ta sake samunsa da mgnr Kareem fah ya matsa akan mgnr aure da Momy da ita da Ya Arman sune suka sameshi suka rinqa nuna masa abin hakan suna nuna masa Kareem namiji ne Kuma yanada kawaici tunda har ya fito da maitarsa ayi masa kada azo a samu matsala. Badon yaso ba ya amshi shawarar tasu dake dama an gama shirya komai na baikon Rasheed da Zulaihat hakanan ya Kuma bada maqudan kudade aka shiga kasuwa aka sake yo siyayyar baikon Kareem da Meenah Meenah batasan meye akeyi ba ranar baikon korasu akayi Katsina gdansu Addah Abulle acan suka yini suna tantalbadedensu akatsai da ranar aure Rasheed da Zulaihat wata biyu masu zuwa ya kama bayan azumi da sati uku dake azumin ya rage saura kwanaki bakwai ne sukuna akasa wata shidda saboda an qiyasta abinne da yanda zaizo daidai da hutun shekarar Kareem din ayi bikin ysnana ya dauki matarsa su tafi. Ranar farin ciki gurin Juhud da Kareem kamar su hadiye juna ta waya inda Rasheed yayi yinin qunci da baqin ciki a qarshe ma daki ya shiga ya kulle kansa yini sur har dare har safiya bai fito ba Mom ce ta kirata tace taje ta duba Baffa'am dinta tun jiya bai fito ba, bataso ba batason haduwa dashi tsoronsa takeji batasan da wacce irin fuska zai kalleta ba, hijjab dinta ta dauka ta Sanya ta fita ta nufi part din nasa tun daga falo ta fahimci akwai matsala kaca ta tarar dashi gabanta ya fadi ganin kwalaben wine da wasu qananun kwalabe ta matsa ta dauki daya ta duba tare da dafe qirji da sauri tace A'uzubillahi Baffa'am Alcohol kakesha?" Tsorone ya sarqeta takai hannunta qofar tana bugawa kusan 20 minutes bataji motsi ba murdawa tayi tajita a kulle ta rinqa bugawa da dukkan qarfinta Amma shiru dube dube ta farayi a falon can ta hango mukullaye a hade ta dauka da sauri ta fara gwadawa cikin saa na qarshen da tasa ya bude qofar ta tura da sauri, toshe hancinta tayi saboda warin daya daki hancinta takai dubanta inda ta hangeshi kwance a qasa cikin amai ta saki qara tana cewa innanillahi meye hakan meye ya sameshi?" Matsawa tayi ta shiga jijjigashi Amma kamar tana jijjiga dutse daidai lkcn Momy da taji shirun tayi yawa ta shigo ganinsa a wannan yanayin yasata sakin ihu tace Abdulrasheed meye hakan bakada lfy ka kulle kanka a daki zaka kashe kanka....."