Sashe 32
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
cikinsa tun lkcn mutuwar Innatu tace Innanillahi Wa Inna ilaihir raji'un Ya'isha don Allah da gaske kikeyi meye yake damun Baffa'am ne komansa daban dana mutane meye yake nufi da fitowa ya baro gdan batare da lamuncewar Iyayensa ba....." Numfashi Ya'isha ta sauke tace tabbas kekam kina ruwa gaban breaker yasaki cikin wani yanayi domin tunda ya sakai ya fice a gdannan Mai Martaba yake saba da marwa babban abinda yafi komai dagawa kowa hankali yanda yaje aka daura muku aure batare da kowa yasani ba Mai martaba yace wato shi bai dauki kowa da muhimmaci ba cikin rayuwarsa kawai abinda zuciya ta saqa masa shi yakeyi kiyi bakin qoqari wajen ganin kin saitashi tunda qaddara ta hadaki dashi babban tashin hankalin ma dazun nan fah mukayi baqin wasu Fulani sunce abinda ya raboki da rugarku Moddibon rugar kika kama kika cinye shine yan'uwansa suka sanyawa bukkar da mahaifiyarki take jinya wuta ke Kuma suka biyoki zasu kasheki Kuma fah kowa ya amince da wannan labarin harma Mai Martaba yayi rantsuwar babushi babu Ya Rasheed muddin be sakeki kin qara gaba ba Addah Abulle ce me cewa ita Allah ya rabata da qaya da tuni danta da takejin dadi dashi ya zama sorry, Mom kam har yanzu ta kasa cewa komai sai hawaye da taketayi na tambayeta meye dalili tacemin Ya'isha sharrin maita yanada ciwo anyima qanwar babana sharrin maita ta mutu da wannan baqin cikin anyiwa yayata sharrin maita tun daga cikin gdanmu Ayshatu ta tashi da wannan ciwon a ranta ta sake samun dangin mijin da basa qaunarta aurenmu na Fulani suka hanata shiga dangi bata zuwa Mali kawai saboda sunce danginta mayune wannan dalilin yasa ta bata a dangi bamu santa ba tun tana qarama dama uwarta tabar gidan babanmu da ita tun suna Senegal Saida ta Isa aure aka aurawa wani bafullace ita ya tafi da ita daga nan bamu sakejin duriyarta ba har kawo yanzun. Ya'isha idan Juhud ta kasance yanda ake tunani to tabbas tana cikin hadari idan Kuma ta kasance akasin haka to tafi shiga hadari domin kuwa duniya zatayi mata qunci zata rasa tudun dafawa ga maraici ga qiyayyar dangin miji nikam banso Rasheed ya auri yarinyar nan a haka ba naso yayi aure me yanci da ita wlh inasonta a cikin jinina Kuma Ina tausayinta" Tunda Ya'isha ta fara mgnr Meenah ke wani irin kuka me ciwo tanajin tausayi da tsanar kanta a hankali ta zame cikin kuka tace inasu Baffa Ribado sukasan inda nake har sukazo suka lalatamin tarihina......" Qwace wayar taji anyi ta dago tana kallonsa tana hawaye, yaja fasali yace ba laifinsu bane nine naje na nemesu domin su dauramin aure dake, ko ki kasance mayya ko ki kasance akasin haka niba damuwata bace damuwata kawai ki kula da kanki ki kiyayeni nima na kiyayeki. Ke Kuma munafuka da kike kwashe komai kike sanar da ita zanyi maganinki duk ranar dana shigo Katsina....." Da sauri Ya'isha ta kashe wayar ya jefata a aljihunsa ya zauna kusa da ita ya riqo hannunta yace idan ya kasance nine mijinki Kuma na yarda da komai akanki Meenah na yarda na mutu saboda ke to meye Kuma saura dazai dami rayuwarki?" Sosai kalamansa suka shiga jikinta ta fada jikinsa ta ruqunqumeshi tace zanyi farin ciki da samun masoyin gsky me qaunata domin Allah Mai sona da aibina Amma bazanso ya kasance nice silar lalacewar alaqarsa da danginsa ba musamman iyaye Baffa'am kada ka zabeni saman mahaifanka don Allah kabarni da qaddarata......" Bakinsa yasa ya rufe nata a hankali suka zube a qasa Yana hura mata iska ya zare bakin nasa yasa saman hawayenta Yana lashewa Saida ya tsotsesu tsaf sannan yace zan tayaki jigila da qaddararki bakin rai bakin fama yanzu ne wasan zai fara Meenah ko kowa zai gujeki Ni zan rayu dake" hannu yasa a aljihunsa ya zaro wata baqar leda ya kunce ta zubansa ido ya tasheta zaune ya zaro abin wuyan dake ciki sai walwali yakeyi ya dubeta itama shi take kallo tace lahh Baffa'am Ina kasamu wadannan?" Murmushi yayi yace tun ranar farko dana tsinceki na cire miki shi a qugunki na adana maki su ke Ina kika sameshi?" Sunkuyar da kanta tayi tace Innatu tacemin na kakata ne da Babanta yabata lkcn aurenta shine data rasu baffana yaci gado shikuma yaketa ajiyarsu gareni har zuwa lkcn da ajalinsa ya riskesa ya samqawa Innatu itama ana gobe zata rasu tabani su Ni nama manta dasu badan yanzun ba"...............