← Book details Juhud Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 64

Sashe 39

Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Oum Hairan* [8/1, 8:43 PM] Oum Hairan: *0025* Sake shigewa tayi jikinsa tana sunsunar qamshin turarensa cikin wata murya me kashe jiki tace inasonka My world" matseta yayi Yana shafa cikinta na watanni hudu yace inasonki fiye da yanda nakeson komai a duniyata ki zama amanata tawa Ni kadai kinji" murmushi tayi masa ya sake mirginawa kanta ta lumshe ido ya dora bakinsa saman idanun nata Yana lasar eyeslashers dinta tare da matse nononta a qirjinsa yana matsata yanda yaga dama wannan Rana an kurbi zumar qauna yanda ya kamata. Sunaji ana buga musu qofar sukayi likimo abinsu fir ya hanata fita wai yau lkcnsa ne bazaa yimasa ojoro ba hatta abinci Saida dare ya fita yaje ya siyo musu ya dawo suka qara bajewa suna tsinkar furensu da dare aka kwanta akaci gaba da bawa qauna haqqinta tun Juhud na jurewa har ta fara gajiyawa abinka dame yaron ciki shikuma dadinta ya hanashi qyaleta, da safe Mom da kanta tayo tattaki tazo barayin nasu domin babu wanda yasan ya dawo sai Muntaz daya daukoshi a airport. Ta jima tana bugu daqyar ya saki Juhud daya maqale ya fito parlourn yana tambayar waye? Jin muryarsa yasa Mom cewa haba nidai naji shirun tayi yawa Rasheedu ashe ka dawo?" Bude mata qofar yayi ya kwantar da kansa a kafadarta wannan tsohuwar al'adarsu ce yace wlh tun jiya da yamma na dawo" murmushi tayi tace babu Kuma ko nemanmu saima hanamin yata fitowa anata hada a cikin gida tun jiya wayarta a kashe" sosa qeyarsa yayi ya zauna lkcn da Juhud din take fitowa ganin mom yasa taji kamar ta nutse ta rusuna a kunyace ta gaisheta tayi dariya tace yar jaka ba ko sisi waike dadi miji mijinki ya dawo kin manta dani ko zai tafi yabarni dake ai muga qaryar rashin kunya" Dariya sukayi dukkansu Ya'isha da Amrah suka shigo da Khadija da Zahrah matar da zaa aurawa Kareem Ya'isha ce kawai ta kalli Juhud tace ai dama Saida na kawo haka a Raina nace duk yanda akayi Babban ogane ya dawo kika manta damu" murmushi tayi tace yo mi zanyi muku duniyata ta dawo gareni" dukkansu kallonta sukayi ta matsa jikinsa lkcn da Mom take fita tana cewa aifa baki ya bude da alamun shima unborn din babansa yake buqata naga yau jiki ya wartsake ya samu abinda yakeso" Gaisheshi sukayi ya Amsa hankalinsa nakan Meenah ya miqa mata hannu ta kama ya dagota jikinsa ya zaunar da ita suka kalli juna Ya'isha tace baba Aminu ne yace mu kawo maka Aunty Khadija ku gaisa Wai kun dade baku hadu ba" shafa qirjinsa yayi yace wlh fah tun rasuwar mijinki halan kin gama idda ne?" Wani farr tayi da idanu tace kayyy soja ai tun lkcn mutuwar Aunty Zulaihat ma nayi iddah" tabe baki yayi yace ok to ai saiki fidda miji kiyi aure kada kice zakici gaba da shashancin da kika rinqayi a baya yaja miki aure da qananun shekaru" murmushi tayi tace ai nama fitar Yaya Soja" bai bawa hirar muhimmaci ba ya kalli Zahrah yace wannan itace dayar amaryan ance amaren ukune halan ya jikin Kareem din hope Yana samun sauqi?" Tabe baki Amrah tayi tana wani yatsina tace to bama dolenshi ya warke ba wannan auren gayya da zaayi masa da yar asali me cikakkiyar nasaba" kallonta yayi batare daya fahimci meye takeso tace ba ya miqe yace Life help me breakfast kin yasheni jiya fah" Saida taso ta nutse dan kunyar qannen mijin nata hakana ta miqe Khadija na harararta ta nufi kitchen cikin yan mintuna ta sama masa abinda zaici ta dauka ta nufi dakinsa ta aje masa zata fita ya riqota yace saurin na meyene?" Zama tayi tana hada masa tea din tana cewa mom tace idan na gama naje mu gaisa da baqin Mali sunzo tun jiya sunata buga sashin nan ka Hana a budensu" yasan da hakan shiyasa baice komai ba ya rinqa janta da hira Saida ya gama yayi wanka sannan suka fito tare sunsha kyau na ban mamaki suna fitowa da ango Kareem suka fara kicibis sukayi musabaha ya tambayesa aiki shikuma ya tambayesa jiki itadai gaba tayi saboda zuwa lkcn wani haushin Kareem din takeji yanda yake nacin kallonta. Ta rigashi shiga tana shiga parlourn Hajiya Bilki da su Nana da sauran mutanen suka fara watsewa ta tsaya sake da baki kawai sai tajiyo a bayanta wata mata na cewa ai wannan kina ganinta kyaun dan maciji baqar annoba kenan yanzu kina cika wargi zaki tsinci kanki a Ramin kabari ta tsotse bargo ta lashe kurwa" Juyawa tayi ta zubawa me mgnr ido hawaye wani nabin wani shiyasa jiya taqi fitowa saboda gudun abinda zatayi gamo dashi a wannan taron bikin, ji tayi an saqalo qugunta taja ajiyar zuciya tare da share hawayenta da gefen mayafinta ya zagayo gabanta yace dame Kuma kika gamu daga fitowarki" murmushi tayi tayi gaba ya riqo hannunta yace wlh bazaki shigaba saikin fadamin uban waye ya tabaki?" Tana Shirin mgn Ya'isha tace wato Ya Rasheed yau zaayi kutmar uba a gidannan....." Fuuuuuu tayi gaba tana zuwa ta dauke Hajiya Bilki da Mari ta kama qunduma mata ashar abinka da bakatsina yau jini ya motsa bala'i takeyi tana dara nandanan gurin ya kacame taron biki ya koma taron fada shidai Rasheed baisan meye yake faruwa ba Saida yaji tana cewa aikin banza aikin wofi har wasu kune zaku dubi Meenah ku rinqa jifanta da miyagun kalamai dama ai na dade Ina jiran damar cin bura uban kowannen shege a gdannan idan kuna taqamar ance muku itan mayya ce to ai gara ita ansan wacece ita ku waye yasan asalinku yayan bayi kawai Wanda tsiya da munafurci ta Haifa ta goya ta shayar Bilki kibi a sannu halwa ce dake gaba da baya Kuma mata ba maza ba aure Big Cele yace bayaso bazai auro irin masifa irin jaraba ba wlh dadai auren halwarki gara auren mayyah so million indai msita irinta Meenah ce Kuma Meenah ta zame muku ciwon ido a gdannan kowanne dan iska saidai yaganta yabarta idan da meja Kuma yaja shima ya wullah barzahu kamar yanda Zulaihat data dage saita shiga tsakanin rabo ta fece, yan iskan banza munafukan wofi" Tunda yaji dalilin rikicin jikinsa ke tsuma ran maza ya baci idanunsa suka kada sukayi jawur ya dubi Juhud data durqushe a qasa taketa aikin kuka me cin zuciya ya juya ya dubi mutanen kowa jikinsa ya hau karkari baice komai ba baiwa kowa mgn ba ya figi hannunta da qarfi suka fice daga falon gurin Mom din da baajeba kenan ya mayar da ita sashinsu ya kulle ya zauna yanata huci ya miqe ya zauna yafi sau ashirin sannan Kiran Mai Martaba ya shigo yayi jifa da wayar ta tarwatse ya tashi ya shiga dakinsa batasan me yayi ba ya fito dauke da jakankuna manya guda biyu ya fice ya jefa a mota daidai lkcn da yake Sanya kayan a mota Mai Martaba ya iso gurin yace ya subhanallah meye Kuma hakan Ina zaka?" Juyowa yayi idanunsa sun kada sunyi jawur ya dubeshi ya kawar dakai Alh Aminu ne ya matso shima lkcn Rasheed din ya koma cikin gdan ya figo hannun Meenah ko dankwali Babu akanta Mai Martaba daya fahimci barin gidan yake niyyar yi yace wai ba mgn nakeyi maka bane" a fusace ya juyo yace banaji Mai Martaba banji abinda kaceba ka kauce kabani guri yau kam ko baku koreni ba na gama zaman gdan sarautar nan akan matata zan iya hqr da komai....." Muryarsa ce ta sarqe ya jefata a mota ya kulle har yanzu kuka takeyi yama kasa rarrashinta ya sake kallon Alh Aminu ya nunasa da yatsa yace ka sanar da munafukar matarka ni Abdulrasheed nafi qarfin yayanta a aure kun bani Zulaihat banaso na karba Allah ya dubeni ya kasheta kun bani Hidaya na sakar muku kayarku shine yanzu zaku liqamin bazawara kwancen wasu saboda kun Mai dani jani talau waima ni kadaine da namiji ne a gidannan Ina Salman Ina Arman Ina Kareem Ina Muntaz hatta Urwat kukayiwa aure zama zaiyi da matarsa saini akanme zaku sanyawa rayuwata idanu ne banaso na fada muku banaso wlh tallahi zanci mutumcin duk ubanda ya qara tunkarata da mgnr aure auren banza auren wofi da har zaku sanyawa matata tsura akansa aiba ita ta hanani ba nine naga batada tamka bare mahadi, Abu na qarshe ka fadawa Bilki ta kiyayi dawowata gdannan Kuma ta shirya Amsa Kira kotu saita fadamin uban wa matata ta kashe da take fadawa duniya cewa in mutum ya cika rabar Meenah saidai yajishi a Ramin kabari?....." Sosai Mai Martaba ya girgiza da yanayin Rasheed din yasan tabbas yau yakai qarshe akwai gagarumar matsala idan yabarshi yabar gidan dama Meenah ce zatake kawoshi tunda shi dama asalinsa bayada ra'ayin zaman gdan sarautar to ya dauke abarsa meye Kuma zaisa suganshi? Mai martaba na Shirin mgn Mom ta iso gurin ita da wasu mata su uku dole tasashi yin shiru ta kama hannun Rasheed tajashi gefe sun jima suna bugawa kafin ta shawo kan kayanta Yana kuka kamar wani yaron goye daqyar ta lallabashi ya yarda zaibar Meenah a gidan sarautar Amma da angama biki da ita zai tafi. Zuwa tayi ta fito da ita a mota ta janye mata sumar data rufe mata fuska tana ganin Mom din ta fada jikinta ta sake rushewa da kuka itama hawaye ta share tana tausayawa rayuwar Meenah Babu uwa Babu uba babu shaqiqin dan'uwan da zata zanta dashi taji dadi ga rayuwar taqi mata dadi wata murya taji ta bayansu tace kiyi hqr Aminatuh komai yayi tsanani sauqi na zuwa hakanan Allah yake jarabta bayinsa zababbu domin ya gwada imaninsu ba sonki ne bayayi ba qaunace ta kawo miki hakan bantaba ganin Wanda akayiwa irin wannan qazafin ya qare rayuwa a wulaqance ba ko baizama wani ba zai samu yardar Allah" Juyawa tayi ta zubawa matar idanu gabanta ya yanke yabada wani rass ta janye jikin Mom da sauri tana qara kallon matar tare da langwabar dakai a rayuwarta nata taba ganin kamar tsagin Kara irin wannan ba kama haske da jiki inda kasan innatun ta a hankali ta sauke ajiyar zuciya tace mom wannan fah?" Dadine ya cika mom ganin ta
Chapter 39 · 0% Book details