Sashe 58
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dakai itama saita waske ya shiga kitchen ya daukowa yarinyar biscuits da yourghut ya zauna Yana bata yana murmushi dadi yakeji a ransa rabonsa da ita tun tana jaririya gata har ta tafi shekara guda ji yake dama ace mahaifiyarta ce a gefensa. Share hawayen daya tsiyayo masa yayi Zahrah na kallonsa tana kada qafa takaici yana qara kamata tace waikai yar wace ka dauko?" Murmushi yayi yace bakisanta ba ko?" Tabe baki tayi tace ya zaayi nasanta tunda baa cikin ahlinmu ta fito ba" sake kallon Muneefah yayi yace qwarai kuwa baa cikin ahlinku take ba tunda kinada ikon canzata daga jinina Zahrah na dade da fahimtar Ina kika dosa koma dai meye a ranki kibi a sannu domin Aisha itace ya babba a gurina Kuma ko zaki haifi duniya bayanta zasu biyo abu na qarshe da nakeso ki sani a aurenki ma arziqin Meenah kikeci saboda haka ki taka a sannu" Tashi yayi ya dauki yarsa ya nufi hanyar ficewa daga gdan tayi dariya tace iska kuwa na wahal dame kayan kara wahalalle Meenah dai tafi qarfinka saidai kaganta ka hanga kayi sake dan zaki ya girma me ita ya dawo son maso wani qoshin wahala" Bai saurareta ya tsaya bata Amsa ba ya fice ya nufi wani shop yayima yarsa siyayya ya juya ya koma gdan sarautar har sun shirya suna zaman jiran dawowarsa domin Alh Garbu yace ba kwana zasuyi ba a ranar zasu koma Kano Meenah bataso haka ba taso ta samu cikakken lkcn fahimtar da Baffa'am dinta gskyr lamari Amma batada wannan damar, tana kallonsa Yana kallonta ya dawo daga yawonsa a mota sukayi sallama da Kumbo Hami da Alh Garbu itakam ko kallo bata isheshi ba wani takaici ya cika mata zuciya abin nasa harda wulaqanci juyawa yayi yayi tafiyarsa tabisa da kallo ta girgiza kai ta shiga motar suka tafi tana waiwayensa hankalinta baimakai ga Kareem da yaketa daga mata hannu ba. Suna tafe tana furzar da iska a haka suka Isa Kano goma na dare suna Isa gdan da suka sauka ta shige daki ta kwantar da Muneefah dake bacci ta zauna zaman karatun wasiqar jaki batada mafita ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta bacci ya gagareta sai juyi kawai da takeyi cikin dare ta lalubi wayarta ta fara neman layinsa ta kasa jurewa Kira biyar tayi baa dagaba ta rubuta masa gajeran saqo na ban haquri, tana qara Kira taji wayar a kashe taja fasali ta kashe tata wayar ta zubawa Muneefah idanu tana sharar kwallah Tabbas duk abinda yasa Rasheed daukan wannan matakin akanta ba qarami bane, da wannan tunanin bacci ya dauketa da asuba ta tashi suka fara shirye nsu domin tashi zuwa Dubai, Tara suka tashi itadai badon tanajin dadin komai ba donma Naila tana dauke mata hankali da dan karen surutunta. Kumbo Hami ta fahimci abinda yake damun jikar tata koda suka isa dinma bata wani saki jiki ba har suka Isa masauki sukayi sallah sukaci abinci sukayi wanka kowa ya nemi makwanci sai dare suka fice daga masaukinsu, suka shiga gari itadai Meenah yaqe kawai takeyi lkc zuwa lkc tana gwada layin Rasheed Amma har yanzu yaqi dagawa har dole tasa ta saduda ta qyaleshi. Sai asuba suka koma gda sukayi sallar asuba suka kwanta rayuwar