← Book details Juhud Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 64

Sashe 28

Juhud Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta kwanta jikinta ke rawa zuciyarta take tashi zazzabi me zafi ya rufeta hakanan ta wanzu a dakin hawaye nabin kuncinta tabbas Allah shine buwayi gagara misali yanzu duk irin tanadin da Zulaihat keyiwa aurenta ashe batada rabon kasancewa da mutumin da takewa tanadin tausayin kanta ya kamata a fili tace Allah na tuba Allah" sai Tara na dare aka dawo daga suturarsu Aunty Zulaihat mutuwar ta Sanyaya jikin kowa Zulaihat mace me shiga rai me hqr da daukar duniya baa bakin komai ba ta wucce sai labarinta. Koda suka dawo Juhud tanajin Mom da Addah suka shigo tayi likimo kamar me bacci Mom ce ta taba jikinta tace inajin zazzabin nan nata ne me zafi ya sake dawowa Allah dai ya yaye dare yanzu yayi Dr Razaq yana asibiti saidai zuwa safiya sai yazo ya dubata" juyawa sukayi suka fita taja fasali ta gyara kwanciyarta itadai ranar bata rintsa ba ga zazzabi ga radadin zucci ga babu abokan tattaunawa, washegari da asuba Mai Martaba ya kirasu dukkansu bayan anyi addu'a yadanyi shiru na lkc kana ya Dora da cewa haka Allah yake ikonsa ubangiji ya jiqan wadanda suka mutu" Amsawa sukayi da Amin ya sake duban Juhud yace naso na daura aurenki da Kareem koda kuwa bayan an daura zai mutu ne so shi ya buqaci abari ya samu lfy tukunna inyaso sai a hada dana yan'uwanki to Alhmdllh hakan ma yayi saboda haka zan daura auren Rasheed da Hidaya qanwar Zulaihat a yau dinnan a masallacin fada insha Allahu kowa zai iya tafiya" idanun Rasheed nakan Juhud ta miqe zatabar gurin taji yace Mai Martaba ka hqr da yimin aure na fada maka ba aurene banaso ba hasali na fada maka muradina ka karba kabani abinda zuciyata takeso zaifi Mana kwanciyar hankali dukkanmu" Ficewa tayi batare da sanin wainar da zaaci gaba da toyawa ba ta nufi cikin gdan daidai lkcn da Muntaz suka shigo da Ya'isha ta tareta da sauri suka rungume juna suka fashe da kuka Juhud tace ina Amrah da Ya Kareem Ya'isha?" Numfashi ta sauke tace ya Kareem da sauqi fah sosai don yanzu ma da zsn taho Saida yace na gaisheki damuwarsa kece yace kada ki sawa ranki damuwa komai zaizo da sauqi da yardar Allah" Wata ajiyar zuciya ta sauke me qarfi tace anjima zanje na ganoshi in naji jikina da sauqi" dubanta Ya'isha tayi tace wai har yanzu jikin ne ke nifa Ina tsoron wani abu Juhud Anya ba cikine dake ba?" Dafe qirji tayi tace na shiga uku ni Aminatuh Ina zan samu ciki?" Murmushi tayi tace kina tunanin takunki da Ya Rasheed zai boyemin ne wlh karki sake kiyi ciki ki shiga ukun da gaske donshi namiji babu ruwansa" Kallon Ya'isha takeyi da mugun mamaki tace Karkice komi wlh tun ranar farko na fahimci shine yayi barnar da kike cewa baki saniba yasan nasani har kirana yayi yayimin kashedin idan wani ya sani bayan Ni to na kuka da kaina hakan tasa nayi shiru na zubanku ido, takun naku salon Yana birgeni sosai saidai inajin tsoron bacin rana fah" fasali Juhud ta sauke tana neman gurin zama tace idan hakan ta kasance ya zanyi ta Yaya zan gane inada ciki?" Matsowa Ya'isha tayi tace jikina duk ciwo yake Bari nayi ruwan dumi nazo mu fita musan abinyi" shigewa tayi bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta jima sannan ta fito tace naga tashin hankali jiya tabbas Allah ne yayi da kwanana a gaba nice fah a gaban mota Ya Kareem da Amrah da Zulaihat suna baya kawai saiji mukayi kamar an daga motarmu anyi sama da ita an dokata jikin wani dutse Wai ashe tayace ta cire nidai ban qara sanin meye ke faruwa ba Saida na farka naganni a gadon asibiti ake cewa motar tana dira qasa murfin ya bude da gangara daji daqyar aka laluboni sukuma tayita qoli dasu har saida masu qararren kwanan suka mutu sannan ta kife aka debi Amrah da Ya Kareem akayi asibiti dasu zuwan Mai Martaba ne ma yasa akan da wata bayan Amrah da Ya Kareem shine suka bazama nemana suka tsintoni a cikin wani rami" Da wannan ta gama shiryawa cikin wasu riga da wando ta dora doguwar riga suka fito Juhud na riqe da key din mota a hannunta suka Isa parking space din suka dauki motarsu suka fito daga gurin a harabar gdan suka hangi Rasheed zaune can nesa da yan zaman mokokin yana kada key a hannunsa saurin zuge glasses din motar sukayi suka fice Ya'isha ta tabota tace guy dinnan takunsa na bani citta....." Juyawar da zatayi taga motarsa a bayansu tace mun shiga uku Meenah yi kwana shiga layin layin Bashar muje shop Ya Rasheed ya biyomu" zuba idanunta tayi akan mirrow din ta zuge glasses din suka hada ido ya daganta gira ta hade rai Yana biye dasu sukayi parking suka fito shima ya fito ya harde jikin motarsa yana kallonta ta fito tana gyara mayafinta fuskar nan kamar an aiko mata da mala'ikan mutuwa suka shiga Mall din a zahiri ba siyayyar ce ta kawosu ba Ya'isha ce ta sace jiki ganin ya shigo Yana duba wasu dogayen ruguna ta samu ta nufi Pharmacy din cikin Mall din ta siyo tsinken test na ciki da wani qwaya da ake Kira Messofem ta hado mata da Vitamin C cikin aljihun wandonta ta zuba tarkacen ta sako audugar mats cikin ledar da multi-Vitamin ta nufo Mall din lkcn ya qaraso inda Juhud ke zaban mayukan shafa ya tsaya a bayanta tanajinsa ya Dora hannunsa saman bombom dinta ya sauke ajiyar zuciya ya kwanto da kansa kafadarta yace. Meye kike son siya ne kin kasa daukar komai" zuciya taja ta juya zata tafi ya riqo hannunta ya daganta gira yace zan samu ganinki?" Murmushin takaici tayi ta juyo a fusace tace na tsani mutum me naci wlh a rayuwata kai Wai bakada aiki sai baqin naci nifa Baffa'am ka takuramin ka hanama rayuwata sakewa wai ya kakeso danine......" Hannu ya dora a lips dinta Yana murmushinsa na isa yace au haba ashe na takura miki?" Dago kanta yayi ya dora bakinsa saman nata ya tsotsi lips dinta yaja numfashi ya janye a hankali yace kina qoqarin aikata kuskure Kuma wahala kawai zakisha ki wahalar da kanki a banza tun sati biyu baya nasan da cikina a jikinki Kuma son abuna nakeyi fiye da yanda kike tunani kada tsautsayi yasa kiyi yunqurin zubarmin da ciki Allah saidai ku tafi tare....." Kallon raini takeyi masa ta saki fuskarta tayi murmushin daya fito da asalin kyawunta tace ashe fah cikine dani ko Kuma kanason abinka hhhhh tabdi Amma lallai kaidin kakai kwarkwar saboda kaga inajin tsoronka kake tunanin zanyi wasa da mutumcina aikuwa saidai ka kasheni in ka kasheni ka soyeni ka rinqa sakata da daya biyu kanaci Amma wlh ciki saina zubar dashi aikin wof....." Riqe bakinta yayi yace karki zageni Meenah duka zanyi miki a gurin nan wlh" hankalin mutane ne ya dawo kansu ya shaqeta yace na rantse da Allah kika zubarmin da ciki saina batar dake daga duniyar nan" janyewa tayi ta galla masa harara tace ka fara Shirin batar dani daga yau....." Bata rufe bakinta ba ya ficeta da qarfi yayi waje da ita ya jefata a mota ya kulle ya nufi cikin ya cillawa Ya'isha key din motarsu ya kama kunnenta yace kece kike bata shawarar ta zubar da ciki ko, zakici ubanki idan naji lbrn kin sanarwa da wani muna tare da ita Allah saikin gwamnace rayuwa a lahira fiye da duniya sakarya kawai" Juyawa yayi ya tafi yaja motar da mugun gudu yabar harabar Mall din ta ganin ya dauki hanyar barin gari yasata kallonsa a razane tace in....Ina zaka kaini!...." Wani mugun kallo ya watsa mata yace saidake zanyi" jan bakinta tayi ta kulle tasan dai duk bala'insa saidai yayi ya gama bai Isa ya zare ranta daga jikinta ba suna tafe tana danna wayarta qarshe ma ta danna Bluetooth a kunnenta ta kunna waqa tanaji tanabi a hankali ya dubeta yayi qwafa wato da gaske yarinyar cikin wata dayan datasan wayeshi tayi bala'in rainashi harma waqa takeyi alama ta ko a jikinta duk abinda zaiyi yayi batada damuwa" parking yayi jikin wani shago ya fita zai kulleta ta kalleshi da fararen idanunta ta fara kwantar da kujerar da take zaune akai ta kwanta tare dayin miqa yabita da kallo ya juya ya shiga shagon bai jima ba ya dawo ya sake tashin motar sukabar gurin tafiya sukayi me tsayi kafin su shiga Kaduna batasan garin ba bin hanya kawai takeyi da kallo har suka shiga wata unguwa da taga ansawa Barnawa Layout ya rinqa kutsawa cikin unguwar a qarshe yayu horn jikin wani gda babba me kyau sosai aka leqo ta wata qofa ya leqa suna ganinsa suka bude masa ya shiga da gudu suna qamewa ko kallonsu baiyi ba ya ashe quarters ne gurin me dauke da gidaje goma Sha biyu yayi horn jikin gda na bakwai aka bude yasa hancin motarsa ya shiga yayi parking ya kwantar da kansa Yana mayar da numfashi na dan lkc kafin ya juya gareta yaga tama lumshe idonta yaja fasali ya bude motar ya fita. Bude gdan yayi ya shiga ta bude motar ta fito tabi bayansa tana qarewa gdan kallo ba wani babba bane falone kawai da kitchen a qasa sai dakin bacci dake sama da wani qaramin falon taja numfashi daidai lkcn da yake saukowa ya tsaya Yana kallonta itama shi take kallo taso ta gwada juriya Amma ta kasa batasan sanda hawaye ya zubo mata ba ya kwashe da dariya harda zubewa a kujera ta zame a qasa tace don Allah ka mayar dani gda Allah na tuba bazan qara ba" dagowa yayi yayi mata murmushi ya miqe yace akwai komai a kitchen dakin baccinmu Yana sama idan da abinda kike buqata ki fada na taho miki dashi kafin nan bani wayarki, zan tafi nemanki Mai Martaba ya kirani yace kin bata" Kudi ya zaro masu kauri ya aje mata harya fita ya dawo ya tarar da ita sake da baki ya tsugunna a gabanta ya hade goshinsu Yana hura mata iskar hancinsa Yana turata baya a hankali har ya zamar da ita ya janye mayafin ya balle
Chapter 28 · 0% Book details