Sashe 52
Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gaba hakanan sai taga Kareem yayi tagumi ya tsunduma duniyar tunani idan ta tambayeshi dalili sai yace mata Babu komi Tasha zuwa ta tarar dashi Yana kuka a daki shi daya tambayar duniya sai yace mata Babu komi dole ta zubansa ido a dan ritsin ne Kuma ya kama rashin lfy sosai itadai Saida ta Kira Mai Martaba ta sanar dashi domin an bashi gado baisan waye akansa ba wani abin mamaki daya razana duniyarta ranar da Mai Martaba yazo tana tsaye jikin gadon da Kareem yake riqe da hannunsa tanayi masa addu'a taji sallamar Mai Martaba ta dago da sauri cak ta tsaya komanta ya tsaya hatta da numfashinta lkcn da tayi arba da wanda yake takewa Mai Martaba baya cikin bugawar zuciya tace Baffa'am!" Kallonta yakeyi da alamun rashin fahimta ta nufesa da sauri tana cewa Ya Allah Mai Martaba yaushe akaga Baffa'am dina Amma aka boyemin meye yasa akayimin haka ashe akwai abinda zaa iya boyemin game da Baffana....." Tana mgnr tana nufarsa shikam ya saki baki ne Yana kallonta zuciyarsa na wani irin bugawa da mugun qarfi qara waro idanunsa yakeyi yanason ya ganeta ya kasa tana Shirin kai hannunta jikinsa taji yace da Mai Martaba mai Martaba itan wacece?!" Ba itaba shi kansa Mai Martaba Saida tambayar ta dakeshi ya dubeta yaga tayi mutuwar tsaye hawaye nabin kuncinta bakinta yana rawa alama ta magana takeson yi ta kasa kama hannun Meenah Mai Martaba yayi yace ki nutsu Meenah Rasheed fah ba qalau yakeba duk duniya Babu wanda yake ganewa" zubawa Mai Martaba ido tayi tace meyesa aka boyemin bayyanarsa?" Murmushi Mai Martaba yayi yace akwai hikima cikin hakan yanzun ma banso kikasan da bayyanarsa ba so dandai ya matsa ne saiya biyoni" Zubewa tayi ta rushe da kuka tace Allah na gde maka daka bayyanamin shi a raye Mai Martaba Amma ya gane Sarki junior ko?" Murmushi yayi yace ni kaina da zan fita na dawo saiya tambayeki waye ni" zubawa Rasheed ido tayi da yake bin dakin da kallo yace Mai Martaba shima wannan dakin bansanshi ba shikuma wannan da bashi da lfy waye?" Yana mgnr yanakai hannunsa ga Kareem dake kwance kamar gawa riqe hannunsa Mai Martaba yayi yace bakasanshi ba?" Daga kai yayi yayi murmushi yace wani qaninka ne Kareem ja tunasa?" Dafe kansa yayi kamar zai tuno ya dago yace ok shine wannan wanda mukayi yaqin tare dashi aka sacemu tare aka kaimu Sudan kace sunan gurin ko?" Murmushi Mai Martaba yayi ya dubi Juhud data kwantar da kanta a jikin gadon tana kallon ikon Allah. Likitan ne ya shigo suka gaisa da Mai Martaba suka fita suka barta ita da Rasheed abin yana tsuma jikinta da ruhinta wai gata ga Baffa'am dinta Amma baiko kallonta harkar gabansa kawai yakeyi ta miqe tanajan tsohon cikinta me watanni takwas ta matsa bayansa ta sassauta muryarta tace Abdulrasheed" juyowa yayi ya zubanta ido tare da dibanta ya watsar hawaye ya sake tsiyayo mata tace wai da gaske baka ganeni ba?" Daina latsa wayar yayi ya sunkuya ya ciro takalminsa duka biyun ya miqa mata yace nasan sune sukayi miki kyau to gasunan na baki" noqewa tayi taqi karba tace meyesa zaka mantani tsayin shekara shidda nakasa cireka a Raina na kasa karbar kowa bayan kai Rasheed ni ban cancanci ka mantani ba....." Saurin ja baya tayi lkcn daya fara kwance tazugen wandonsa gabanta ya fadi tana kallonsa tanajin ninkin faduwar gaba gani tayi ya zare wandon ya kuma cire rigar ya rage dagashi sai singlet da boxes ya nufeta Yana murmushi yace nifa kinganni banida rowa idan kinason wadannan dinma zan iya baki wlh Meenah ta tafimin duk abinda na mallaka a duniya Kuma kinsan Meenah ta mutu Ina zuwa kogin maliya zan fada ciki na tsunduma tsundum na mutu nima kowa ya huta yawwa ai kema kinsan zan hadu da Meenah acan ko?" Tashin hankali Yana matsarta tana matsawa ya damqo hannunta ta rintse idonta ya damqa mata kayan yace ki riqe nabaki sadaka idan kinason agogon ma da zoben duk na cire miki Ni dama na daina kwalliya takaba nakeyi Kuma bazan qarason wata mace ba a duniya tunda na rasa Meenah" Girgiza masa kai takeyi tana kuka me gunji ya dora hannunsa a bakinsa yashe dallah malama kiyi shiru Meenah batason kuka" gumtse bakinta tayi ya juya zai fita Mai Martaba ya budo qofar ya shigo yaja ya tsaya da sauri yace ya subhanallah Rasheed meye hakan?" Murmushi yayi ya sosa sumarsa yace ai harkai zan iya kyautarka indai akan Meenah ne" zaro ido Mai Martaba yayi yace nidin Rasheed" dariya yayi harda riqe ciki yace kaidin har wata daraja ce dakai ta musamman da zatasa naqi fansar dakai akan Meenah?" Girgiza kai Mai Martaba yayi yace naji banida ita Sanya kayan naka muje masauki" juyawa yayi ya kalli Juhud ya tsugunna yace don Allah mamana kibani aro Allah niba barawo bane zan dawo miki dasu yau dinnan aidai bake kika sani ba nine nasa kaina nabaki kyautarsu ko?" Miqa masa tayi yace aafah Hajiya in kinsan ba tsakani da Allah kika baniba bar kayanki" Dauke qwallah Mai Martaba yayi yace karbi tsakani da Allah tabaka" yasa hannu ya karba Yana sawa Yana waqarsa Meenal Aso kin matar da zuciyata ta mace! ki tausaya karki sani bangare na yaudara!! Ina gudun duniya!!!" Da wannan ya fice Mai Martaba ya dubeta yace likitana ya tabbatar min da zai samu sauqi fah karki damu" ficewa sukayi suka barta da kallon Kareem dake kwance kamar gawa ta juya itama ta fice kamar mahaukaciya ta nufi block nasu ta fada gado domin tabawa zuciyarta hutu daga sabon tashin hankalin daya tunkarota ga Baffa'am dinta a gabanta Amma yakasa ganeta to waima meye asalin dalilin sukurkucewarsa ne haka Shiba Mai mgn ba Amma surutai rarrara kamar Wanda ya qone a qeya miqewa tayi tare da cewa tabbas lkc yayi da zan sakawa Mafi cancanta Alkhairinsa....." Tunaninta ne ya tsaya cak da tunawa da Kareem shikuma da yake cikin halin ni yasu dora hannu tayi akanta daidai lkcn da wayarta tayi ring ta wawurota Ya'isha tace na dade inason tsegumta miki watanni biyu baya anga Big Cele a Tanzania to tsoron jagula wannan dofanannen auren naki da Ya Kareem yasa Mom ta Hanani fada miki wai Kuma yau sainaji me kankat ankawo mikishi har qasarku" Cikin kuka tace shine me gata ko rashin galihu yasa kukaki fadamin labari mafi soyuwa a duniyata Ya'isha ko ku fada ko karku fada Rana irin wannan zatazo gashi tazo Baffa'am ya dawo zamana da Kareem ya qare....." Da qaraji Ya'isha ta katseta da cewa bakida hankali ne karki soma wlh Kareem yafi kowa buqatar taimakonki kinaganin fa a halin da yake" jan zuciya tayi tace meye ribata dama uwarsa ta rantse indai na haihu saiya sakeni to kafin ma na haihu zanbar mata gidan danta nima a dole nake zaune don halacci" magana Ya'isha keson yi mata ta kashe wayarta can Mom ta kirata tace idan kin kwantar da hankalinki akwai labari me dadin dadi da nakeson baki" Muryarta harta dashe tace kun boyemin abinda na cancanci nasani Mom meyesa" murmushi tayi tace saboda kada muyi mahaukata biyu a dangi shiyasa Meenah kifa nutsu motsi kadan zakiyi ki fada rami mijinki yafi kowa buqatarki to kibi sannu kada santsi ya debeki"haka Mom ta rinqa bata kalamai wai ita a dole saita kwantar mata da hankali batasan qara tashin hankalinta takeyi ba suna kashe wayar Dr Khazeem yazo ta dubeshi yace ya naki jikin batason hayaniya hakan yasa tace naji sauqi so ganin yanayinta yasashi ficewa ta koma ta kwanta kamar bazata koma asibitin ba saidai taji zucciyarta taqi natsuwa dole ta shirya ta nufi asibitin ga mamakinta saita isheshi a zaune shida Mai Martaba ta dubesu suka gaisa da Mai Martaba yace kema kina buqatar hutu ya kamata ki koma gda ki haihu acan" jinjina kai Kareem yayi yace dama inada burin hakan sai na kwanta jinyar nan" da wannan sukaci gaba da tattaunawarsu hankalin Kareem na kanta Mai Martaba yace ki koma masaukinku ki huta zan kwana dashi muga abinda hali zaiyi"....... _Yau fah saidai hqr da qarancin page din_ Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241... Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241..... *Oum Hairan* [8/12, 8:08 PM] Oum Hairan: Duban juna Juhud da Kareem sukayi yayi mata qaramin murmushi ya shafa sajensa tare da nuna mata hanya yace kije ki huta heart kinyi qoqari fah na gde Allah yabada lada" sunkuyar da kanta tayi tare da daukar wayarta tayi musu Saida safe ta fice ta nufi masaukin nasu zuciyarta na kaikawo tsakanin qirjinta da duniyar Rasheed, tana zuwa wanka kawai tayi tayi sallah ta kwanta itakam wannan dare barawon ma kasa satarta yayi gabadaya ta rasa nutsuwarta batajin daidai saina tunanin Rasheed, da asuba tayi sallah ta zauna tanayima iyayenta da Rasheed addu'a tare da fatan sauqi da sassauci cikin wannan jarabawa da suka tsinci kansu a ciki ciwon tabuwar qwaqwalwa a Rasheed abin Babu kyau. Data tashi da ciwon mara ta tashi hakan yasa bata koma asibitin da wuri ba Saida Tasha magani ta dan samu relief sannan ta fita ta nufi hospital din a qofar dakin da Kareem yake ta ishe Rasheed Yana tsaye yana danna waya kamar ance ya dago suka hada ido ya lumshe idanunsa qirjinsa Yana bugawa itama haka ta matsa gabansa tace barka da sfy Baffa'am" ja tayi da baya lkcn daya kece da dariya yace shegiya ashe kinsan sunana ai Meenah ce take kirana da wannan sunan" lumshe idonta tayi hawaye ya ciko ijiyarta ta bude akansa ta girgiza kai tare da cewa ka manta kowa da komai ka manta kamannin Meenah a zahiri Amma baka manta sunanta ba Baffa'am ya akayi hakan?" Yarfa hannu yayi yace nima to nasani kawai dai kema kinsan idan na kama Wanda ya kashemin Meenah a gabana saina dirmeshi da alburushi ke barima kiji fah koda yake na daina kulaki Meenah kishine gareta batason a hadata