taci gaba da gudana a haka baqin naci ya hana Juhud daina kiransa shikuma yaqi dagawa kamar yanda Kareem yake nacin kiranta itama tana jizgashi idan abin ya dameta saidai ta Kira Ya'isha tasa mata kuka tace ta tayata bawa Baffa'am dinta hqr saidai Ya'isha tayi murmushi tace wlh Meenah baqin kishine yake damun Ya Rasheed Amma Ni shaida ce bai daina sonki ba" da haka take dan kwantar mata da hankali take samun nutsuwa. Satinsu biyu suka daga zuwa Malay daga Malay sukayi India daga can sukayi Saudi sukayi Umarah daga nan sukayi Turkey daga Istanbul suka gangaro Nigeria daga Nigeria suka zarce Mali, watanni hudu suka kwashe a yawon nasu suna dawowa suka shiga bikin Naila da Hameen dake abin duka na family ne yayi armashi sosai. Mom ita da Ya'isha da Aunty Hamida duka sunzo tunda sukazo take maqale da Mom tanata zubanta shaqwaba washegari suna gurin dinner Rasheed ya dira a qasar Basu dawo gida ba sai wajen 12:30am suna kowa baccine akansa tana shigowa tana cewa ni Allah Mom badon kin takura ba bazanje wannan dinner ba gara na kwanta nayi chat....." Mgnr ce ta maqale mata lkcn da idanunsu ya sarqe ana juna ya wani maze tunaninsa zatayi masa mgn ga mamakinsa sai yaga taba banza ajiyarsa ta Kara wayarta a kunne tana cewa double sorry na shiga yanayine wayar na jakka bansa ka kiraba sai yanz...." Iyakar nan Rasheed yaji ta shige daki yaji gabansa na mugun faduwa ya dubi su Mom da suketa faman dariya ita da yan'uwanta ya miqe zuciyarsa na tafasa yace. Gobe da wuri zan wucce Ghana ba lallai mu samu haduwa ba" bai jira amsar Mom ba ya fita ya ishe Alh Garbu da fadawansa sunata hira gda kamar kasuwa ya lura suma dabi'ar qasar kamar basa bacci sosai da dare, daquwa Alh Garbu yayi masa yace dan boko dan qaniyarka shine ka shige cikin mata ga qannenka da yayyaenka da iyayenka duka bazakazo cikinsu ba" yaqe kawai Rasheed yakeyi ya isa garesu ya gaishesu wasunsu da yawa yasansu qannen Mom ne wasu Kuma jikokin gdanne nan aka baje sabuwar hira Nan Alh Sulaiman babban yayan su Mom ya kaikaice yace Alh dama tun kusan sati uku nakeson yi maka mgn wai ya mgnr yaran nan Najeeb da Ameenah....." Tunda ya Fadi haka Rasheed ya zubansa ido duk da baisan wacce Aminan ake nufi ba Amma yaji saukar saqon faduwar gaba. Zubansa idanu Alh Garbu yayi Yana nazarinsa can yayi murmushi yace to ai lamarin Aminah ne akwai rikitarwa kaga mijinta na farko ko igiya daya bai yanke mata ba nemansa akayi aka rasa shari'a tabata damar aure ta auri qaninsa shikuma qaddara ta rabasu da saki daya to mijinta na farko din ya bayyana Kuma tanasonsa shima na shaida yanasonta wani dalili ne ya hanashi magantuwa saboda haka indai sunason juna to sunfi dacewa da juna wannan dalilin yasa nace da Najeeb ya hqr wannan abu duk na gidane dashi da Rasheed duk jikokin gdannan ne rashin zumincinsu yasa basusan juna ba" Tunda Alh Garbu ya fara mgnr gumi ke karyowa Rasheed baqin kishinsa ya motsa ya dago idanun nan kamar gauta Yana Shirin yin mgn wayarsa tayi ring ya zaro ya duba aqogo daya na dare harta gota ganin number Ya Arman yasashi tunanin akwai dai wani abu daya faru daga wayar