← Book details Juhud Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 64

Sashe 4

Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da wadannan abubuwan" Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su kubce miki kinji" jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa washegari da safe na damawa Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da zaki fita dashi talle. A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura au renki da Manga nikuma gashi Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa. *ASALIN LABARI* Jikin Juhud ne ya qara sanyi hawaye na sunturi a kucinta tace yanzun wadannan sune kadai dalilan da suka sanya Suka kashemin Baffina Amma aka kasa daukar mataki akansu Innatu wannan wacce irin Al'umma muke ciki meson kanta? Shafa nadaddiyar sumarta tayi itama cikin hawaye tace haka rayuwa ta zama kina gani fah tunda Baffanki ya rasu ko nono sun hanamu tatsa saidai su tatse subawa matansu suje su siyar idan kinga mun samu nono a rugarnan to Moddibo ne ya tatso mana Juhud ya zakayi ne da qaddararka ni yanzu burina a duniya naga kinyi aure kin samu matsugunni saboda wannan rayuwar bata yuwuwa a haka" Fadawa tayi jikin Innatu tana kuka me cin zuciya itakam da Innatu zata amince da sun bar rugar nan tunda baa sonsu amma tasan bazata aminta ba, da wannan tunanin bacci barawo ya saceta. Washegari da wuri ta dauki tallan nononta ta tafi tasha cike da doki yau tayi niyyar idan tayo ciniki har Balangu zata sawowa innatu ko tsiren quli tana tafe tana yan waqoqinta harta isa gari koda taje yan nonon gurin ya cika batada guri dole ta koma gefe ta rakuye tana wasanninta na quruciya dagowar da zatayi taga wani baqin hadari ya gangamo tana juyawa taga Fulanin duk suna hade karensu gashu batayi cinikin kirki ba donma ta datsa yariman ne ta dibarwa wani na dari biyu shiyasa da haka zata koma. Ganin hadarin na gangamowa yasata miqewa jikinta a salube tana juya dari biyun ta gama kasaftata tasai mawa Innatu maganin ciwon jikin hamsin tasai mata balangun dari ta riqe hamsin a hannunta ko batirin fitila sa siya, daukar qoranta tayi ta aza aka ta juya kenan zata tafi taji wata mota tayi horn a bayanta ta juya taga me motar ya zuge glass wani matashin saurayi ne me qwarjinin gaske fuskarsa a daure ya bude bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace na nawa ne?" Cikin fullanci yayi mgnr tayi saurin Amsawa da cewa na dubu Uku ba dari biyu" dubanta yayi yace harke?" Kallonss tayi da rashin fahimta ya daganta gira yace inaso ki juyemin da sauri" daidai lkcn taji gabanta ya yanke yabads wani dam ta dafe qirji da sauri tana waige yace ko bakiji ne?" Da qaraji yayi mgnr taja numfashi ta miqa masa har qoran tace banida ledar da zata dauka duka kaje da qoran ka dawo mani dasu wataran" karba yayi yasa a bayan motar ya zaro dubu biyar ya bata yace gashinan har kudin qoranki bana shigowa garinnan sai idan wani babban uzuri ya taso" karba tayi tayi godiya ta juya da sauri ga mamakinsa kawai yaga ta take a guje ya saki baki yana kallonta a fili yace lkc guda nutsuwarta ta gushe ko meye yaja hakan?" Tabe baki yayi ya daki kansa yace kaima Cornel Rasheed da shiga abinda babu ruwanka kake" cikin kasuwar ya shiga yayi siyyayarsa ya juya da motarsa yabi wata siririyar hanya. Itakuwa koda ta kwasa a guje duk nisa dake tsakaninta da rugarsu haka ra rinqa cin gudu harta fara hango rugar tasu nesa sosai gabanta ya qara yankewa ya fadi ganin wani baqin hayaqi yana tashi ta sashin da bukkarsu take, da sassarfa ta nufi gurin kawai taji an wafci hanunta da qarfi dagowar da zatayi taga Moddibo Buba ne idanunsa sharkaf da hawaye yana janta yana kallon bukkar tasu dakeci da wuta, Da qarfin gaske ta turje cikin fitar hayyaci tace Innatuuuu!" Saurin rufe mata baki yayi yaci gaba da janta bai qyaleta ba saida yabar sashin rugar da ita ya tsaya jikin wata itaciya yana sharce hawaye ya dubeta yace Haka Allah yake ikonsa Aminatu a wannan qarnin babu wani abu dazan iyayi miki face na saki a hanya kibar yankin nan gabadaya Su Bangel basu da Imani Ina zargin sune suka sanyawa dakin Indo wuta suka qoneta ina daji Audi yaje yake fadamin har yana cemin yanzu Hakama Ribadu da Manga sunacan suna nemanki kema sunason kasheki ne tunda uwayenki sunqi amincewa su bawa Manga Aurenki harma suna masa sharrin zai lalataki............ *THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566* *Shares Please* *Oum Hairan* [7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD* *(OUM HAIRAN)* *( Pure love sex nd romantic)* *FREE PAGE FOUR 4* *SUBSCRIBE* _DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_ https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ *TUNATARWA* Tabbas gafalalle shine wanda yake take laifinsa yake kallon na waninsa asara da tabewa ta tabbata garesa, kada ka damu da kuskuren wani domin bakasan boyayyen sirrin dake tsakaninsa da Allah ba, yi qoqarin ganin ka samu kusanci da mahaliccinka wannan shine cikar hankali Dubanshi takeyi da yanayi na gushewar hankali tanason ta bude bakinta tayi magana amma yayi mata nauyi gabbanta gabaki daya rawa sukeyi na tashin hankali zuciyarta tayi matuqar quntata, daqyar ta iya hada kalmar Moddi sun kashemin Innatu me tayi musu kana ina ka bari suka kashemin Innatu na Moddi shin Ina gatana???" Tana mgnr ne cikin gushewar hayyaci inda shikuma yaketa qoqarin janyewa daga gareta har ya samu ya yakice ta ya juya yana tsiyayar da hawaye batare da ya iya bata amsa ba. Saida ya bata tazara sosai tana tsaye kamar sassaqe sannan ya tsaya batare daya juyo ba yace ki miqe hanyar nan tabbas nasan zasu biyoki koma suna kusa ki tafi Juhud kada su hallakaki burinsu ya cika banason burinsu ya cika nafiso su rinqaji a ransu cewa bayan Haro da Indo akwai wani abu da ya zame musu alaqaqai din da suka rasa samun damar cimma buri akansu tabbas taimakon Allah zai riskeki ta inda baki zata ba....." Daga haka bai kuma cewa komai ba ya tafi yabarta a kan kwanar ta durqushe a gurin ta rushe da wani marayan kuka na tunanin rashin madafa wanda bataji yana bawa zuciyarta sanyi ba saima qarin tafasa da takeyi. Haka tanaji tana gani Moddi ya rinqa ratsa Kalgo da Sabara har ya bacewa ganinta haka ta wanzu a gurin tsayin lkc tana dama ace itama Allah ya aiko abinda zashi dauki rayuwarta ta huta, yanzun idan tabar guringa ina ta nufa....... Tana tsaka da wannan tunanin ta rinqajin qarar yayi alamun tahowa akeyi gareta tayi saurin saita nutsuwarta duk tsoro irin nata yau zuciyarta ta soye mutuwa tafi buqata fiye da rayuwa, ji tayi an tsaya can ta fara hango duhun mutane har uku Muryar Baffa Ribado tajiyo yana cewa yawwa gata cen...." Ai bata gama jin cewarsa ba ta zabura ta miqe daidai lkcn da suka zagayeta kowa da makami a hannunsa jikinta ya dauki tsuma ta dubi fuskokinsu zatayi mgn kawai Manga yakai mata sara ta goce ta fadi qasa warwas. Ya sake daga Addar Hannunsa ya saita qirjinta ta rintse idonta tanajin saukar saran daya sanyata sakin wata razananniyar qara data cika dajin. Ya sake daga Addar zai qara mata suka ga wani haske me dogon zango ya haskesu tuni suka saki makaman suka juya da sauri suka tsuke suka shige cikin duhun dare domin a lkcn magaruba ta jima da wuccewa. Hasken yaci gaba da kusantota har ya iso daf da ita cambala qafarsa da yayi a cikin jini ne yasashi saurin haska qasa yaga jinine yake malala a qasa kamar ruwa, da sauri ya saita fitilarsa a wajen da yaga jinin yana gangarowa ya matsa da sauri ya zubawa yar fulanin ido tare da russunawa ya haske fuskarta da fitilarsa sosai yaji faduwar gaba daidai lkcn da ruwan saman ya kece da qarfin gaske, yace Cornel Rasheed yar fillon da kasai nono a gurinta ne dazun" Safa ya zaro cikin jakar dake goye a bayansa yasa a hannunsa ya daga rigarta tare da zaro ido
Chapter 4 · 0% Book details