yayi ya Kara a kunnensa numfashi ya sauke me nauyi yace ina Kareem din?" Huci ya furzar yace Har matarsa aka kashe ko iya shi kadai ne?" Sake jan numfashi yayi yace ok zan dawo gobe" daga haka ya kashe wayarsa. Ya miqe ya nufi makwancinsa ya soma safa da marwa Yan fashi sun shiga gdan Kareem sun kasheshi shida matarsa? To akanme?" Tambayar da ya rinqa yima kansa kenan mara Amsa a hankali yaji wasu hawaye sun zubo masa ya nemi guri ya zauna Yana tuno haduwarsu ta qarshe da kalmar qarshe ta Kareem ya fada masa, Kai dan uwana ne na jini Ya Rasheed a tunanina murna ya kamata kayi da ya kasance nine na kula maka da iyalanka a halin bakanan ba gaba yakamata kayi dani ba! Ya Kareem har gobe inason Meenah bazan taba daina sonta ba har fitar numfashina na qarshe na hqr da Meenah ne badon zuciyata ta hqr ba saidon bata damar kasancewa dakai domin kaine zabinta, dani qaddara ta rubutawa bacewa ka auri matata idan na dawo gdy zanyi maka badon bana kishinta ba aa saidon nasan ta cancanta ne shiyasa ta zama matar gado cikin ahlinmu".......... A daren nan Rasheed bai rintsa ba kwana yayi Yana tuna abubuwa da dama da suka faru tsakaninsa da Kareem tun daga ranar farko da suka fara qullah soyayya da Meenah kawo lkcn daya aureta ta qarfi da irin wahalar da Kareem ya rinqa Sha ta ciwon zuciya duk akanta kawo yanzu yanayin da suke ciki da irin bibiyar da Kareem ya rinqa yi masa akan yayi hqr ya daina gaba dashi sosai yayi kuka da baitabayin irinsa ba a duniya tabbas ya tafka kurakurai masu wuyar gyarawa Kareem baya duniya labarinsa ya shude balle yaje ya nemi afuwarsa akan abinda yayita qoqarin ganar dashi yaqi bashi qofa. Da asussuba kuwa ya dokawa Mom Kira itanma yanda ya kwana haka ta kwana saboda tun Daren itama aka fada mata abinda ke faruwa Meenah kam batasan meke faruwa ba Amma ranar ta kasance cikin wani yanayi domin a daren waya sukeyi da Kareem Yana mata wasu kalamai data kasa fahimtarsu can taji yace Meenah kada ki manta wannan wlh tallahi duk duniya nafi kowa sonki ban barki don biyayya ga umarnin Addah ba nabarki ne don nasan kedin banine a zuciyarki ba Meenah in son samuna ne Muneefah ta rayu a qarqashin kulawarmu ni dake nasan hakan bazata samu ba wani abu yana gaf da faruwa dani, Ina kukan rabuwa da abubuwa biyu da nafi qauna ke Meenah da Kuma yarmu Muneefah Amma a wani sashin Ina farin cikin kasancewar zata rayu da cancanta madadina wato Rasheed Meenah ki komawa Rasheed don Allah don taimakon maraicin Aishatuna kinji......" Daga haka ya tsaya da mgnr taji wata qara can taji yace ina zuwa zan kiraki kamar Yan fashi sun shigo unguwarmu" daga wannan tajishi shiru kalamansa sun tsayanta a rai zuciyarta ta karye tabbas lamarin Kareem akwai taqawa da tsoron Allah baitabayin Abu don jin dadin kansa ba komai zaiyi yanayine don mafitar Al'umma Kareem yakai masoyi a gurinta. Miqewa tayi zumbur lkcn da taji Ya'isha ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati Mom da gaske Ya Kareem sun kasheshi ya mutu shikenan bazai qara dawowa duniya ba Muneefah ta zama marainiya....." Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu